Ma'anar Tsakake zuciya1

Ma'anar Tsakake zuciya1

Ma'anar Tsakake zuciya

Wanda duk ya san Allah sai ya so shi, ya tsarkake ibada gare shi

Ikhlasi shi ne aljannar masu Ikhlasi, kuma ruhin masu tsoron Allah, sannan shi ne sirri tsakanin bawa da Ubangijinsa, shi ne abin da yake yanke waswasi da riya. Ikhlasi shi ne ka yi nufin Allah da aikinka, kada ka nufi waninsa, kada ka nemi waninsa, kada ka nemi yabo daga wajen mutane, kada ka jira wani sakamako sai a wajen Allah (S.W.T).

Ayyub Assakhatiyani ya kasance yana tsayuwar dare gabaxayansa, yana voye haka, idan safiya ta yi, sai xaga muryarsa kamar yanzu ya tashi.

Ikhlasi shi ne cikar aiki da kyansa, kuma shi ne mafi girman abu a duniya, shi ne kaxaita Allah da xa’a, da mantawa da cewa mutane suna ganinka, ta hanyar tunawa da cewa Allah yana ganinka, duk abin da aka yi don Allah to zai saka a kanshi, duk kuwa abin da aka yi don waninsa, to zai tafi a wofi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Dukkan ayyuka sai da niyya, kuma kowane mutum yana da sakamakon abin da ya yi niyya. Wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai samu, ko mace da zai aura, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da ya yi hijira zuwa gare shi”. (Bukhari ne ya rawaito shi)

Matsayin Ikhlasi

Ikhlasi yana da matsayi babba a addini, wanda babu abin da ya kai shi matsayi, ba a karvar aiki sai da tsarkake niyya, Allah Maxaukakin Sarki ya tunatar da mu Ikhlasi a wurare da dama a cikin Alqurni mai girma, daga ciki akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki “Ba a umarce su sai dai su bautawa Allah suna masu tsarkake addini gare shi” (Albayyinah : 5)

Kuma Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ka ce haqiqa sallata da yankana da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai. Ba shi da abokin tarayya, da wannan aka umarce ni, nine farkon musulmi” (Al’an’am : 162 – 163)

Allah mai girma da buwaya ya ce, “Wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarrabeku wanene a cikinku ya fi kyan aiki” (Al-mulk : 2)

Kuma Ya sake cewa : “Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah kana mai tsarkake masa addini, ku saurara addini. Tsarkakakken addini na Allah ne” (Azzumar : 2 – 3)

Kuma Ya ce, “Wanda yake fatan gamuwa da Ubangjinsa to ya yi aiki na qwarai kada ya haxa wani da Ubangijinsa a wajen bauta” (Alkahfi : 110)


Ta yaya za ka zama mai tsarkake zuciyarka?

Abu na farko : tabbatar da (Tauhidi) kaxaita Allah. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa, “Kana mai tsarkake addini gare shi. Ku saurara addini tsarkakakke na Allah ne” (Azzumar : 2 – 3)

Duk wanda baxininsa ya sava da zahirinsa, to wannan abu ne vatacce.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ba a umarce su ba sai dai su bautawa Allah suna masu tsarkake addini gare shi” (Albayyinah : 5)

Na biyu : Tabbatar da biyayya ga Manzon Allah (S.A.W) da yi masa xa’a cikin abin da ya umarta, da nisantar abin da ya hana, ya tsawatar a kai, da gaskata shi cikin abin da ya ba da labari. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa,.. “Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah ku bi Manzosa, da ma’abota al’amura a cikinku, idan kun yi jayayya akan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzo, in har kun yi imani da Allah da ranar lahira, wannan shi ne mafi alheri kuma shi ne kyau ga fassara”. (Annisa’i : 59)

Na uku : Idan kana son ka samu Ikhlasi to ka yi qoqarin aiki na qwarai, ka riqa tunawa a koyaushe cewa daga cikin mutum bakwai da Allah zai musu inuwa ranar da babu inuwa sai inuwarsa, akwai : “Mutumin da ya yi sadaka ya voye ta yayin bayarwa”. (Bukhari ne ya rawaito shi)

Ka sake tunawa dai cewa : “Dukkan ayyuka sai da niyya” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Na huxu : Ka watsar da son yabon mutane daga zuciyarka, ka xebe qauna daga abin da yake hannun mutane, ka mayar da komai naka zuwa ga Allah mai girma da buwaya. Mai tsarkake niyya mai yin abu don Allah baya kwaxayin wata duniya da zai samu, ko wata mace da zai aura, kwaxayinsa kullum shi ne rahamar Allah.

Na biyar : Ka koma ka faxi gaban Ubangijinka, ka lazimci bakin qofarsa mai girma da buwaya tare da yin addu’a Allah ya azurtaka da tsarkin zuciya, da barin riya, ya karvi tubanka daga abin da ya gabata na zunubai da savo.

Tsarkake niyya shi ne kada nemi wani ya san aikinka sai Allah, kada ka nemi wani sakamako daga wajen waninsa

Na shida : Nisantar riya da guje mata, Idan bawa ya shigar da kansa hanyar riya to ya qara nisa daga hanyar Allah. Misalin haka yadda wasu mutane suke kiran kawunansu da waliyyi, ko mutum ya yarda a kira shi da haka, ko ya riqa bayar da labarun ayyukansa da biyayyarsa ga Allah. Allah yana cewa, “Waxanda suke neman rayuwar duniya da adonta to za mu cika musu sakamakon ayyukansu a cikinta ba za a rage musu ba. Waxannan ba su da komai a lahira sai wuta, ayyukansu da suka yi sun rushe, abin da suke aikatawa ya lalace” (Hud : 15 – 16)

Riya qaramar shirka ce, amma rashin karvar aikin da ta shiga cikinsa koda kuwa a zahirinsa ingantacce ne, da mayar da shi ga waxanda suke yin shi, ya ishe ya nuna mummunar makomarta,

Na Bakwai : Zama da masu Ikhlasi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mutum yana kan addinin abokinsa” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Ikhlasi da son yabon mutane bacsa haxuwa a zuciya, sai dai kamar yadda wuta da ruwa suke haxuwa.

Na takwas : Voye ibada da sirrinta ta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Idan kuka bayyana sadaka to madallah da ita. Idan kuka voyeta kuka baiwa mabuqata to wannan shi ya fi alheri gareku” (Albaqra : 271)

Na tara : Yiwa kai hisabi mai tsanani. Wato hisabi a koda yaushe. Allah maxaukakin Sarki ya ce, “Waxanda suka yi qoqari a kanmu za mu shiryar da su hanyoyinmu” (Al’ankabut : 69)

Ka lura da faxin Allah (S.W.T) “A kanmu”

Na goma : lizimtar addu’a, da fuskantar Ubangiji da yawaita hakan. Idan bawa faqiri ya lizimci qofar ubangidansa, sai ubangidan nasa ya tausaya masa, ya biya masa buqatarsa da abin da yake nema. Addu’a ita ce roqon Allah mai girma da buwaya.


Daga Fa’idojin Ikhlasi

1-Karvar ayyuka : Wanda wannan abu ne mai mahimmanci, kuma sharaxi ne daga sharuxxan karvar ayyuka. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Haqiqa Allah ba ya karvar aiki sai wanda ya kasance an yi shi da tsarkakakkiyar zuciya, kuma an yi don neman yardarsa” (Nasa’i ne ya rawaito shi)

2-Samun Nasara da kafuwa : Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah yana taimakon wannan al’umma da raunananta, ta hanyar addu’arsu da sallarsu da Ikhlasi” (Nasa’i ne ya rawaito shi)

3-Kuvutar zuciya daga cututtuka : Ina nufin cututtukan zuciya, kamar qullata, da qyashi, da ha’inci, da hassada. Manzon Allah (S.A.W) ya faxa a lokacin hajjin ban kwana ya ce, “Abubuwa guda uku zuciyar musulmi ba ta qullata a kansu : Tsarkake aiki ga Allah, yi wa shugabannin musulmi nasiha, lizimtar jama’ar musulmi. Domin addu’a tana kewaye da su” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Abdullahi xan Umar ya ce, &"Da na san Allah ya karvi sujjadata guda xaya, da sadakar dirhami xaya, da babu abin da zan fi so kamar mutuwa. Kun san aikin wa ake karva? &"kaxai Allah yana karva daga masu tsoronsa ne&"

4-Haxa ayyukan duniya da ayyuka na qwarai : Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “A cikin tarawar xayanku da iyalinsa akwai ladan sadaka. Sai suka ce, ya Manzon Allah, yanzu xayanmu zai biya sha’awarsa kuma ya zama yana da lada? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku ba ni labari idan ya sanyata a haramun yana da alhaki? To haka ma idan ya sanyata a halal, to yana da lada” (Muslim ne ya rawaito shi)

5-Korar munanan saqe-saqen Shaixan da wasiwasinsa : Yayin da Allah ya kori Shaixan ya nisantar da shi daga rahamarsa sai Allah ya faxa mana abin da ya ce, ”Ya ce, ya Ubangijina saboda vatar da ni da ka yi, sai na qawata musu (Varna) a bayan qasa gabaxayansu. Sai dai bayinka cikinsu waxanda aka tsarkake” (Alhijri : 39 – 40)

Ta yi wu wani ya nisanci duniya da jikinsa, amma kuma yana tare da ita a zuciyarsa. Ta yiwu wani kuma yana tare da duniya da jikinsa, amma kuma baya tare da ita da zuciyarsa, wannan shi ya fi hankali.

6-Yaye damuwa da wahalhalu : kamar misalin abin da ya kasance a cikin labarin mutanen nan guda uku, waxanda barci ko ruwan sama ya kora su zuwa ga wani kogo. Asalin hadisin yana cikin Bukhari da Muslim.

7-Tsira da aminta daga haxarin fitintunu : kamar yadda ya faru da Yusuf (S.A.W) Allah yana cewa a kansa : “Ta himmatu da shi, shi ma ya himmatu da ita, ba don ya ga dalilin Ubangijinsa ba, hakan ya faru ne don mu kawar masa da mummunan aiki da alfasha, haqiqa shi yana cikin bayinmu tsarkaka” (Yusuf : 24)

Ta yi wu aiki kaxan, niyya ta mayar da shi mai yawa. Ta yi wu kuma aiki mai yawa niyya ta mayar da shi kaxan.

Ibnul Mubarak

8-Samun lada koda kuwa aikin bai kai ba. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Da waxanda idan sun zo wajenka don ka xauke su (zuwa jihadi) sai ka ce babu abin da zan xauke ku a kanshi, sai su juya idanuwansu suna zubar da hawaye don baqin cikin ba su samu abin da za su ciyar ba” (Attaubah : 92)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda ya roqi Allah shahada da gaskiya, to Allah zai kai shi matsayin Shahidai, koda kuwa ya mutu a kan shimfixarsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

9-Shiga Aljannah : saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Ba komai ake saka muku ba, sai abin da kuka kasance kuna aikatawa”. (Assaafat : 39)

Ka voye kyawawan ayyukanka kamar yadda kake voye munanan ayyukanka.

Abu Haazim Al-madiniiy

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Sai dai bayin Allah tsakakakku. Waxannan suna da wani arziki sananne. Kayan marmari kuma suna ababen girmamawa. A cikin aljannatai na ni’ima. Akan gadaje suna fuskantar juna. Ana kewayawa a cikinsu da kofi na giya ta wani marmaro. Fara sal mai daxi ga masu sha. Babu wani jiri a cikinta, kuma ba za su yi wani maye ba. Kuma suna da wasu mata masu taqaita kallonsu. Masu manyan idanu. Kamar su wani qwai ne voyayye” (Assaafat : 40 – 49)

Wannan yana cikin manya-manyan fa’idojin tsarkake zuciya