Ma'anar Ubangiji1

Ma'anar Ubangiji1

Ma’anar Ubangiji

Lafazin Allahu, suna ne mai daxi a wajen ma’ana da faxa, kuma ya samo asali daga Allantaka da so da qauna, da kaxaitawa da tsakake zuciya, me ya fi wannan sunan girma!! “Shi ne Allah Mahalicci mai qirqirar halitta” (Alhashar : 24)

Ubangiji shi ne shugaban da babu kamarsa, wanda yake gyara al’amuran halittarsa da abin da ya zubo musu na ni’imomi. Mai mulkin da yake da halitta da al’amura gabaxaya, ba a amfani da lafazin (Arrabbu) a kan halitta sai dai idan an goya shi da wani suna,kamar a ce, Rabbud Dari, ko Rabbul Mali, wanda ya mallaki gidan ko dukiyar, amma a faxe shi haka kurum ba tare da an goya shi da wani suna ba, to wannan sai ga Allah shi kaxai.

Shi ne Allah Mahalicci wanda ya yi qirqira, mai kamanta halitta yadda ya so, wanda ya halicci dukkan komai, ya samar da su ya daidaita su, ya suranta su da hikimarsa, kuma Allah bai gushe ba da wannan siffofi har abada.

Da yake mutane sun riga sanin buqatarsu ga wanda zai rene su ya kula da su, kafin su san buqatarsu ga abin bauta, haka ma sun fi sanin a biya musu buqatunsu na gaggawa kafin waxanda za a biya musu a nan gaba, don haka sai suka yadda da kaxaituwar Allah da ayyuka, kafin su yarda da cancantarsa da bauta kiransa shi kaxai, da neman taimakonsa da dogara da shi fiye da bauta masa da komawa zuwa ga gare shi.

Allah Ubangiji shi ne mai renon dukkan bayinsa, ta hanyar jujjuya al’amura da ni’imomi kala-kala, musamman ma renon da yake wa bayinsa kevantattu na gyara musu zukata da halaye, don haka suke yawan kiran shi da sunan (Rabbu) don suna neman irin wannan renon kevantacce.

Lafazin (Arrabbu) ya qunshi abubuwa da dama, kamar jujjuwa abubuwa, da azurtawa, da ba da lafiya, da datarwa, Allah yana cewa, “Shi ne wanda yake ciyar da ni yake shayar da ni. Idan na yi rashin lafiya shi ne yake warkar da ni. Wanda kuma yake kashe ni kuma yake rayani” (Ashua’ara : 79 – 81)

Dalilan Da Suke Nuna Samuwar Ubangiji

Duniyar nan gabaxayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da faxin akwai Allah Mai girma da buwaya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Manzanninsu suka ce, yanzu akwai shakka a cikin samuwar Allah, wanda ya halicci sammai da qassai, yana kiranku don ya gafarta muku zunubanku ya jinkirta musu zuwa wani lokaci sananne. Sai suka ce, kufa ba kowa ba face mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Ibarahim : 10)

Mumini shi ne da ya yi yaqinin cewa Allah Maxaukakin Sarki shi ne Ubangiji, mai iko, ya kuma tabbatar da cewa shi ne abin bautawa shi kaxai.

Ta yaya za a nemi dalili akan samuwar abin da shi ne dalilin samuwar komai Allah mai girma da buwaya.

Idan muka tsallaka zuwa ga dalilan da suke nuna samuwar Allah, za mu samu dalilai kama haka :

Dalili Na Fixirah

Babu wani abu da za ka yabi Allah da shi face da falalarsa da ni’imominsa, kai kuma a kowane hali kana buqatar Allah mai girma da buwaya.

Asalin halitta an yi ta ne a kan imani da Allah mahalicci. Babu wanda yake barin wannan abin da aka halicce shi a kai na imani da Allah mahalicci sai wanda Allah ya rufewa zuciya da hankali. Daga cikin manya-manyan dalilai da suke nuna an halicci mutum a kan imani da samuwar Allah Maxaukakin Sarki faxin Manzon Allah (S.A.W): “Dukkan wanda ake haihuwa ana haihuwarsa akan asalin halitta (Fixirah), iyayensa ne suka mayar da shi bayahude ko banasare ko bamajuse, kamar irin yadda dabba take haihuwa, shin kuna ganin ana haihuwar mai yankakken kunne”(Bukhari ne ya rawaito shi)

Dukkan wani abin halitta ya yarda da kaxaita Allah a yanayin halittarsa. Allah ya ce, “Ka tsayar da fuskarka a kan addini, kana mai karkata ga barin qarya. Halittar Allah ce da ya halicci mutane a kanta, babu canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addini miqaqqe sai dai da yawan mutane ba su sani ba” (Arrum : 30)

Waxannan dalilai na hankali suna nuna samuwar Allah maxaukakin Sarki.

Tabbatuwar da samuwar Allah a hankalce ya fi kowane dalili qarfi ga duk wani wanda shaixanu ba su janye shi ba, don haka Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Halittar Allah ta asali da ya halicci mutane a kanta” (Arrum : 30)

Bayan ya ce “Ka tsayar da fuskarka ga addini kana kaucewa varna”. (Arrum : 30)

Sunan Allah suna ne da aka zana shi a cikin halittar kowa, ba ya buqatar wani dalili fiye da wannan.

Lafiyayyen hankali yana shaida wa da samuwar Allah, amma wanda shaixanu suka janye shi zai iya qin wannan dalili ya ji ba ya buqatarsa. Amma idan ya faxa cikin wata matsala babba, sai ka ga hannayensa da idanuwansa da zuciyarsa sun nufi sama kai tsaya suna neman taimako da agaji daga Ubangijinsa. Domin ya koma halittarsa ta asali madaidaiciya.

Dalili Na Hankali

Daga cikin manya-manyan dalilai masu qarfi, waxanda ba wanda zai yi musu akansu sai mai jayayyar runto kaxai, akan tabbatar da samuwar Allah mahalicci, daga cikinsu akwai :

1-Dukkan halitta akwai wanda ya halicceta : dukkan waxannan ababen halitta gabaxayansu akwai wanda ya samar da su, domin ba zai yi wu su samar da kansu da kansu ba, saboda babu abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi. Sannan kuma samuwar waxannan abubuwa akan wannan tsari mai kyau, haxaxxe, mai tafiya tare da sababi, a haxe da juna, ba zai yiwu ba a ce haka kurum abun ya faru kwatsam, a’a dukkan wani mahaluki ba makawa yana da wanda ya halicce shi. To idan kuwa abin haka yake, to lallai Allah ne Ubangijin talikai ya samar da su, Allah MaxaukakinSarki ya faxi wannan dalili inda yake cewa “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar” (Axxur : 35)

Allah yana nufin su ba haka kurum akan halicce su ba, ba tare da wani wanda ya halicce su ba, kuma ba su suka halicci kawunansu ba, to dole suna da wanda ya halicce su, wanda shi ne Allah Maxaukakin Sarki, don haka ma lokacin da Jubairu xan Mux’im – Allah ya yarda da shi – ya ji Manzon Allah (S.A.W) yana karanta suratux Xuri, ya zo kan waxannan ayoyi, inda Allah yake cewa, “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar. Ko su ne suka halicci Sammai da Qasa, a’a ba su yi yaqini ba. Ko a wajensu akwai taskokin Ubangijinka, kai ko su ne waxanda suka mamaye komai” (Axxur : 35 – 37).

A lokacin Jubairu yana mushiriki bai musulunta ba, amma duk da haka sai ya ce, “Zuciyata ta kusa ta tsinke” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Xan adam tare da ximbin ilimin sanin duniya da Allah ya ba shi, har yanzu ya kasa gano wasu abubuwa na voye waxanda babu abin zai kawo qarshen cece-kuce a kansu sai kawai imani da akwai Allah shi kaxai.

2-Bayyanannu ayoyin Allah a cikin duniya da halittarsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ku duba (ku yi tunani) mene ne a cikin Sammai da Qasa” (Yunus : 101)

Saboda a cikin duba sammai da qasa zai bayyana Allah ne mai halitta, kuma ya qara tabbatar da kaxautuwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai ya ce, “Alamar sawu tana nuna tafiya, kashin raqumi yana nuna akwai raqumin. To yanzu sama mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu waxannan ba za su nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.

3-Tsaruwa lamarin duniya da kyautatuwarsa, dalili ne akan wanda yake tsara shi, shi ne abin bauta shi kaxai, kuma mamallakinsa shi kaxai, Ubangiji shi kaxai, babu wani abin bauta sai shi, kamar yadda ba zai yi wu ba a samu Ubangiji biyu, masu halitta kuma waxanda suka yi daidai da juna, to haka ma ba zai yiwu a samu ababen bauta guda biyu ba, waxanda suka yi daidai da juna. Kuma ba zai yi wu a samu waxanda suka yi duniya su biyu ba, abu ne tabbatacce a hankali, to haka ma ba za a samu abbaben bautawa guda biyu ba.

Dalilin Shari’a

Dukkan Shari’u suna nuana samuwar wanda ya yi halitta, kuma suna nuna cikar iliminsa da hikimarsa da jinqansa, saboda dukkan shari’u ba makawa da wanda ya shar’anta su, wanda shi ne Allah Mai girma da buwaya, Allah ya ce, “Ya ku mutane ku bautawa Ubangijinku wanda ya halicce ku, da waxanda suke gabaninku ko kwa samu taqawa. Wanda ya sanya muku qasa ta zama shimfixa gareku, ya sanya kuma sama ta zama gini gareku, ya saukar daruwa daga girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (Albaqra : 21 – 22)

Dukkan littattafan da Allah ya saukar suna faxin haka.

Dalili Na Gani da Ji

Daga bayanannun dalilai da suke nuna samuwar Allah Mahalicci akwai dalilin da duk mai hankali yake gani kuma yake jinsa, kamar :

1-Amsa addu’o’i : Mutum yana roqon Allah, ya ce, “Ya Ubangiji” ya roqi wani abu, sai kuma ya ga an amsa masa, to wannan dalili ne da ake gani dake nuna samuwar Allah Ubangiji, saboda Allah ya amsa masa, kuma mutum ya ga hakan quru-quru. Haka ma muma sau da yawa mun ji misalai a da, da yanzu na cewa Allah ya amsa musu abin da suka roqa. To wannan wani lamari ne da yake nuna samuwar Allah Mahalicci, a cikin Alqur’ani akwai dalilai irin waxannan da yawa, daga cikinsu akwai faxin Allah, “Ka tuna (Annabi) Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa cewa cuta ta shafe ni, Allah kuma kai ne mafi jinqai masu jinqai. Sai muka amsa masa” (Al’anbiya : 83 – 84)

Da ayoyi da yawa irin waxannan.

Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani.

2-Shiryar da halittu zuwa ga abin da yake shi ne sirrin rayuwarta. Wan ne ya shiryar da mutum zuwa ga kama mama yayi da aka haife shi? Wanene ya shiryar da Al-Hudu-Hudu har yake gane wurin ruwa a qarqashin qasa, wanda ba wanda yake ganin hakan sai shi? Haqiqa Wannan aikin Allah ne, yana cewa : “Ubangijinmu wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar da shi” (Xaha : 50)

3-Ayoyin da Allah ya aiko Annabawa da Manzanni da su, su ne Mu’ujizozin da Allah ya qarfafa su da su, ya zave su, daga cikin mutane ya fifita su. Dukkan wani Annabi Allah ya aiko shi da wata mu’ujiza zuwa ga mutanensa, tana tabbatar da cewa abin da aka aiko shi da shi daga wajen Allah ne, mahalicci abin bauta shi kaxai, babu wani abin bauta wanda ba shi ba.

Tasirin Kaxaita Allah a cikin ayyukansa akan bawa mai tauhidi

1-Fita daga ruxu da shakka : To ta yaya ma wanda ya san yana da Ubangiji, wanda shi ne Ubangjijin komai zai ruxe ya shiga shakka, alhali ya san Allah shi ne ya halicce shi, ya daidaita shi, ya girmama shi ya fifita shi, ya hore masa abin da yake cikin sammai da qasa gabaxaya, ya kwararo masa ni’imominsa na zahiri da baxini, don haka sai ya nutsu da Ubangijinsa, ya koma wajensa, ya gane cewa wannan rayuwar gajera ce, tana haxe da alheri da sharri, da adalci da zalunci, da jin daxi da wahala.

Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani, kuma duhu ne a cikin zuciya da tozarta a rayuwa.

Amma waxanda suka yi jayayya da ayyukan Allah, suka yi shakkar gamuwa da shi, to rayuwarsu ba ta da wani xanxano ko ma’ana, dukkanta tashin hankali ne da ruxewa, da tambayoyi da dama, ba su da wani wuri da za su koma gare shi, hankalinsu ya kwanta. Koyaushe suna cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da ruxu da shakka. Wannan kuwa azaba ce ta duniya, wuta ce da take dukan fuskarsu safe da yamma.

2-Samun kwanciyar hankali : Hanya xaya ce ta samun kwanciyar hankali ita ce imani da Allah da ranar lahira. Imani mai qarfi na gaskiya wanda babu wata shakka a cikinsa. Wannan shi ne abin da tarihi ya nuna, kuma kowane mutum mai adalci zai tabbatar da hakan, saboda mun riga mun sani cewa mafi yawancin mutanen da suke cikin damuwa da tozarta da damuwa da shakka su ne waxanda Allah bai ba su imani da shi ba, ba su da yaqini na imani, don haka rayuwarsu ba ta da wani xanxano ko zaqi, koda kuwa an lulluve su da kayan daxi, saboda rayuwarsu ba ta da wata ma’ana, ba su gane sirrinta ba, to ta yaya zasu samu nutsuwa a cikin zukatansu da kwanciyar hankali.

Imani shi ne kwala-kwalen tsira

Samun nutsuwa wata fa’ida ce daga fa’idojin imani da Allah, saboda kaxaita Allah (Tauhidi) wata bishiya ce mai tsarki, wadda take ba da ‘ya’yanta a kowane lokacin da izinin Ubangijinta, wata kyauta ce daga sama Allah yake saukar da ita akan zukatan muminai, don su samu tabbata yayin da mutane suka raurawa, su yarda yayin da mutane suka yi fushi, su yi yaqini yayin da mutane suke shakka, su yi haquri yayin da mutane suka haukace, wannan nutsuwar ita ce wadda Allah ya raya zuciyar Manzon Allah (S.A.W) da ita a ranar hijira, don haka babu wani tsoro ko baqin ciki ko wata damuwa da ta same shi. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “In ma ba ku taimake shi ba, to Allah ya taimake shi yayin da kafirai suka fitar da shi, suna su biyu a cikin kogo, a lokacin da ya cewa abokinsa, kada ka damu, Allah yana tare da mu”. (Attaubah : 40)

Duk wanda ya wadatu da Allah, sai mutane su buqace shi.

Damuwa da tsoro ya riga ya kama zuciyar abokinsa Abubakar Assidiq, ba wai tsoron rayuwarsa ba, a’a yana tsoron abin da zai sami Manzon Allah (S.A.W) da kiran da ya zo da shi na kaxaita Allah, har Sayyidina Abubakar lokacin da ya ga maqiya sun kewaye kogon da suke ciki sai ya ce : “Ya Manzon Allah da xayansu zai duba qasan dugadagansa da ya ganmu, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa, yana mai kwantar masa da hankali, “Ya Abubakar mene ne zatonka da mutane biyun da Allah ne na ukunsu”. (Muslim ne ya rawaito shi)

Duk lokacin da alakarka da Allah ta yi rauni to shakka da waswasi za su yi ta bijiro maka cikin zuciya.

Wannan nutsuwa wata rayuwa ce daga Allah, kuma haske ne da mai tsoro yake nutsuwa a cikinsa, wanda yake cikin tashin hankali ya samu nutsuwa, wanda yake cikin damuwa ya samu rarrashi a cikinta, mai rauni ya samu qarfi, rikitacce ya samu shiriya. Wannan nutsuwar qofa ce da Allah yake buxewa muminai daga cikin bayinsa, daga nan suke samun iskarta mai daxi, haskenta yake haskaka musu, suke samun qanshin turarenta, saboda Allah ya xanxana musu sakamakon abin da suka aikata na alheri, kuma ya nuna musu xan qaramin misalin abin da yake jiransu, sai su sami ni’ima da aminci da rayuwa da daga wannan iskar wannan nutsuwar.

3-Samun Yarda da aminta da Allah : komai yana hannun Allah, har amfani da cuta, Allah Maxaukakin Sarki shi ne mahalicci, shi ne mai azurtawa, mamallakin komai, mai jujjuya al’amura, dukkan makullan sammai da qasa suna hannunsa, don haka yayin da mumini ya san cewa babu wani abin da zai same shi sai abin da Allah ya rubuta msa, na alheri ko sharri, na amfani ko cutuwa, koda kuwa dukkan halitta sun haxu akan yi masa savanin abin da Allah Ya qaddara masa, to ba hakan ba zai tasiri ba a kanshi har abada, saboda ya san Allah shi ne mai amfanarwa da cutarwa, shi kaxai ne mai bayarwa da hanawa, sai sanin hakan ya qara wa mumini aminci da yarda da Allah mai girma da buwaya, da kaxaita Allah, don haka ma Allah ya zargi wanda yake bautawa abin da baya amfanarwa baya cutarwa, baya wadatawa wanda yake bauta masa da komai, Allah yana cewa, “Dukkan makullan Sammai da qasa na Allah ne. waxanda suka kafirce wa ayoyin Allah waxannan sune hasararru”. (Azzumar : 63)

Zuciya a hargitse take babu wani abin da zai haxa ta wuri guda, sai fuskantar Allah. A cikinta akwai kewa babu abin da zai gusar da ita sai kaxaita Allah da xebe kewa da shi. A cikinta akwai damuwa da baqin ciki babu abin da zai tafiyar da su sai farin cikin sanin Allah da mu’amalar gaskiya tare da shi.

4-Gimama Allah : Tasirin girmama Allah a fili yake a rayuwar mumini, wanda ya yi imani da Allah, ya kaxaita shi da bauta, da nufi da yin abu don shi, a duk lokacin da mumini ya lura da abin da Allah yake da shi na mulkin sammai da qasa to babu abin da zai yi face ya ce, “Ilimin Ubangijina ya yalwaci komai” (Al’an’am : 80)

Yana cewa, “Ya Ubangijina ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata a gareka” (Al-Imran : 191).

Duk wannan yana nuna ratayuwar zuciya da Ubangiji mahallicci mai girma da buwaya, da ba da qoqari wajen neman yardarsa, da qoqari wajen girmama shari’arsa da al’amuransa, da rashin yin shirka da shi, da haxa shi da wanda ba ya mallakar kansa, ba ya iya mallakawa waninsa daidai da qwayar zarra a cikin qasa da sama, dukkan wannan girmama Allah ne, kuma kaxan ne daga cikin tasirin kaxaita Allah ne a cikin ayyukansa ga mumini.

Aqidar Babu Allah Da Haxarinta

Aqidar babu Allah : ita ce musun samuwar Allah mahalicci mai girma da buwaya, kodai tan hanyar gurvataccen tunani, ko kuma mummunan fahimta, ko kuma girman kai da qin gaskiya. Wannan aqida ta kore samuwar Allah wata cuta ce a cikin hankali da vataccen tunani da duhun zuciya, tana mayar da mai ita mai raunin tunani, mai duhun zuciya, ba ya ganin komai ko fahimtar wani abu sai abin da yake iya riskarsa ta hanyar jinsa da ganinsa da sauran gavovin jikinsa. Sai wannan ya ja shi zuwa ga aiwatar da ra’ayoyin masu ganin babu wani abu samamme sai Madda, akan xan adam da aqidunsa. Wannan ya kai shiga tavewa da vata, ya xauki mutum ba wani abu ne ba sai “madda” don haka shi zama za a xabbaqa masa irin dokokinta ne.

Imani da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, shi ne mafi girman ayyuka, mafi xaukakarsu mafi matsayinsu, kuma mafi xaukakarsu wajen samun rabo.

Imam Shafi›i

Wannan kuwa wani haxari ne ga xan adam, wajen komawarsu zuwa ga duniya tsantsa, da tsantsan aiki da hankali wanda babu ruhin addini a cikinsa. Mai aqidar babu Allah tun da har ba zai yarda akwai abin bauta ba, to zai aikata abin da ya so, a kowane lokaci ba tare da tsoron azaba ba, ko tsoron wani abin bauta, abin da zai kai shi zuwa ga lalacewar zuciyar xan adam da halakarta, duk da kasancewa ya kafircewa Allah mai girma da buwaya, ya karkata haqqin Allah zuwa ga waninsa, Don haka a tarihin kafuwar aqidar babu-Allah aka riqa samun masu kashe kansu da kansu, suka yi yawa a cikin masana da mawaqa. Kuma bincike ya tabbatar da haka. A cikin binciken da vangaren kula da lafiya na majalisar xinkin duniya (WHO) ya gabatar, waxanda wasu qwararre biyu, Dr Jose Manuel da wata mata Alessandra Fleischmann suka yi, sun bayyana alaqa tsakanin addini da kashe kai, kuma suka tabbatar da mutanen da suka fi kowa kashe kansu su ne masu aqidar babu-Allah, ga yadda qididdigar abin yake.