Rayuwa Da Allah Da Sunayensa Da Siffofinsa

Rayuwa Da Allah Da Sunayensa Da Siffofinsa

Allah Mai Rahama Mai Jinqai

Haqiqa Allah mai rahama mai jinqai ne

Ya wajabta wa kansa yin rahama, kuma rahamarsa ta riga fushinsa, kuma ta yalwaci dukkan komai.. “Lallai rahamar Allah tana kusa da masu kyautatawa” (Al-aaraf : 56)

Mai rahama, mai jinqai, mai alheri, mai karamci, mai kyauta, mai jinqai, mai yawan kyauta. Waxannan sunaye ma’anoninsu suna kusa da juna, kuma dukkaninsu suna nuna siffantuwar Allah da rahama, da aikin alheri, da kyauta, da karamci, kuma suna nuna yalwar rahamar Alah wadda ta haxa komai da komai, gwargwadon yadda hikimar Allah ta hukunta. Ya kevance muminai da wani kaso mai yawa a cikinta, da rabo mai girma. Alllah ya ce, “Rahamata ta yalwaci dukkan komai, zan rubutata ta akan waxanda suke da taqawa” (Al’aaraf : 156) Ni’imomi da kyautatawa dukkansu alamu ne na rahamar Allah Maxaukakin Sarki da kyautarsa da karamcinsa, da alkhairin duniya da lahira, duk wannan alamomin rahamarsasa ne.

“Lallai Shi Allah mai rahama ne mai jinqai”

Allah ya fi jin tausayinmu fiye da iyayenmu mata. Manzon Allah (S.A.W) ya nuna wata mace mai shayar da wani jinjiri ya ce, “Kuna ganin wannan za ta iya sanya xanta cikin wuta, sai muka ce, a’a, ba za ta iya jefa shi cikin wuta ba, sai Manzon Allah ya ce, “Allah ya fi tausayin bayinsa fiye da wannan ga xanta” (Bukhari ne ya rawaito shi)

“Lallai Shi Allah mai rahama ne mai jinqai”

Yana tausayin dukkan bayinsa, kuma yana da wata rahama da ya kevance ta ga bayinsa muminai “Allah ya kasance danagane da muminai mai jinqai” (Al-ahzab : 43)

“Haqiqa shi Mai jinqai ne”

Yana cikin jinqan shi aiko Muhammad (S.A.W) don ya zama rahama ga talikai, mai shiryar da su, mai kiyaye musu maslaharsu ta duniya da ta addini

“Lallai shi mai jinqai ne”

Ba wanda yake riqe da rahamarsa sai shi, babu wanda yake sakinta sai shi.. “Abin da Allah ya buxe na rahamarsa ga mutane babu mai riqe shi, abin da kuma ya riqe babu mai sakinsa a bayansa, shi ne mabuwayi mai hikima” (Faxir : 2)

Lallai shi Allah mai rahama mai jinqai


Allah mai yawan kyauta ne

Lallai shi Allah mai yawan bayarwa da yawan kyauta

Ya wanda yake ba da ni’ima, ya wanda yake ba da abin nema, ya wanda yake ba da kyautatawa

Ka ba ni kyautar yardarka, ka ba ni aminci, ka ba ni sa’ada da tausayi.

Ka yi mana kyautar ka qara mana, kai ne ma’abocin kyauta da karamci “Ka ba mu wata rahama daga wajenka, haqiqa kai mai yawan bayarwa ne mai yawan jinqai” (Al-imran : 8) , “Allah mai karamci ne, yana son karamci da halaye masu girma, yana qin qasqantun halaye” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

“Mai Yawan kyauta da bayarwa“

Yana ba wanda ya so, yana hana wanda ya so.

“Mai yawan kyauta”

Kyautarsa ba ta da iyaka, ba mai mayar da falalarsa, yana cewa abu : “kasance, sai ya kasance” (Albaqra : 117)

“Mai yawan bayarwa”

Yana ba da arziqin fili da na voye, yana baiwa da falalarsa da karamcinsa.

Daga cikin haka abin da Allah yake buxewa bayinsa daga tunani mai kyau, da amfani, da ilimi da shiriya, da dacewa, da karva addu’a, dukkan wannan yana cikin arziki na voye da Allah yake ba da yawa daga cikin mutane.

“Mai yawan bayarwa”

Ya bayar, ya hana, ya sauke ya xaukaka, ya sadar, ya yanke, a hannunsa alheri yake, kuma shi mai iko ne akan komai

Shi ne Allah mai yawan bayarwa da yawan kyauta


Allah Mai yalwa ne

Lallai Allah mai yalwa ne “lallai Allah ne mai yalwa ne kuma masani ne”(Albaqra : 115)

“Mai yalwa”

Mai kyauta ne ga wanda ya roqa

“Mai Yalwa”

Cikakke cikin siffofinsa, mai girma cikin sunayensa, ba za a iya kidigdige yabo a gare shi ba, mai girma, mai yalwar mulki da iko da falala da kyauta da kyautatawa.

“Mai yalwa”

Ya yalwaci halittarsa gabaxaya wajen kyauta da gamsarwa da ilimi da kiyayewa da tsatstsara al’amura.

“Mai Yalwa

Wanda jin sa ya yalwaci dukkan sautuka, yaruka ba sa cuxe masa.

“Mai Yalwa”

Ya sauwaqa wa bayinsa bauta, ya kuma sanya musu addini mai sauqi, ya kuma yalwata musu.

Haqiqa Shi Allah Mai yalwa ne


Allah Abin Qauna ne

Haqiqa Shi Allah abin qauna ne “Shi ne mai yawan gafara abin qauna” (Alburuj : 14)

Allah mai qaunar bayinsa ne, yana son su, yana kusanto su, yana yi musu abin da za su yarda, kuma ya yarda da su. “Yana son su, suna son sa” (Alma’idah : 54)

“Abin qauna” .. wanda yake son Annabawansa, da mabiyansu, kuma su ma suna son shi, sun fi son shi fiye da komai, zuciyarsu ta cika da son shi, harsunansu suna cike da yabonsa, zukatansu sun tafi wajensa da so da qauna da komawa zuwa gare shi cikin dukkan al’amura.

Allah yana azurta su da son mutane gare su, su so su, su karvi abin da suka zo da shi.

“Abin Qauna”

Makusanci abin qauna, mai son alheri ga bayinsa

“Abin qauna”

Bayinsa suna son shi, suna shauqin gamuwa da shi. Ya zo a cikin hadisi : “Wanda ya so gamuwa da Allah sai Allah ya so gamuwa da shi” (Bukhari ne ya rawaito shi)

“Abin Qauna”

Yana umartar ka da wanke zuciya, da tsarkake ta daga gaba da qiyayayya, da wanke daga dattin qulli da ruwan so da qauna, da kashe wutar hassada da qanqarar soyayya da qauna.

Lallai Shi ne Allah Abin qauna


Allah Rayayye Tsayayye

Haqiqa shi ne Allah Rayayye Tsayayye “Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye tsayayye” (Al-imran : 2)

“Rayayye”

Cikakkiyar rayuwa, ba ya buqatar waninsa, amma kowa yana buqatarsa, kuma komai zai halaka Fuskarsa.

“Tsayayye”

Wanda yake tsaye da kansa, mawadaci gabarin waninsa

“Rayayye Tsayayye”.. Mai cikakkiyar rayuwa, wanda yake tsaye da kansa, kuma wanda yake tsaye a kan ma’abota sammai da qassai, wajen jujjuya al’amuransu da halayensu. “Rayayye”.. Wanda ya zatinsa ya tattara dukkan siffofin kamala

“Tsayayye”

Wanda yake tsaye akan kowace rai da abin da ta aikata, mai kiyaye ayyukan ba yi da halayensu da maganganunsu, da kyawawan ayyukansu da munannansu, mai ba su sakamako a kansu.

“Tsayayye”

Wanda yake lissafa abin da bayi suka aikata.

“Tsayayye”

Wanda ya xau nauyin rayuwar dukkan halittarsa, yana azurta su, yana jujjuya al’amuransu, da sha’aninsu.

“Rayayye Tsayayye”

Mawadaci wanda ba zai gushe ba. Ya xaukaka ya tsarkaka.

Haqiqa Shi ne Allah rayayye tsayayye.


Allah shi ne Mai tilastawa

Haqiqa Shi ne Allah mai girma da buwaya mai tilastawa. “Shi ne Allah wanda babu abin bautawa sai shi, mai mulki, tsakakakke, mai aminci, mai gaskatawa, mai kulawa, mabuwayi mai tilastawa, mai nuna isa, tsarki ya tabbata gare su daga barin abin da suke siffata shi da shi” (Al-hashru : 23)

“Mai Mikarwa”

Mai xora karyayye, mai taimakon fursuna, mai wadatar da talaka, mai tayar da masu tuntuve, mai gafarta zunuban masu zunubi, mai yanta waxanda suke cikin azaba, mai tayar da zukatar masoya masu tsoronsa.

“Al-jabbar”.. ma’ana maxaukaki, mai rinjaye, mai tausayi, mai miqar da karyayyun zukata, da gajiyayye mai rauni, da wanda ya fake a wajensa.

“Mai rinjaye”

Wanda xaukakarsa ta cika, ni’amarsa ta girmama a kan dukkan komai

“Mai qasaita”

Wanda komai da komai suka sunkuya masa, suka sallama masa, babu wani abu da yake shagaltar da shi daga wani abu.

“Mai qasaita”

Ma’abocin qasaita, da sarauta, da isasshen mulki, da girma da xaukaka

‘Mai rinjaye”

Wanda dukkan masu girman kai suka sunkuya masa, masu girma suka karaya a gabansa, masu mulki da manya suka qasqanta a gabansa, masu laifi da xagawa suka zube a gabansa.

Haqiqa Shi ne Allah Mai tilastawa ne


Allah Shi ne Mai kyau

Haqiqa Shi ne Allah mai kyau mai girma da buwaya

Ya Allah muna roqonka samun jin daxin ganin fuskarka mai karamci, da shauqin gamuwa da kai

“Mai kyau”

Yana da sunayen da babu abin da ya fi so kyau, da siffofin da babu abin da ya fi su cika

“Mai kyau”

Cikakkun kyawawan sunaye, cikakkun kyawawan sifofi, kyawon da ya kai matuqa ga kyau. “Kalmomin Ubangijinka sun cika wajen gaskiya da adalci” (Al-an’am : 115)

Wanda ya kyautatawa komai da ya halitta.

“Mai kyau”

Kyau abubuwan duniya dalili ne na kyansa mai girma da buwaya, kyansa hankali ba ya iya sanin qarshensa, haka ma babu wata fahimta da za ta iya sanin qarshensa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ba zan iya qididdige yabo gareka ba. Kai kamar yadda ka yabi kanka “ (Muslim ne ya rawaito shi)

“Mai kyau”

Ya yi wa halittarsa kyautar kyau, da kyan halaye, ya kuma ba su kyautar yi masa kyakkyawan zato.

Ya wanda yake mai kyau, yana son kyakkyawa, ka qawata zukatanmu da imani, ka yi mana kyautar halaye kyawawa, da zukata masu kyau, da zahiri mai kyau.

Haqiqa Allah shi ne Mai kyau


Allah masani qwararre mai ba da labari, mai kewaye da dukkan komai da iliminsa

Haqiqa shi ne Allah qwararre wanda yake kewaye da komai da iliminsa.

“Masani, qwararren mai bada labari, wanda yake kewaye da komai da iliminsa”

Wanda iliminsa ya kewaye komai ciki da waje, fili da voye, wajiban abubuwa da waxanda ba za su yi wu ba, da waxanda za su yi wu, da duniyar sama da qasa, da can da yanzu, da nan gaba, babu wani abu da yake voye masa.

“Masani qwararre Mai bada labari”

“Lallai Allah a wurinsa ne sanin ilimin alqiyama yake, yana saukar da ruwan sama, yana sanin abin da yake cikin mahaifa, wata rai ba ta san abin da za ta yi gobe ba, haka ma wata ran ba ta san a inda za ta mutu ba, lallai Allah shi ne masani qwararre mai ba da labari” (Luqman : 34)

“Allah masani mai kewaye da komai da iliminsa”

“Ya san abin da yake cikin sammai da qassai, ya san abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa, Allah masanin abin da yake cikin qirji ne” (Attagaabun : 4)

Shi Allah Masani ne ga dukkan komai

“Allah wanda ya halicci sammai bakwai, kuma qasa kwatankwacinsu, yana saukar da al’amura tsakaninsu, don ku sani Allah mai iko ne a kan dukkan komai, kuma ya kewaye komai da saninsa” (Axxalaq : 12)

Allah maxaukakin Sarki ya ce, “Lallai Allah ya kewaye dukkan komai da sani” (Axxalaq : 12)

Lallai Allah masani ne qwararre mai ba da labari, mai kewaye da dukkan komai da sani


Allah Makusanci

Lallai Allah makusanci

Ya wanda yake kusa da wanda ya kira shi, ya wanda yake kusa da wanda ya yi fata nagari gare shi.

Ya wanda yake kusa da wanda ya roqe shi, ya wanda yake kusa da mu fiye da jijiyar wuyanmu

Ka yi mana baiwar samun xebe kewa da kai, da zancenka, ya wanda yake kusa .. “Idan Bayina suka tambayeka danagane da ni, ka ce ni a kusa nake” (Albaqra : 186)

“Makusanci”

Makusanci a cikin xaukakarsa da iliminsa da tsinkayensa na dukkan komai

Makusanci ga kowa da kowa da iliminsa, da saninsa, da kulawarsa, da ganin abin da ake, da kewayewarsa da sanin komai

“Makusanci”

Ga wanda ya kira shi, yana bayarwa yana tausayawa, yana xagewa ya yaye, ya amsawa wanda yake cikin buqata.

“Makusanci”

Ga wanda ya tuba zuwa gare shi, ya ta’allaqa da shi, yana gafarta zunubai, yana karvar tuba.

“Makusanci”

Yana karvar abin da bawansa ya kusance shi da shi, yana kusantar bawansa gwargwadon yadda bawan ya kusance shi.

“Makusanci”

Wanda yake ganin dukkan yanayin da bayinsa suke ciki, babu wani abin da yake voye masa

“Makusanci”

Makusanci da tausayinsa, da kiyayewarsa, da taimakonsa, da qarfafawarsa, wannan na musamman ga bayinsa waliyyansa kaxai.

“Makusanci”

Zuwa gare shi bayinsa za su koma a qarshen lamarinsu..“Mu muka fi kusa da shi fiye da ku” (Alwaqi’a : 85)

“Makusanci”

Zukata suna nutsuwa da shi, su na farin ciki da ambatonsa.

Lallai Allah Makusanci ne


Allah Mai Amsawa

Lallai Allah mai amsawa ne mai girma da buwaya.. “Haqiqa Ubangijina makusanci ne mai amsawa” (Hud : 61)

“Mai amsawa”

Yana amsawa bayinsa idan suka kama qafa gare shi, suka kirawo shi, suka roqe shi. Shi ne wanda ya umarce su da addu’a, kuma ya yi musu alqawarin amsawa.

“Mai amsawa”.. yana amsawa masu roqo duk irin yadda suka kasance, a duk inda suke, a kowanne hali suke ciki.

“Mai amsawa”

Da shi ne fursina ya dogara a cikin kurkunsa, hakanan da shi talaka ya dogara a halin talaucinsa, hakanan maraya a halin maraicinsa, da marar lafiya a lokacin rashin lafiyarsa, da bakararre yayin da ya rasa haihuwa. Kuma duk ya biya musu buqatunsu duka.

“Mai amsawa”

Yana amsawa mai tsananin buqata “Waye yake amsawa wanda yake cikin tsananin buqata idan ya kira shi, kuma ya yaye cuta”. (Annamli : 62)

A lokacin da ya fi kusancin amsa addu’a shi ne lokacin da bawa ya kira shi, ya yi kamun qafa da sunayensa da siffofinsa. Sau tari fursuna ya roqe shi ya fito da shi, wanda ruwan teku ya ci, ya roqe shi ya kuvutar da shi, ya nemi arziqinsa daga talaucin da yake ciki ya azurta shi. Maraya nawa ne ya roqe shi, ya amsa masa ya kula da shi, har ya girma. Mara lafiya nawa ne ya roqe shi lafiya, kuma ya rubuta masa waraka. Nawa wanda ba ya haihuwa ya qasqantar da kai gare shi, ya azurta shi da xa, ya karrama shi.

Lalla Allah mai amsawa ne


Allah Haske ne

Allah Haske ne
 
2498

Allah Haske ne

Lallai Allah haske ne.. “Allah ne hasken sammai da qassai” (Annur : 35)

“Haske”

Wanda ya haskaka zukatar bayinsa, waxanda suka san shi, suka yi imani da shi, ya haskaka zukatansu da shiriyarsa.

“Haske”

Ya tafiyar da duhu da haskensa, ya haskaka sammai da qasa, ya haskaka hanyar masu bautata masa, ya haskaka zukatansu.

Allah haske ne, hijabinsa ma haske ne, da zai yaye shi, da kyan fuskarka ya qona iya inda ganinsa ya tsaya daga cikin halittarsa.

Lallai Allah haske neTags:

 

Allah Mai hikima ne

Lallai shi ne Allah mai hikima.. “Ashe ba Allah ba ne mafi iya hukuncin masu hukunci” (Attiin : 8)

“Mai Hikima”

Wanda ya kyautata komai, yake sanya komai a wurin da ya dace da shi, da qaddarawarsa mai girma da xaukaka.

“Mai hikima”.. shi ne wanda yake da hikima maxaukakiya a cikin halittarsa da al’amuransa, ba ya halittar abu don wasa, baya shar’anta komai haka kawai ba hikima, shi ne wanda yake da hukunci a duniya da lahira.

“Mai hikima”

Ya shar’anta shari’o’i saboda hikimarsa, ya sunnanta sunnoni saboda hikimarsa, Shari’arsa ta kai matuqa wajen hikima, a cikin manufofinta da sirrikanta da sakamakonta duniya da lahira

“Mai hikima”

Mai hikima ne cikin abin da ya qaddara ya hukunta, mai hikima cikin abin da ya zartar ya hukunta, mai hikima ne akan talaka da talaucinsa, ko maras lafiya da rauninsa, ko wanda ake bi bashi da damuwarsa da rashinsa, babu matsala a cikin abin ya shirya, babu tawaya a cikin maganganunsa, ko ayyukansa. Tsarki ya tabbata gare shi ma’abocin hikima ta qarshe.

“Mai hikima”

Wanda ya kimsawa bayinsa hikima da sani da nutsuwa da bi a hankali, ya sanya al’amura a wurin da ya dace da su.

Allah ne mafi hikimar masu hikima, babu wani abu da zai faru a duniyarsa sai da izininsa, shi ne yake halattawa yake haramtawa, abin da ya shar’anta shi ne hukunci, addini shi ne abin da ya yi umarni da shi da abin da ya hana, babu mai cin gyarar hukuncinsa, babu mai mayar da hukuncinsa da qaddararsa.

“Mai hikima”

Ba ya zaluntar kowa, mai adalci ne cikin umarninsa da haninsa, da labarinsa.

Lallai Allah mai hukunci ne mai hikima


Allah Mai Mulki, Mamallaki

Lallai shi ne Allah mai mulki.. “Mai mulki tsarkakakke” (Al-hashru : 23)

“Mai Mulki”

“Mamallaki mai mulki” .. wanda mulki nasa ne, ya siffata da siffar mulki, sifa ce ta girma da xaukaka, da rinjaye da jujjuya al’amura, shi ne wanda yake da cikakken tasrifi a cikin halitta da umarni da sakamako, duniyar sama da qasa ta shi ce, dukkansu bayinsa ne, ababan mallakarsa ne, masu buqata ne a gurinsu.

Ma’abocin girma da xaukaka, yana jujjuya al’amuran bayinsa yana tasarrufi a cikinsu, su bayinsa ne, mabuqata a gurinsa, shi kuma mamallakinsu ne mai mulkinsu.

Yana da mulki cikakken mulki, babu wani sarki ko mai mulki ko shugaba face mallakarsa ne, babu wani alheri a sama ko a qasa face kyautarsa ce da falalarsa.. “Dukkan abin da yake sammai da qasa nasa ne” (Albaqra : 255)

Mai Mulki

“Yana bayarwa babu hisabi, yana kyauta mai yawa ga bayinsa, hakan ba ya rage komai daga mulkinsa, kuma babu wani abu da yake shagaltar da shi. Ya zo a cikin hadisi qudusi : “Da a ce na farkonku, da qarshenku, da mutanenku, da aljanunku, za su tsaya a wuri xaya, su roqi wani abu, kuma in baiwa kowa abin da ya roqa, da hakan ba zai tauye komai daga cikin mulkina ba, sai kamar yadda allura za ta rage daga teku idan an shigar da ita cikinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

“Mai Mulki”

Yana ba wanda ya ga dama mulkinsa. Allah ya ce, “Ka ce Allah mamallakin Mulki kana ba da mulki ga wanda ka ga dama, kana cire wanda ka ga dama, kana xaukaka wanda ka ga dama, kana qasqanta wanda ka ga dama, alheri yana hannunka, haqiqa kai mai iko ne akan dukkan komai” (Al-Imran : 26)

“Mamallaki”

Wanda ya mallaki halittarsa, mai tasarrufi a cikinsu duniya da lahira, don haka bayi su yi kwaxayin abin da yake wajensa, su koma wajensa, su qara kwaxayin abin da yake wajensa, da naci da roqo.

Haqiqa Allah mamallaki ne mai mulki”


Allah Tsarkakakke ne

Shi ne Allah Mai tsarki

Ya tsarkaka a cikin xaukakarsa, yabonsa ya girmama, ni’imominsa sun girmama. “Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai mulki, tsakakakke, mai aminci” (Al-hashru : 23)

“Tsakakakke Mai aminci”.. abin girmamawa, wanda ake tsarkakewa daga siffofin tawaya gabaxayansu, haka nan ya xaukaka daga wani daga cikin halittarsa ya yi kama da shi, ya tsarkaka daga dukkan aibubbuka, ya tsarkaka daga wani ya yi kama da shi a wajan cikar kamala.

Wanda ake wa tasbihi, mai tsarki Ubangijin Mala’ika da Jibrilu, tsarki ya tabbata gare shi mai mulki tsarkakakke

“Lallai Shi ne Allah Tsarkakakke”

Tsarkakakke daga dukkan aibi da naqasa, da duk wata siffa da ba ta dace da shi ba.

“Haqiqa Shi ne tsarkakakke”

Wanda ya siffatu da siffofin kamala da kyau, ya tsarkaka daga tawaya ko aibi, babu wanda ya yi kama da shi, kuma babu wanda ya yi daidai da shi a wajen kamala, wanda ya kai shi a sunaye da siffofi

“Shi ne tsarkakakke”

Wanda zuciya take tsarkakewa, take rataya dukkan burinta gare shi, harasa suke tsarkakewa, suke masa tasbihi a kowane lokaci

“Lallai shi tsarkakakke ne”

Ma’abocin albarka da kyauta, da falala da yabo, albarka daga gare shi take, kuma gare shi za ta koma, shi ne yake albartakar bayinsa, ya yi musu albarka da abin da ya ga dama na kyauta da qari.

Lallai shi Allah tsarkakakke ne


Allah mai aminci

Shi ne Allah mai aminci

Allah ne aminci, kuma daga gare shi aminci yake, bawa ba ya aminta sai da amintarwa Allah, ba a samun nasara sai da datarwarsa.

Lallai shi Aminci ne

Sumul ne daga duk wata tawaya da aibi, mai kuvutar da kowa daga cututtuka da sharri.

Lallai Shi mai aminci ne

Siffofinsa Allah sun kuvuta daga kama da halitta, sun kuvuta daga nau’o’in tawaya da siffofin gazawa. Iliminsa cikakke ne kuvutacce ne, adalcinsa gamamme ne kuvutacce, mulkinsa cikakke ne kuvutacce ne, hukuncinsa kuvutacce ne, hakama aikinsa, shi ne aminci, kuma daga gare shi aminci yake.

Allah ya sanya wa bayinsa aminci a duniya da lahira.. “Aminci ya tabbata ga Ibrahim” (Assaafat : 109) , “Aminci ya tabbata ga Musa da Haruna” (Assaafat : 120) , “Aminci ya tabbata ga Manzanni” (Assaafat : 181)

A lahira ya ce, “Ku shige ta da aminci kuna amintattu” (Al-hujurat : 46)

Aminci

Aminci cikakke wanda babu tsoro a bayansa, da afuwar da babu tsoro bayanta.

Shi ne aminci kuma daga gare shi aminci yake

Shi ne Allah mai aminci


Allah shi ne gaskiya

Allah shi ne gaskiya
 
2614

Allah shi ne gaskiya

Haqiqa Allah shi ne gaskiya.. “Saboda Allah shi ne gaskiya” (Al-hajji : 6)

Allah Shi ne Gaskiya

A cikin zatinsa da siffofinsa, shi ne cikakke a cikin siffofinsa, samuwarsa dole ce, babu wani abu da zai samu in babu shi, shi ne wanda bai gushe ba, kuma ba zai gushe ba da girma da kamala, da kyautatawa

Allah shi ne gaskiya

Maganarsa gaskiya ce, aikinsa gaskiya ne, gamuwa da shi gaskiya ce, manzanninsa gaskiya ne, litattafansa gaskiya ne, addininsa gaskiya ne, bauta masa shi kaxai ita ce gaskiya, duk abin da yake da danganta da shi gaskiya ne. “Saboda Lallai ne Allah shi ne gaskiya, kuma waxanda suke bautawa ba shi ba su ne qarya, kuma lallai Allah shi ne maxaukaki mai girma (Al-hajji : 62)

Haqiqa Allah shi ne gaskiyaTags:

 

Allah shi ne mai gaskatawa mai mamaye dukkan komai

Shi ne Allah mai gasgatawa mai kulawa.. “Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai mulki, tsakakakke, mai aminci, mai gaskatawa mai kulawa” (Al-hashru : 23)

“Mai gaskatawa” .. Wanda ya yabi kansa da siffofi na kamala, da kamalar cika da girma, wanda ya aiko manzanni ya saukar da littattafai da ayoyi da hujjoji, ya gaskata manzanninsa da kowace aya da hujja, wadda take nuna gaskiyarsu da ingancin abin da suka zo da shi.

“Mai amintarwa”

Wanda ta hanyar wahayinsa yake yaxa aminci a tsakanin bayinsa, da zaman lafiya a tsakanin halittarsa, da nutsuwa. “ya amintar da su daga tsoro” (Quraish : 4)

“Mai amintarwa”

Amintacce, wanda ya mamaye dukkan komai, mai shaida akan bayinsa da abin da suke yi.

“Amintacce”

“Mai kulawa”.. Mai ganin voyayyun al’amura da abin zukata suka voye, wanda ya kewaye komai da ilimi.

Wanda ba ya rage lada, ba ya qara uquba. Shi ne mafi cancantar wanda ya yi qari, da ya kyautata.

“Mai kulawa”

Ya mamaye bayinsa, ya rinjaye su, ya kula da su, yana ganin ayyukansu da halinsu, yana kewaye da su, duk wani abu mai sauqi ne a wajensa, kuma komai yana da buqata a wajensa. “babu wanda ya yi kama da shi, shi mai ji ne kuma mai gani” (Asshura : 11)

Shi ne Allah mai gaskatawa mai kulawa


Allah mai afuwa da yawan gafara

Lallai shi ne Allah mai afuwa mai yawan gafara. “Haqiqa Allah mai afuwa ne mai yawan gafara” (Al-hajji : 60)

“Allah mai afuwa da gafara”

Wanda bai gushe ba yana yin afuwa, yana mai siffata da afuwa da gafara, kowa yana buqatar afuwarsa da gafararsa, kamar yadda kowa yake buqatar rahamarsa da karamcinsa.

Ya wanda ya yi alqawarin gafara da afuwa ga wanda ya zo da sabubbanta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce “Ni mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba, ya yi imani ya yi aiki na qwarai sannan ya shiriya” (Xaha : 82)

Muna roqonka, ya mai gafara ka azurta mu da tuba na gaskiya, wadda za mu bar zunubanmu da ita, mu yi nadama akan abin da muka yi na savo da wanda ba daidai ba, kuma mu qara azama da ita a wajen bauta maka. Ka gafarta mana ya mai yawan gafara.

Ya Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi mana afuwa, Ya Allah ka ba mu labari kai mai gafara ne mai jin qai.. “Ka ba bayina labari cewa nine mai gafara mai jin qai” (Al-hujrat : 49)

Ka ji qanmu, ka yi mana gafara, ya mai yawan gafara.

Haqiqa shi ne Allah mai yawan gafara da gafartawa


Allah Mai karvar tuba

Shi ne Allah mai karvar tuba.. “Lallai Allah mai yawan karvar tuba ne mai jin qai” (Attaubah : 118)

“Mai karvar tuba”.. Wanda bai gushe ba yana karvar tuban masu tuba, yana gafarta zunuban masu zunubi, duk wanda ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, Allah zai karvi tubansa, shi ne wanda yake sanya masu tuba su tuba, ta hanyar datar da su, da fuskantar da zukatansu zuwa gare shi, shi ne yake karvar tubansu, idan sun tuba, ya yafe musu kurakuransu.

“Mai Karvar Tuba”

Wanda ya shar’antawa bayinsa tuba, saboda falalarsa da karamcinsa, ya yi musu alqawari da abin da ya fi haka yawa, shi ne ya sanya munanan ayyukansu su zama masu kyau.

“Mai karvar tuba”

Wanda yake tabbatar da bayi akan tubansu, ya taimake su akan abin da ya xora musu na ayyuka.

“Mai karvar Tuba”

Wanda yake datar da bayinsa zuwa ga tuba, ya kwaxaitar da su, ya sanya musu sonta.

“Mai karvar tuba”

Wanda yake karvarta daga bayinsa, ya ba su lada, ya xaukaka musu darajan, ya kankare musu zunubai, Allah mai girma da buwaya

Haqiqa shi Allah mai karvar tuba ne”


Allah shi ne xaya tilo

Haqiqa Allah Shi ne tilo

Ya wanda yake shi kaxai ne a cikin zatinsa, shi kaxai a sunayensa, shi kaxai a siffofinsa.

Muna roqonka tsarkin zuciya da so, da fata. Ya wanda yake shi kaxai wanda ake nufi da buqata.

“Shi kaxai tilo”

Guda xaya tilo.. Wanda ya kaxaita da dukkan kamala, babu wanda ya yi tarayya da shi a ciki. Kuma wajibi ne akan bayi su kaxaita shi, a tunaninsu, da maganganunsu da ayyukansu, su yarda da kamalarsa da kaxaitakarsa, su bauta masa shi kaxai

Tilo a cikin zatinsa, da sunayensa, da siffofinsa, baya da kishiya ko makamanci, ko kishiya ko kini. “Shin ka san takwara gare shi” (Maryam : 65)

“Tilo”

Tilo cikin alantakarsa, wanda ya cancanci bauta, babu wani wanda za a bautawa da gaskiya sai Allah, ba a juyar da ibada kaxan ko mai yawa ga wanin Allah.

“Tilo”

Shi kaxai tilo wanda ake nufata. Ubangiji abin bauta, dukkan zukata sun yi masa shaida, idanuwa sun ratayu da shi, masanin gaibu.

Shi xaya kaxai tilo”

Allah ya halicci bayi akan kaxaita shi, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya, babu wanda ya fuskanci waninsa ya samu nasara, ko ya bauta wa waninsa ya samu sa’ida, ko ya yi shirka da shi ya tsira.

Haqiqa Allah xaya ne shi kaxai tilo.


Allah wanda ake nufa da buqata

Haqiqa Allah shi ne wanda ake nufa da buqata.. “ka ce shi ne Allah xaya. Allah wanda ake nufata da buqata” (Al-ikhlas : 1 – 2)

“Wanda ake nufa da buqata”

Cikakke a sunayensa da siffofinsa, ba wata tawaya ko gazawa dake samunsa

“Wanda ake nufa da buqata”.. Wanda halittu gabaxayansu suke nufa da dukkan buqatunsu da lalurorinsu da halayensu, saboda kamalar cikarsa, a zatinsa da sunayensa da siffofinsa da ayyukansa.

“Wanda ake nufa da buqata”

Mawadacin da kowa yake buqatarsa, shi kuma ba ya buqatar kowa.. “yana ciyarwa shi kuma ba a ciyar da shi” (Al-an’am : 14)

“Wanda ake nufa da buqata”

Ubangiji mai jujjuya al’amura, mai mulki, mai tasrifi.

“Wanda ake nufa da buqata”

Zukata sun fuskance shi da buqatu, ya ba su bai hana su ba, sun kirawo shi akan buqatunsu, ya yaye musu damuwa ya amsa musu. Waxanda suka bar shi sun kirawo shi ya ba su, waxanda suke jin tsoro sun koma wajensa ya amintar da su, masu tauhidi sun yi fata a wajensa, ya ba su abin da suka yi fata, waxanda suke cikin musiba sun kirawo shi, ya kuvutar da su, dukkan bayi sun sunkuyar da kai gare shi.

Haqiqa shi ne Allah wanda ake nufa da buqata


Kuma Allah Mabuwayi

Kuma Allah Mabuwayi
 
3134

Kuma Allah Mabuwayi

Haqiqa Allah Mabuwayi ne mai girma da xaukaka.. “Allah mabuwayi ne mai hikima” (Al-anfal : 67)

Allah mabuwayi mai qarfi mai rinjaye.

Wanda qarfin mai qarfi ba ya cutar da shi, kuma ikon mai iko ba ya gajiyar da shi, albarkarsa ta yawaita maxaukaki masani.

“Mabuwayi”.. Wanda yake da buwaya gabaxaya, buwayar qarfi, buwayar rinjaye, buwayar kariya, babu wanda zai iya cutar da shi daga halittunsa, ya rinjayi dukkan halitta, kuma sun sunkuyar da kai gare shi, saboda girmansa.

“Mabuwayi”

Buwayarsa ta cika, kowa da kowa ya sunkuyar da kai gare shi, duk wani mai qarfi ya yi rauni a gabansa, duk wanda ba shi ba qasqantacce ne, duk wani mahluki na qasqanta ne a gurinsa.

“Mabuwayi”

Yana ba wanda ya ga dama buwaya, yana qwaceta daga wanda ya ga dama, yana qasqanta wanda ya ga dama, a hannunsa alheri yake, Allah ya ce, “Haqiqa buwaya gabaxayanta ta Allah ce” (Yunus : 65)

Babu wata xaukaka ta nasaba ko matsayi ko dukiya, sai daga wajensa kuma daga gare shi.

“Mabuwayi”

Ba wanda yake xaukaka sai da xaukakarsa, ba mai qarfi sai da falalarsa, duk wanda zai fake ya fake da shi, duk wanda yake neman xaukaka to ya fuskanci Allah da zuciyarsa... “Xaukaka ta Allah ce da Manzonsa da Muminai” (Almunafiqun : 8)

Haqiqa Allah mabuwayi neTags:

 

Allah Mai qarfi mai rinjaye

Shi ne Allah mai qarfi mai rinjaye

Wanda ya rinjayi mutum da aljan da samansu “Kuma Shi ne mai rinjaye a saman bayinsa, shi ne mai hikima masani” (Al-an’am : 18)

“Mai rinjaye”

Ya rinjayi halittarsa ta hanyar xaukakarsa, da iliminsa, da kewayewarsa ga komai, da tsarawarsa, da xaukakarsa a kansu, babu wani abu a wannan duniya mai faxi face da izininsa da saninsa.

“Mai qarfi da rinjaye” .. Mai rinjayar dukkan komai, wanda dukkan halittu suka sunkuya masa, suka qasqantar da kai ga buwayars da cikar ikonsa

“Mai rinjaye”

Wanda ya rinjayi masu taurin kai da girman kai da manya-manya hujjoji, mabayyana, a kan cancantarsa da bauta shi kaxai, da cancantar kaxaita shi da bauta da ayyuka da sunaye da siffofi maxaukaka

“Mai rinjaye”

Wanda ya rinjayi azzalumai da masu xagawa da girman kai, zai tara su suna ababan rinjaya ba tare da son su ba.. “Suka bayyana ga Allah shi kaxai mai rinjaye” (Ibarahim : 48)

“Mai rinjaye”

Abin da ya so yana faruwa, ba wanda ya isa ya mayar da shi daga cikin halittarsa ko meye girmansa. Kyakkyawan aikinsa ya gagare masu qarfi kowane irin qarfi kuwa, harasa suna gaza bayanin kyan halittarsa, duk yadda suka kai da qwarewa da gwanancewa.

Haqiqa Allah shi ne Mai qarfi mai rinjaye


Allah mai azurtawa

Shi ne Allah mai azurtawa.. “Haqiqa Allah shi ne mai tsananin karfi” (Azzariyat : 58)

“Mai azurtawa”

Wanda arziqin bayi yake hannunsa, shi ne wanda yake shimfixa arziqi ga wanda ya so daga cikin bayinsa ya qaddara masa abin da ya so, a hannunsa. Makullan sammai da qasa suke a gunsa. Allah maxaukakin Sarki ya ce, “babu wata dabba a bayan qasa face arziqinta yana ga Allah, ya san matabbatarta da ma’ajiyarta” (Hud : 6)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Dabba nawa ce da bata xauke da arziqinta Allah ne yake azurtata da ku gabaxaya. Shi ne mai ji masani” (al’ankabut : 60)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Haqiqa Ubangijinka yana shimfixa arziki ga wanda ya ga dama ya Quntata shi ga wanda ya ga dama. Haqiqa shi dangane da bayinsa masani ne mai gani” (Al-isra’i : 30)

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Allah yana azurta wanda ya ga dama ba tare da lissafi ba” (Albaqra : 212)

“Mai azurtawa”

Dukkan mutane mabuqata ne, gare shi da arzikinsa, yana azurta dukkan mutane, nagarinsu da fajiransu, na farkonsu da na qarshensu.

“Mai azurtawa”

Yana azurta wanda ya fuskance shi da zuciya mai kyau, gyaruwar zukata shi ne mafi girma arziki. Yana kwarara ilimi da imani ga wanda ya roqe shi, yana ba da arziqi na halal ga wanda ya neme shi, wanda yake taimakawa wajen gyara zuciya, da gyaruwar addini, ga wanda ya bukaci hakan daga wajensa.

Lallai Shi ne Allah Mai azurtawa


Allah mai tausasawa ne

Shi ne Allah mai tausasawa.. “Haqiqa Ubangijina mai tausasawa ne ga wanda ya ga dama” (Yusuf : 100)

Mai tausasawa

Wanda yake horewa halitta wata halittar don tausasawa da jin qai da qauna.

Mai tausasawa

Mai bayar da manya – manyan kyaututtuka masu yawa,

“Mai tausasawa”.. Wanda iliminsa ya kewaye dukkan abin da yake voye da fili, ya san voyayyu da qananan abubuwa, mai tausasawa bayinsa muminai, mai sada su da maslaharsu da tausayinsa da kyautatawarsa ta hanyar da ba su sani ba.

Mai Tausasawa

Mai tausasawa bayinsa.. “Allah mai tausasawa bayinsa ne” (Asshuura : 19)

Yana ba su abin da yake alheri a cikin addininsu da duniyarsu, ya kuma kare su daga abin da yake sharri gare su a duniyarsu da addininsu.

Mai tausasawa

Gannai ba sa iya riskarsa, shi ne yake riskar gannai… “Gannai basa iya riskarsa, shi ne yake iya riskar gannai, shi mai tausasawa masani mai ba da labari” (Al-an’am : 103)

“Mai tausasawa”

Ya san voyayyun abubuwa, yana lissafa qananan ayyuka, babu wani abu da zai vuya gare shi da dare ko rana. Ya san abin da ya dace da bayinsa, qanana da manya, yana tausaya musu.

Mai tausasawa

Yana tausasawa bayinsa idan ya hukunta wani lamari, yana taimaka musu idan ya qaddara abu, yana buxe musu qofofin farin ciki idan lamarin ya tsananta, ya kawo musu sauki idan lamari ya ta’azzara.

Lallai Shi ne Allah mai tausasawa


Allah Mai hukunci mai buxewa

Tabbas shi ne Allah mai hukunci.. “Shi ne mai hukunci masani” (Saba : 26)

“Mai Hukunci da buxewa”

Yana buxe mana rahamarsa. “Abin da Allah ya buxewa mutane na rahamarsa babu mai riqe shi” (Faxir : 2)

“Mai hukunci da buxewa bayinsa”

“Mai hukunci”.. Wanda yake hukunci da hukunce-hukuncensa da shari’onsa tsakanin bayinsa, hukunce-hukuncensa waxanda ya qaddara, da sakamako, wanda da tausayinsa ya buxe basirar masu gaskiya, ya buxe zukatansu da son shi da koma zuwa gare shi, ya buxewa bayinsa rahama da arziki kala-kala

Ya buxe mana, mu da ku albarkarsa, ya ba mu wani abu daga cikin falalarsa da kyautarsa, ya qara mana daga afuwarsa da kyautarsa.

Shi ne Allah mai buxe abin da ya rufe zukata, da mabuxan shiriya da imani

“Mai Hukunci da Buxewa Bayi Alheri”

Yana buxe qofofin rahama ya sako ta, ya kwararo musu ni’ima, ya qara, ya buxe musu hasken ilimi da hikima ga hankulansu, ya qawata su, ya buxe zukata da imani ya shiryar da su.

“Mai hukunci da buxewa”

Wanda yake yaye wa bayi damuwa, ya yaye musu baqin ciki da duk wata cuta.

“Mai hukunci da buxewa”

Wanda yake buxe kofar adalci ga bayinsa a lahira, shi ne majivinci sha yabo.

Haqiqa Allah shi ne mai hukunci


Allah ne mawadaci Mai wadatarwa

Shi ne Allah mawadaci mai wadatarwa

“Mawadaci”

Wadatar zati, wanda yake da wadata cikakkiya, babu wata tawaya ko aibi a cikin siffofinsa ta kowace irin fuska, kuma koyaushe a wadace yake, saboda wadatarsa tana daga siffofin zatinsa, kamar yadda ya zama mai halitta ba, mai iko, mai kyautatawa. Baya buqatar kowa ta kowace fuska, shi ne mawadacin da taskokin sammai da qasa suke hannunsa, da taskokin duniya da lahira. Kuma mai wadatar da dukkan halittarsa wadata gamammiya.

Mawadaci

Mawadaci ga barin bayinsa, baya buqatar abinci ko abin sha a wurinsu, bai kuma halicce su ba don ya qara yawa da su saboda qaranci, ko kuma ya yi qarfafa da su, ko ya xebe kewa da su, a’a su ne suke da buqatarsa a wajen abincinsu da abin shansu da sauran al’amuransu. Allah Maxaukakin Sarki ya ce,.. “Ban halicci aljanu da mutune ba sai don su bauta min. Ba na buqatar wani arziki daga wajensu, kuma ba na buqatar su ciyar da ni” (Azzariyat : 56 – 57)

Mai wadatarwa

Ya wadatar da mutane daga talaucinsu da buqatunsu, kyautarsa ba ta rage masa komai ba, kuma bayinsa ba sa buqatar wani wanda ba shi ba. Kamar yadda ya zo a cikin hadisi qudusi : “Da a ce na farkonku da na qarshenku da mutananku da aljanunku za su tsaya a wuri xaya, su roqe ni , in baiwa kowa abin da ya roqe ni, da hakan ba zai tauye abin da yake wurina ba, sai dai kamar abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita teku” (Muslim ne ya rawaito shi)

“Mai Wadatarwa”

Ya wadatar da wasu daga cikin bayinsa ta hanyar shiryar da su zuwa ga gyaruwar zuciyarsu, da saninsa da xaukaka shi da girmama shi, da son shi, sai ya wadatar da su da abin da ya fi cika da kaiwa matuqa daga gyaruwar duniyarsu.

Ya wanda kyauta ba ta rage abin da yake wajensa, ka wadatar da mu da halal xinka daga barin abin da ka haramta, haqiqa kai mawadaci ne mai wadatarwa.

Haqiqa shi Allah mawadaci ne mai wadatarwa.


Allah ne mai ciyarwa

Haqiqa Shi Allah mai ciyarwar ne “Allah ya kasance mai kiyayewa akan dukkan komai” (Annisa’i : 85)

Mai ciyar da kowa da komai.. Wanda ya isar wa da dukkan komai abin da zai ci, ya ba wa dukkan halitta arziqinta, ya sarrafa shi yadda ya ga dama da hikimarsa da godiayrsa.

“Wanda yake ciyar da kowa”

Wanda ya isarwa da dukkan halittu abincinsu, ya halitta musu abin da za su rayu da shi, ya ba su abin da za su sha ya qosar da su, ya ba su rayuwa mai kyau.

Mai ciyarwa

Wanda yake ciyar da zukata da ilimi kala-kala, ta rayu da shi, hankula su kwanta da shi.

Ya Allah wanda yake tsaye da sha’anin bayi, da jujjuya rayuwarsu da makomarsu, kiyayewarka da afuwarka da lafiyarka muke nema.. “Allah ya kasance mai kiyayewa akan dukkan komai” (Annisa’i : 85)

Haqiqa Allah shi ne mai ciyar da dukkan komai mai kula da shi.


Allah Shi ne mai isa

Haqiqa shi ne Allah mai isa

Allah ya isarwa bayinsa, ya ishe su daga barin dukkan komai.. “Ashe Allah ba mai isa ne ga bawansa ba?” (Azzumar : 36)

&"Mai isa&"..Wanda ya kewaye da sanin komai daki-daki, ya san shi ciki da bai, ya san abin da halittunsa suka voye.

Allah ya isar mana kuma madallah da abin dogara.... Annabi Ibrahim ya faxi haka yayin da aka jefa shi wuta, sai ta zama sanyi da aminci gare shi. Haka ma sahabbai sun faxe ta, kamar yadda yake cikin faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Lallai mutane sun yi yi muku taron dangi…” (Al – Imran : 173)

Sai suka ce,. “Allah ya isar mana, kuma madallah da abin dogara. Sai suka juya da ni’ima daga Allah da falala, ba wata cuta da ta same su, suka bi yardar Allah” (Al-imran : 173 – 174)

Allah ne mai hisabi, wanda yake yi wa bayinsa hisabi, yana lissafa musu ayyukansu, ya saka musu bisa ayyukansu, alheri da alheri, sharri da sharri, sakamakon abin da suka aikata. “Shi ne mafi saurin masu hisabi” (Al’an’am : 62)

Mai Isarwa.. Ya isar wa bayinsa da dukkan abin da suke nema, kuma suke buqata, ya ishi wanda ya yi imani da shi, ya dogara da shi, ya nemi buqatunsa na duniya da lahira a wajensa, ya ishe shi, isa kevantacciya,

“Mai isa”

Wanda ya kewaye da sanin komai daki-daki, ya san shi ciki da bai, ya san abin da halittunsa suka voye.

Ya Ubangiji ka isar mana sharrin abin da ya dame mu, ka kimsa mana shiriyarmu, ka qara mana alheri ya mai karamci.. “Allah ya isa Gwanin Hisabi” (Annisa’i : 6)

Haqiqa shi Allah shi ne mai hisabi da wadatarwa


Allah ne Mabayyani

Lallai Allah shi ne Mabayyani.. “Lallai Allah shi ne gaskiya mabayyani” (Annur : 25)

Ya wanda yake Mabayyani, ka bayyana mana hanyar gaskiya, ka tseratar da mu daga haxewar hanyar gaskiya da ta qarya, ya Ubangiji.

Allah mai bayyana gaskiya ne da dukkan wasu abubuwa, a lokacin duk shakka zata kau.

Lamarin kaxaitakar Allah a bayyane yake, ba shi da abokin tarayya

“Mabayyani”

Ba ya vuya ga halittarsa saboda abin da ya sanya na alamomin hankali da shari’a na zahiri, waxanda suke nuna samuwarsa da kyautarsa, da kuma ikonsa.

“Mabayyani

Wanda ya bayyanawa bayinsa hanyar gaskiya, ta hanyar aiko musu da Manzon Allah (S.A.W) da littafi bayananne.. “Haqiqa wani haske da wani littafi mabayyani sun zo muku daga Allah” (Alma’idah : 15)

Allah wanda ya bayyana hanyar sa’ida ga bayinsa, ya gwama ta da yi masa xa’a da kaxaita shi a wajen bauta.

Haqiqa Allah Mabayyani ne


Allah ne Mabayyani

Lallai Allah shi ne Mabayyani.. “Lallai Allah shi ne gaskiya mabayyani” (Annur : 25)

Ya wanda yake Mabayyani, ka bayyana mana hanyar gaskiya, ka tseratar da mu daga haxewar hanyar gaskiya da ta qarya, ya Ubangiji.

Allah mai bayyana gaskiya ne da dukkan wasu abubuwa, a lokacin duk shakka zata kau.

Lamarin kaxaitakar Allah a bayyane yake, ba shi da abokin tarayya

“Mabayyani”

Ba ya vuya ga halittarsa saboda abin da ya sanya na alamomin hankali da shari’a na zahiri, waxanda suke nuna samuwarsa da kyautarsa, da kuma ikonsa.

“Mabayyani

Wanda ya bayyanawa bayinsa hanyar gaskiya, ta hanyar aiko musu da Manzon Allah (S.A.W) da littafi bayananne.. “Haqiqa wani haske da wani littafi mabayyani sun zo muku daga Allah” (Alma’idah : 15)

Allah wanda ya bayyana hanyar sa’ida ga bayinsa, ya gwama ta da yi masa xa’a da kaxaita shi a wajen bauta.

Haqiqa Allah Mabayyani ne


Allah Mai gado ne

Shi ne Allah Mai gajewa.. “Lallai mu muna rayawa muna kashewa, kuma mu ne magada” (Al-hijir : 23)

Mai gado”

Wanda yake gaje qasa da waxanda suka kanta, babu wani abu da zai yi saura sai shi, mai girma da buwaya

“Mai gado”

Wanda zai dauwama bayan halittarsa, saboda cikar mulkinsa, kuma zuwa ga mulkinsa kowane mai mulki zai koma. Yana gargaxin duk wanda ya yi zalunci ya yi girman kai cewa makoma tana wajensa, domin shi ne mai gado.

“Mai gado”

Yana kwaxaitar da bayinsa akan ciyarwa saboda shi. Dukiya abin aro ce, rayuwa kuma tafiya take, komawa kuma za ta kasance zuwa Allah mai gaje dukkan komai

“Mai gado”

Yana gargaxin bayinsa da su guji butulce masa, saboda asalin ni’ima daga gare shi ne, kuma gare shi za ta koma.

“mai gado”

Yana gaje qasa da waxanda suke kanta, duk kuwa wanda zai wanzu bayan wani ya tafi to shi ne Mai gado.. “Mun kasance mune masu gado” (Al-qasas : 58)

Haqiqa shi Allah mai gajewa


Allah mai ji mai gani

Shi ne Allah mai ji mai gani

Ya wanda yake ji, ka saurari addu’o’inmu, ka amsa mana, kai ne mai ganin ayyukanmu, da gazawarmu da buqatunmu, kai kaxai.

Allah mai ji

Yana jin muryoyi dukkansu, masu rauni da masu qarfi, wata muryar ba ta hana shi ya ji wata, wani mai roqo baya ha na shi jin wani mai roqon.

“Mai ji mai gani”.. Yana jin maganarka, don haka ka yi wa kanka hisabi, yana jin addu’arka, don haka ka nace masa, yana ganin ayyukanka, kada ka voye masa komai, ka kyautata, Allah yana son masu kyautatawa.

Allah mai gani ne

Yana ganin komai, duk qanqantarsa ko girmansa, ko voyayye ciki dare ko rana.

Mai ji

Yana jin magana, duk da savanin yaruka, da buqatu kala-kala

“Mai Gani”

Yana ganin tafiyar baqar tururuwa a cikin duhun dare, a kan kurman dutse. Yana ganin abin da yake qasan bakwai, kamar yadda yake ganin abin da yake saman bakwai.

Mai ji mai gani

Babu wani abin da yake voye masa, babu wani abin da yake guje masa.

Haqiqa shi mai ji ne mai gani


Allah Mai godiya Abin godewa

Shi ne Allah mai godiya abin godewa

Shi ne Allah mai godiya.. “To haqiqa Allah mai godiya ne masani” (Albaqra : 158) , “Haqiqa Ubangijinmu mai yawan gafara ne mai godiya” (Faxir : 34)

Allah shi ne mai godewa aiki kaxan, ya gafarta zunubi mai yawa, ya ninnika ladar masu tsarkake aiki gare shi, ba tare da wani lissafi ba.

“Allah Mai yawan godiya”

Yana bawa wanda ya gode masa, ya yi falala ga wanda ya roqe shi, ya ambaci wanda ya ambace shi, wanda ya gode yana da qari, wanda ya kafirce kuwa ya yi hasara. Allah ya ce “Idan kuka gode tabbas zan qara muku, idan kuwa ku ka yi butulci to azaba ta mai tsanani ce” (Ibrahim : 7)

“Lallai shi Allah mai godiya ne abin godewa”


Allah Sha Yabo

Haqiqa shi ne Allah sha yabo

Abin yabo a zatinsa, abin yabo a ayyukansa, abin yabo a halayensa, abin yabo a maganganunsa, babu wani abin yabo a duniyae nan sai Allah (S.W.T), dukkan yabo da kirari nasa ne, tsarki ya tabbata a gare shi.

Sha yabo

Sha yabo a zatinsa, da sunayensa, da sifofinsa, da ayyukansa, yana da sunaye mafiya kyau, siffofi mafiya cika, ayyuka mafiya kyau da cika, dukkan ayyukansa suna kewayawa tsakanin falala da adalci. Godiya taka ce, kai kaxai. Ka saukar mana da littafinka, ka sanar da mu girmanka da xaukakarka, ka aiko mana manzonka Muhmamad (S.A.W)

Lallai Shi ne Allah sha Yabo


Allah sha yabo, mai girma, mai xaukaka

Shi ne Allah abin yabo da girma da xaukaka

Shi ne Allah wanda ya siffatu da siffofin girma, da xaukaka, wanda ya fi komai girma, ya fi komai xaukaka. Yana da girma da xaukaka a cikin zukatan masoyansa zavavvun bayinsa. Zukatansu sun cika da girmansa da xaukakarsa, da qasqantar da kai gare shi.

Tsarki ya tabbata gareka. Ya girma mene ne ya yi girmanka!!... “Ka tsarkake sunan Ubangijinka mai girma” (Alwaqi’a : 96)

Ba za mu iya lissafa yabo a gareka ba, da girmanka. Ya mai girma. Ya ma’abocin girma da karamci.

Mai girma cikin zatinsa, mai girma cikin sunayensa da siffofinsa… “Babu abin da ya yi kama da shi” (Asshura : 11)

Shi ne ma’abocin girma da xaukaka, duk wanda ya ja da shi a cikin haka, zai karya shi, kamar yadda Allah ya faxa a cikin hadisi qudusi : “Nuna isa mayafina ne, girma kuma kwarjallena ne, duk wanda ya yi ja da ni a cikin xaya daga cikinsu zan jefa shi a wuta” (Ahmad ne ya rawaito shi)

Shi ne Allah abin mai girma da xaukaka


Allah maxaukaki mafi xaukaka

Shi ne Allah maxaukaki mafi xaukaka.

Maxaukaki Mai xaukaka.. Yana da xaukaka a akan dukkan bayinsa, xaukakar zati, da xaukakar daraja, da xaukakar siffa, da xaukakar rinjaye.. (Shi ne Maxaukaki mai girma) (Albaqra : 255)

Ya daidaita a kan al’arshi, da dukkan siffofin girma da xaukaka da kyau, da cikar kamala ta qarshe da nuna isa.

“Maxaukaki Mafi xaukaka”

Ya xaukaka daga duk wata siffa da ba ta dace da shi ba, da duk wata tawaya. Ya xaukaka a zatinsa da siffofinsa da karfinsa, shi ne Allah Maxaukaki

Shi ne Allah Maxaukaki Mafi xaukaka


Allah Mai Riqewa Da Shimfixawa

Shi ne Allah mai riqewa da shimfixawa

“Allah Mai Riqewa”

Ya riqewa wasu mutane arzikinsu don ya jarrabe su. Yana hana wasu don ya tanqwara su, ya tsare na wasu nasu don ya xaukaka su.

“Allah Mai Shimfixawa”

Ya shimfixa arziki, ya shimfixawa zukata saninsa, duk wannan da hikimarsa da rahamarsa da kyautarsa, tsarki ya tabbata a gare shi.

Lallai Shi ne Allah mai riqewa da shimfixawa


Allah Mai Bayarwa Mai Hanawa

Lallai Shi ne Allah mai bayarwa mai hanawa

Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kamar yadda ya siffata kansa, sama da yadda halittarsa suka siffata shi.

Imam Shafi›i

“Allah mai bayarwa mai hanawa”.. Ba wanda zai hana abin da ya bayar, ba kuma mai ba da abin da ya hana, dukkan wata maslaha da amfani a wurinsa ake nema, a wurinsa ake kwaxayinsu, shi ne mai bayarwa ga wanda ya ga dama, yana hana wanda ya ga dama da hikimarsa da rahamarsa.

Ya mai shimfixawa, shimfixa mana daga rahamarka, ka ba mu daga kyautarka, ka kame mana mummuna ya mai kamewa, ka kare mana sharri da mummuna ya wanda yake hanawa.

Shi ne mai bayarwa mai hanawa