Soyayya 1

Soyayya 1

Soyayya

Abin da ake nufi da son Allah

Duk wanda ya san Allah sai ya so shi

Son Allah: Shi ne zuciya ta nutsu da Allah, da karkata gare shi, ta amsa masa cikin dukkan abin da yake so, ambaton Allah ya mamaye dukkan zuciyar

Haqiqanin Son Allah

Son Allah shi ne son ibada da qanqan da kai da girmamawa, ya zama a cikin zuciyar masoyi akwai gimama wanda yake so, wato Allah, abin da zai kai zuwa ga kamanta umarninsa, da nisantar abin da ya hana. Wannan son shi ne tushen imani da tauhidi, akwai falala mai yawa a kansa wadda ba za su lissafu ba. Yana daga cikin son Allah son abin da Allah yake so, na wurare da lokuta da mutane, da ayyuka da maganganu, da wasunsu daga abubuwan da Allah yake so

Kamar yadda son Allah ya wajaba ya kasance don shi kaxai aka yi, amma wannan ba ya karo da so na xabi’a, kamar son xa ga mahaifinsa, da mahaifi ga xansa, da xalibi ga malaminsa, ko kamar son abinci da abin sha, da aure, da tufafi da abokai da sauransu.

Babu wani abin da aka bautawa Allah da shi kamar so da tsoro da fata.

Amma haramtaccen so shi kamar haxa Allah da wani cikin soyayya, kamar irin son da mushirikai suke yi wa gumakansu da waliyyansu, ko kuma gabatar da son zuciya akan abin da Allah yake so, ko son abin da Allah ba ya son shi, na lokuta da wurare da mutane da ayyuka da maganganu, kuma shi ma wannan son hawa-hawa ne. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Daga cikin mutane akwai wanda yake riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah, suna son su kamar yadda suke son Allah, waxanda suka yi imani sun tsananan son Allah. (Albaqra : 165)

Daga cikin Falalar Son Allah

1-Ita ce tushen tauhidi. Tsarkake soyayya ga Allah shi kaxai shi ne ruhin tauhidi, kai ita ce ma haqiqanin bauta, tauhidi baya cika har sai son bawa ga Ubangijinsa ya cika, kuma son Allah ya riga yi duk wata soyayya, ta yarda zai kasance dukkan abin da bawa yake so yana bin bayan abin da Allah yake so, da irin wannan soyayya ne bawa yake samun arziki da rabo.

Shauqin zuwa ga Allah da son gamuwa da shi wani abu ne da yake tasowa daga zuciya don ya tafiyar da zafin duniya.

2-Jin rarrashi yayin afkuwar masifa : Masoyi yana samun daxin soyayya da zai sa shi ya manta da masifa, kuma ta zama mai sauqi a kanshi.

Babu wanda ya fi tavewa a bayan qasa fiye da wanda aka hana masa samun nutsuwa da Allah mai girma da buwaya.

3-Samun cikakkiyar ni’ima da farin ciki mai yawa : hakan baya samuwa sai da son Allah mai girma da buwaya, babu abin da yake wadatar da zuciya, ya kare mata buqatarta, ya qosar da yunwarta sai son Allah da fuskantarsa mai girma da buwaya. Da mutum zai samu dukkan abin da ake jin daxi da shi, ba zai samu nutsuwa ba da kwanciyar hankali sai da son Allah, don haka son Allah shi ne ni’imar zuciya, lafiyayyun zukata da lafiyayyun hankula ba su da abin da ya son Allah da shauqin gamuwa da shi daxi da farin ciki a garesu, daxin da mumini yake ji a zuciyarsa yana sama da kowane daxi, ni’imar da yake ji tafi kowace ni’ima cika, daxin da take ji ya fi kowane daxi. “Abubuwa guda uku, wanda yake da su, to ya samu zaqin imani, Allah da Manzonsa su zama mafi soyuwa a wurinsa fiye da waxanda ba su ba. Ya so mutum ba ya son shi sai don Allah. Ya qi ya koma kafirci kamar yadda yake qin a jefa shi a wuta” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi)

Abubuwan Da Suke Jawo Son Allah

Ubangijinmu Allah mai girma da buwaya yana son wanda yake son shi, da wanda ya kusance shi, saboda haka farkon abin da yake jawo son Allah Maxaukakin Sarki shi ne bawa ya so Ubangijinsa son da ba ya yima wani daga cikin halitta. Ga bayanin abubuwan da suke jawo son Allah Maxaukakin Sarki gasu kamar haka :

1-Karanta Alqur’ani da fahimtar ma’noninsa da abin da ake nufi da su : Duk wanda ya shagala da littafin Allah ya yi aiki da shi, to za a raya masa zuciya da son Allah.

2-Kusantar Allah da nafilfili bayan an yi farillai “Bawana bai zai gushe ba, yana kusantata da nafilfili har sai na so shi, idan na so shi, sai in zama jinsa da yake ji da shi, in zama ganinsa da yake gani da shi, in zama hannunsa da yake damqa da shi, in zama qafarsa da yake tafiya da ita, idan ya roqe ni zan ba shi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina tabbas wallahi zan tsare shi (Hadisi Qudusi Bukhari ne ya rawaito shi)

3-Dauwama a cikin ambaton Allah a kowane lokaci da harshe da zuciya da aiki da hali

4-Gabatar da abin da Allah yake so akan abin da zuciya take so, na kwaxayi da sha’awar duniya

“Yana son su, kuma su ma suna son shi” (Alma’idah : 54)

5-Tsinkayo sunayen Allah da sifofinsa da saninsu a cikin zuciya.

6-Kallon kyautatawar Allah da ni’imominsa na fili da na voye.

7-Karyewar zuciya a gaban Allah mai girma da buwaya.

8-Kaxaita da Allah a qarshen kashi uku na dare, a lokacin da Ubangijinmu yake sauka zuwa ga sama ta kusa, sai bawa ya kevanta da Allah ya gana da shi, ya karanta littafinsa, ya yi ladabi a gabansa, yana tsaye yana sallah, ya cika da tuba da neman gafara.

9-Zama da masoya Allah na gaskiya, da zavar maganganunsu masu daxi, kamar yadda yake zavar ‘ya’yan itace mai daxi, da rashin magana sai yayin da maslahar maganar ta bayyana, ya bayyana akwai amfanuwar wani a cikin maganar

10-Nisantar dukkan wani abin da yake shiga tsakanin zuciya da Allah, mai girma da buwaya

Daga Cikin Amfanin Allah Ya So Bawa

Duk wanda Allah ya so shi, zai shiryar da shi ya kusantar da shi gare shi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ni ina akan yadda bawana ya zace ni, ina tare da shi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni a cikin ran shi, sai in ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin taro, sai in ambace shi a cikin taron da ya fi nashi alheri, idan ya kusace ni xani xaya, sai in kusace shi zira’i xaya, idan ya kusace ni zira’i, sai an kusace shi kamu, idan ya zo min yana tafiya, zan zo masa ina sarsarfa. (Sahihul Bukhari)

Don haka duk lokacin da bawa ya ji tsoron Ubangijinsa sai ya samu wata shiriyar, a duk lokacin da ya so Allah, sai ya qara masa shiriya, duk lokacin da ya shiryu zai tsoron Allansa ya qaru.

Duk wanda Allah ya so shi, zai rubuta masa karvuwa a bayan qasa

Abin da ake nufi karvuwa ga wannan bawan da Allah yake so, da karkata zuwa gare shi, da yarda da shi, da yabonsa, komai zai so sai dai kafiri, saboda shi kafiri baya son Allah mai girma da buwaya, to ta yaya zai so masoya Allah? Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Idan Allah ya so bawa, sai ya kira Jibrilu, ya ce masa, ni ina son wane ka so shi, sai Jibrilu ya so shi, sannan sai ya yi kira a sama, ya ce, Allah yana son wane, ku so shi, sai waxanda suke sama su so shi, ya ce, sai a sanya masa karvuwa a bayan qasa” (Muslim ne ya rawaito shi)

To haka lamarin yake idan Allah ya so bawa sai ya kewaye shi da kulawarsa da kiyayewarsa, kuma ya sanya komai ya yi masa xa’a ya kusantar masa da nesa, ya sauqaqa masa al’amarin duniya, ba zai ji wata gajiya ba ko wahala ba. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Haqiqa waxanda suka yi imani suka yi aiki na qwarai Allah mai rahama zai sanya musu so da qauna” (Maryam : 96)

Duk wanda Allah ya so shi, sai ya sanya shi tare da shi. Idan Allah ya so bawa sai ya zama tare da shi, yana kiyaye shi yana kula da shi, ba zai ba wani dama a kanshi ba ya cuce shi. A cikin hadisi qudusi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah ya ce, wanda ya yi gaba da waliyyina to na yi masa shelar yaqi, bawana ba zai kusance ni ba da wani abu da nafi so, fiye da abin da na wajabta masa, bawana ba zai gushe ba yana kusantata da nafilfili har sai na so shi, idan na so shi, sai in zama jinsa da yake ji da shi, in zama ganinsa da yake gani da shi, in zama hannunsa da yake damqa da shi, in zama qafarsa da yake tafiya da ita, kuma lallai idan ya roqe ni tabbas zan ba shi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina tabbas wallahi zan tsare shi. Babu wani abu da zan aikata, na yi kaikawo a kansa kamar karvar ran mumini, yana qin mutuwa ni kuma ina qin sava masa” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Imani na gaskiya rayuwa ce ga zukata, kuma fage ne na farin ciki, kamar yadda kaficewa Allah yake mutuwa ga zukata tun gabanin mutuwa, kuma fage na baqin ciki.

Wanda Allah ya so shi sai ya amsa masa addu’arsa : Daga cikin alamar son Allah ga bayinsa muminai shi ne ya amsa musu addu’o’insu, ya yi musu ni’ima da sun xaga hannayensu sama, sun ce “Ya Ubangijin”. Allah ya ce, “Idan bayina suka tambayeka dangane da ni, to ni ina kusa, ni amsa kiran mai kira idan ya kirani, su amsa mini su yi imani da ni, ko sa samu shiriya” (Albaqra : 186).

An karvo daga Salmanul Farisi ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah mai kunya ne da karamci, yana cin kunyar bawansa idan ya xaga hannunsa sama ya dawo da su ba komai” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Idan Allah ya so bawa, sai sanya Mala&"iku su riqa nema masa gafara. Mala&"iku suna newawa wanda Allah yake so gafara, suna nema masa rahama daga wajen Allah, Allah ya ce, “Waxanda suke xauke da Al’arshi da waxanda suke gefensa suna yin tasbihi ga Ubangijinsu, suna yin imani da shi, suna nema wa waxanda suka yi imani gafara, (suna cewa) Ya Ubangijinmu ka yalwaci komai da rahama da ilimi, ka gafarta wa waxanda suka tuba, suka bi hanyarka, ka tseratar da su daga azabar Jaheem” (Gafir : 7)

Allah yana cewa “Sama ta kusa ta tsage a samansu. Mala’iku suna godewa Ubangijinsu suna neman gafararsa ga waxanda suke bayan qasa. Ku saurara! Haqiqa Allah shi mai yawan gafara ne mai jinqai”. (Asshura : 5)

Idan Allah ya so bawa, sai ya xauki ransa yana kan aiki na qwarai. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Idan Allah ya nufi bawa da alheri, sai ya buxa masa. Aka ce, meye ma’anar ya buxa masa? Sai ya ce, “ya buxe masa aikin qwarai gabanin mutuwarsa, sannan sai ya xauke shi a kansa”. (Ahmad ne ya rawaito shi)

-Idan Allah ya so bawa sai ya amintar da shi yayin mutuwa.

Idan Allah ya so bawa sai ya amintar da shi a duniya, ya azurta shi mutuwa cikin aminci da sabati, ya aiko masa Mala’ikunsa su karvi ransa cikin sauqi, su tabbatar da shi akan gaskiya yayin mutuwa, su yi masa bushara da Aljannah. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Waxanda suka ce Ubangijinmu Allah sannan suka daidaita, Mala’iku suna sauka a gare su, (Suna ce musu) kada ku ji tsoro, ku yi bushara da Aljannah wadda aka kasance ana muku alqawari” (Fussilat : 30).

-Idan Allah ya so bawa sai ya dauwamar da shi a cikin Aljannah

Wanda duk Allah ya so shi, to yana cikin Aljannah a lahira, girmamawar Allah da karamcinsa ga bawa a lahiri wani abu ne wanda tunani bai iya tunaninsa, Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa masoyansa alqawarinsa da Aljannah, wadda a cikinta akwai abin da zuciya take so, kamar yadda ya zo a cikin hadisi qudusi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce,.. “Allah ya ce, na tanadarwa bayina salihai abin da idanu ba su tava gani ba, kunnuwa ba su tava ji ba, kuma bai taba xarsuwa ba a zuciyar wani mutum. Ku kuranta wannan ayar in kun ga dama, “Wata rai ba ta san abin da aka voye musu ba na farin ciki” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Duniya ba ta tava daxi ba, sai da son Allah da yi masa xa’a, haka nan Aljannah bata tava daxi ba sai da ganin Allah Maxaukakin Sarki

Daga cikin fa’idar son Allah ga bawa, ganin da bawa zai yi wa Allah Maxaukakin Sarki.

Ubangiji mai girma da buwaya yana bayyana da haskensa ga bayinsa waxanda yake son su, ba za su ga wani abin da suke so fiye da shi ba, har abada, saboda abin da aka rawaito cewa Manzon Allah (S.A.W) ya kalli wata a lokacin da ya cika, ya ce, ..“Haqiqa za ku ga Ubangijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba za ku yi turarreniya ba wajen ganinsa. , Idan kun sami dama kada a rinjaye ku akan barin sallah kafin vullowar rana da gabanin faxuwarta to ku yi, ku karanta faxin Allah : “Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kafin vullowar rana da gabanin faxuwarta”(Sahihul Bukhari)

Wasu Hukunce-Hukunce Da Faxakarwa Akan So

1-Son Allah ga bawa ba ya hana faruwar bala’i gare shi, Manzon AllAh (S.A.W) ya ce, “Girman lada yana tare da girman bala’i, kuma idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, duk wanda ya yarda yana da yarda, wanda ya yi fushi, shi ma fushi ya hau kansa”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Sai Allah ya jarrabi bayi da nau’ikan bala’i, har sai ya tsarkake su daga zunubi, ya raba zukatansu daga shagala da duniya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Za mu jarrabeku har sai mun san mujahidai a cikinku da masu haquri, kuma mu jarrabi labarurrukanku” (Muhammad : 31)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Tabbas za mu jarrabeku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar rayuka da dukiya da ‘ya’yan itace. Ka yi wa masu haquri bushara. Waxanda idan musifa ta same su, sai su ce, mu daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma. Waxannan suna da tsira da rahama daga Ubangijinsu. Waxannan sune shiryaryu” (Albaqra : 155 – 157)

2-Savawa bawa ga Allah yana rage son Allah, ya kawar da kamalarta, saboda soyayya ma kamar imani ce, tana da tushe da kamala, gwargwadon savo gwargwadon yadda zata ragu. Idan mutum ya shiga cikin shakka da babban munafunci, sai asalinta ya tafi, ya zama babu, wanda kuma a zuciyarsa babu son Allah to kafiri ne ya yi ridda, ya zama babban munafiki, bai da rabo a cikin addini. Amma masu savo ba zai yi wu a ce ba sa son Allah ba, sai dai a ce son su ga Allah ragagge ne, don haka akan haka za a yi musu mu’amala. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Da ba ku yin zunubi da Allah ya halicci wasu mutane suna yin zunubi yana gafarta musu” (Ahmad ne ya rawaito shi)

“Yanci shi ne ‘yantuwar zuciya daga shirka da sha’awa da shubuhohi. Bauta kuma ita ce bautar zuciya, ta zama ba ga wanin Allah ba.

3-Son Allah ba ya kore so na xabi’a, wanda zuciya take karkata zuwa gare shi, kamar son abinci da abin sha da ruwa, da sauransu. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An sanya min son mata da turare a duniya” (Ahmad ne ya rawaito shi)

Don haka akwai wasu abubuwa a duniya da son su ba ya cikin shirka, saboda Manzon Allah ya so su, don haka ya halatta mutum ya so wani abu na duniya matuqar dai ba abin da aka haramta ba ne.

4-Wanda duk ya so wani kamar yadda yake son Allah, to shi mushiriki ne. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa, “Daga cikin mutane akwai waxanda suke riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah suna son su kamar yadda suke son Allah, waxanda suka yi imani sun fi tsananin son Allah. Da waxanda suka yi zalunci za su ga, - yayin da za su ga azaba - cewa dukkan qarfi na Allah ne gabaxaya, kuma Allah mai tsananin azaba ne”. (Albaqra : 165)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi soyuwar aiki a wurin Allah mai girma da buwaya shi ne so don Allah da qi don Allah”.

A cikin wannan ayar akwai narkon azaba mai tsanani ga wanda ya daidaita soyaryar wani da ta Allah a wajen ibada da girmamawa.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “ka ce in iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara, da kasuwancin da kuke jin tsoron lalacewarsa, da wuraren zama da kuke so, sun fi soyuwa a wajenku fiye da Allah da Manzonsa da Jihadi akan tafarkinsa to ku jira, har Allah ya zo da lamarinsa” (Attaubah : 24)

A cikin wannan ayar akwai narko mai tsanani ga mutumin waxannan abubuwa guda takwas suka fi soyuwa a wajensa fiye da Allah. An karvo daga Anas, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Xayanku ba zai yi imani ba, har sai na kasance mafi soyuwa a wajensa fiye da ‘ya’yansa da iyayensa da dukkan mutane gabaxaya” (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

5-Jivinta da son mushirikai koma bayan muminai ya ci karo da son Allah, saboda shirkar mushiriki a addininsa. Son don Allah da qi don Allah tushe babba a musu lunci. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kada muminai su riqi kafirai ababen jivinta ba muminai ba, duk wanda ya yi haka, sai dai in don ku kare kanku daga gare su ne” (Al-Imran : 28)

Allah ya hana muminai su jivinci kafirai, ya qarfafa hanin da cewa, duk wanda ya yi haka, to ba shi ba soyayyar Allah a cikin komai, son masoyi da son maqiyinsa sun savawa juna ba sa haxuwa. “Sai dai ku kare kanku daga garesu” (Al-Imran : 28)

Allah ya yi rangwame wajen son su idan musulmi sun ji tsoronsu,kuma ba za su iya zama da su ba, sai da hakan, a wannan lokaci ya hallata su cakuxu da su a zahiri, amma zuciyarsu ta zama cike da Imani da qyamar kafirai. Kamar yadda Allah mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa tana cike da Imani” (Annahli : 106)

Walqiyar So

Alamar son Allah yawan ambatonsa, da shauqin gamuwa da shi, duk wanda yake son abu zai ya yawaita ambatonsa, ya so gamuwa da shi.

Arrabi›u xan Anas

Yayin da aka ba Annabinmu (S.A.W) zavi tsakanin rayuwar duniya ko gamuwa da Allah mai girma da buwaya, sai ya ce, “A’a zuwa ga abokantaka mafi xaukaka” (Ahmad ne ya rawaito shi)

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya zavi son Allah mai girma da buwaya, da son haxuwa da shi, ya fifita hakan, ya gabatar da shi akan son duniya da sha’awarta da kayan jin daxinta.

Kyakkyawan Fata

Abin Da Ake Nufi Da Shi :

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku sauqaqa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku kori mutane” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Fata shi ne : Jin samuwar Allah da falalarsa da rahamarsa, da samun hutu da kwanciyar hankali yayin da aka tsinkayi karamcinsa da kyautarsa, da yarda da hakan. Fata wani abu ne da yake kora zuciya zuwa ga Allah da neman Aljannarsa. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Duk wanda ya aikata mummunan aiki ko ya yi zalunci kansa, sannan yana nemi gafarar Allah, to zai samu Allah mai yawan gafara mai yawan jinqai” (Annisa’i : 110)

Nau’ikansa :

Fata kala uku ne, guda biyu ababen so ne, guda xaya kuwa ba a son shi.

1-Fata wanda ya yi aiki da xa’ar Allah a bisa hasken Allah yana mai neman lada a wurin Allah.

2-Fatan da wanda ya yi zunubi sannan ya tuba yake yi, yana fatan gafara Allah da shafe zunubbain da yafe masa su da suturta shi.

3-Fata na wanda ya ci gaba da sakaci da savo da munanan ayyuka yake yi, na fatan rahamar Ubangijinsa da gafara amma fa ba tare da ya yi wani aiki ba!!! To wannan fatan ba komai ba ne face ruxi da fatan qarya, ba fatan gaskiya ba, kuma wannan fata ba a son shi har abada, saboda fatan muminai shi ne wanda ya haxe da aiki. Allah ya ce, .. “ Haqiqa waxanda suka yi imani da waxanda suka yi hijira a kan tafarkin Allah, waxannan suna fatan samun rahamar Allah. Allah mai yawan gafara ne mai yawan jin qai” (Albaqra : 218)

Matakansa :

Fata yana da matakai da darajoji, suna bambanta daga wani mutum zuwa wani

1-Fatan da yake sanya dagewa wajen yin ibada, ya haifarwa mai yinsa jin daxi yayin da yake ibada, koda kuwa ibadar mai wahala ce, sai riqa jin daxin ne saboda abin da ya nisanta na zunubai da ababen qi.

2-Fatan masu qoqari sosai, wajen barin abin rayukansu da al’adunsu suka saba da su, da barin abin da zai kawar da su daga abin da Ubangijinsu yake nema, wanda zai kaxaita zukatansu ga Allah kaxai.

Wanda duk yake fatan wani abu zai name shi.

3-Fatan Ma’abota tsarkakan zukata, shi ne fatan gamuwa da Allah, wanda yake sa su shauqin zuciya da ratayarta ga Allah kaxai. Wannan fatan shi ya fi dukkan sauran nau’o’in fata. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Duk wanda ya kasance yana fatan gamuwa da Uabangijinsa to ya yi aiki na qwarai, kada kuma ya shirka wajen bautawa Ubangijinsa da wani” (Alkahfi : 110)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wanda yake fatan gamuwa da Allah to ajalin da Allah ya sanya mai zuwa ne, kuma shi (Allah) mai ji ne kuma masani” (Al-ankabut : 5)

Alaqar Fata Da Sanin Sunayen Allah Da Siffofinsa

Mai fata wani mutum ne da yake dauwama akan ayyukan xa’a ga Allah, yana mai tsayuwa da abubuwan da imani ya nuna, yana fata a wurin Allah mai girma da buwaya kada ya karkatar da shi, ya karvi aikinsa kada ya dawo masa da shi, ya ninka masa ladansa, don haka yana qoqarin bin sabubban da suke kawo rahama daidai iyawarsa, yana fatan rahamar Ubangjijinsa, saboda saninsa ga sunayen Allah da siffofinsa, ya riga ya san yana mu’amala ne da Allah mai rahama, mai son bayinsa, mai godiya, mai karamci, mai yawan bayarwa, mai yawan gafara, mai tausayi, don haka a nan duniya yana tsoro, yana kuma fatan aminci idan ya koma zuwa ga Ubangijinsa.

Fa’idojin Fata :

1-Yana qarawa mai yin shi qoqarin dagewa wajen yin ayyuka da xa’a ga Allah.

2-Yana sa mai yin sa ya saba da dauwama akan ayyukan xa’a, a kowane irin halin da ya shiga.

Mai fata koyaushe zai kasance mai kwaxayi a wajen Allah, mai tsoro, mai san falalar Ubangijinsa, mai kyautata zato ga ubangijinsa.

3-Yana sa mai yin sa ya saba da dauwama wajen fuskantar Allah, da ganawa da shi, da tausasawa wajen roqonsa tare da naci.

4-Yana fito da bautar bawa ga Ubangijinsa da buqatuwarsa gareshi a fili, tare da jin cewa shi ba zai tava wadatuwa ga barin falalar Allah ba, da kyautatawarsa a kowanne lokaci.

5-Sani da sakankancewa da samuwar Allah da karamcinsa, Allah tsarki ya tabbata a gare shi, shi ne mai yalwar mai bayarwa, don haka yana so bayinsa su yi fata a wajensa, su kuma nace.

Mumini ya kyautata wa Ubangijinsa zato sai ya yi kyakkyawan aiki. Fajiri kuwa ya munanawa Ubangijinsa zato sai ya munana aiki.

6-Fata nagari yana kai bawa zuwa ga soyayyar Allah Maxaukakin Sarki da isa zuwa ga qololuwar soyayya, duk lokacin da fatan bawa ga Allah ya qaru, ya kuma samu abin da yake fatan, sai ya qara son Ubangijinsa, ya qara gode masa da yarda da shi, wannan kuwa yana cikin rukunan da bautawa Allah take kawo wa.

7-Yana kai bawa zuwa ga maqamin godiya, domin zai zaburar da shi ganin ya isa zuwa maqamin godiya akan ni’imomi, wannan kuwa ita ce tsantsar bauta ga Allah.

8-Sanin Sunayen Allah da sifofinsa, Shi Allah shi ne mai jinqai, mai karamci, mai yawan bayarwa, mai amsawa wanda ya kira shi, kyakkyawa, mawadaci tsarki ya tabbata a gare shi, babu wanda ya kai girman Allah.

Yana cikin kyautata zato ga Allah ka sani cewa Allah ba ya tozarta wanda ya koma zuwa gare shi.

9-Sababi ne na bawa ya samu abin da yake fata, saboda samun abin da ake nema yana taimakawa akan jajircewa da neman qari da fuskantar Allah, hakanan bawa ba zai gushe ba imaninsa yana qaruwa yana qara kusantar Allah mai Rahama.

10-Farin cikin muminai ranar alqiyama da samun abin da suke fata, na yardar Allah da Aljannah, da ganin Allah, duka gwargwadon yadda suke bayi suke fata, da gwargwadon tsoronsu ga Allah a duniya.

Hukunce-Hukuncen Fata Da Faxakarwa

Da za a zo da ma’auni a auna tsoron mumini da fatansa da sun kasance daidai wa daidai.

1-Tsoron Allah yana lazimta fata gare shi, kamar yadda fata gare shi yana lazimta tsoronsa a wajen mumini, don haka ma yana da kyau samun fata a wurin da yake kyau a samu tsoro.. “Me ya sameku ba ku fatan nutsuwa ga Allah” (Nuhu : 13)

Kuma Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ka cewa waxanda suka yi imani su yi gafara ga waxanda ba sa tsoron azabar Ubangiji” (Aljasiya : 14)

Ma’ana basa tsoron abubuwan da Allah zai afko musu kamar yadda suka afkawa waxanda suke gabaninsu na halakarwa da rushewa.

Ba zan so ba a ce babana ne zai min hisabi, domin Ubangijina ya fi min alheri fiye da babana.

Imam Sufyan Assauri

2-Fata nagari wani magani ne da muke buqatarsa a duk lokacin da

- xebe qauna ya mamaye zukata, suka bar ibada

- tsoro ya rinjayi mutum, har yana cutar da kansa da iyalansa, tsoronsa ya qetare inda shari’a ta ce, to irin wannan yanayi ba makawa sai bawa ya samu abin da zai daidaita tsoronsa, wanda shi ne fata nagari..

Ibada ba ta cika sai da tsoro da fata nagari, da tsoro ake barin abubuwan da aka hana, da kuma fata ne ake yawaita biyayya.

Iman Ibnu Kasir

3-Fata kishiyar xebe qauna ne, xebe qauna shi ne tunanin rasa rahamar Allah, da barin nemanta, wanda wannan sababin halaka ne da kafirci. Allah ya ce, “kada ku xebe qauna daga rahamar Allah, babu wanda yake xebe qauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai”. (Yusuf : 87)

Tsoro

Ma’anarsa :

“Allah yana tsoratar da ku kansa” (Al-imran : 30)

Tsoron Allah yana daga cikin ibadu masu girma da ake yi da zuciya. Allah ya ce, “Wancan Shaixan ne yake tsoratar da ku masoyansa, kada ku ji tsoronsu, ku ji tsorona in kun kasance muminai” (Al-imran : 175)

A cikin wannan aya akwai abin da yake nuna wajabcin tsoron Allah shi kaxai, da qarfafa cewa hakan yana cikin lawazim na imani, gwargwadon imanin bawa gwargwadon tsoronsa ga Allah.

An karvo daga uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Na tambayi Annabi (S.A.W) akan wannan aya : “Waxanda suke bayar da abin da aka ba su zukatansu suna jin tsoro”Su ne waxanda suke shan giya, suke sata? Sai Manzon Allah ya ce, “A’a yake ‘yar Siddiq, su ne waxanda suke azumi suke sallah, suke sadaka, amma suna tsoron kada ko ba a karva daga gare su ba”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Abubuwan Da Suke Kawo Tsoron Allah

1-Girmama Allah, saboda da saninsu ga sunayen Allah da siffofinsa.. “Suna tsoron Ubangijinsu a samansu” (Annahli : 50)

2-Tsoron kada makoma ta kasance abin da ba a so, na azaba mai raxaxi a cikin wuta, tir da wannan makoma.

3-Jin gazawa wajen sauqe wajiban da suke kansa, tare da riskar cewa Allah ya san komai kuma yan gani kuma yana da iko, da rashin ganin qanqantar zunubi fiye da ganin girman wanda aka savawa.

4-Tuntuni game da zancen Allah wanda yake cike da alqawarin azaba da tsoratarwa ga wanda ya savawa Allah, ya bar shari’arsa, da barin hasken da aka aiko shi da shi.

5-Tuntuni game da zancen Allah da Manzonsa, da duba tarihin Annabi (S.A.W)

6-Tunani akan girman Allah mai girma da buwaya, duk wanda ya yi tunani a kan haka, zai ga sifofin Allah mai girma da buwaya da girmansa, kuma duk wanda zuciyarsa ta hararo girman Allah zai san girman tsoratarwarsa, to ba makawa zai ji tsoron Allah. Allah ya ce, (Allah yana tsoratar daku kansa) (Al-Imran : 28)

Allah mai girma da buwaa ya ce, (Ba su girmama Allah ba yadda ya cancanci a girmama shi, qasa gabaxayanta damqarsa ce ranar alqiyama, sammai kuma suna naxe a damansa) (Azzumar : 67)

Tsoron Allah yana lazimta saninsa, sanin Allah yana lazimta tsoronsa, tsoronsa kuma yana lazimta yi masa xa’a

7-Tunanin mutuwa da tsananinta, kuma babu mai guje mata “Ka ce mutuwar da kuke gujewa za ta riske ku”. (Al-jumu’a : 8)

Wannan yana haifar da tsoron Allah, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku yawaita tuna mai katse jin daxi, babu wani wanda zai tunata yana cikin matsatsin rayuwa face sai ta yalwata masa, ko wanda yake cikin yalwa face sai ta quntata masa” (Xabarani ne ya rawaito shi)

8-Tuna abin da yake bayan mutuwa, na qabari da abubuwan ban tsoronsa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Na kasance da na hanaku ziyarar maqabarta to ku ziyarceta yanzu, haqiqa tana sa gudun duniya, kuma tana tinatarwa ga lahira”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

An karvo daga Bara’u ya ce, “Mun kasance tare da Manzon Allah (S.A.W) a wata jana’iza, sai ya zauna a gefen qabarin, ya yi kuka har sai dai ya jiqa qasa, sannan ya ce, “Ya ‘yan uwana saboda irin wannan ku yi tanadi”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, kuma ku ji tsoron wata rana da uba ba ya isarwa da xansa da komai ba, ko wanda aka haifa ba zai iya isarwa wanda ya haife shi da komai ba. Haqiqa alqawarin Allah gaskiya ne, kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kada mai ruxi ya ruxe ku game da Allah” (Luqman : 33)

9-Tunani akan qarshen masu raina qananan zunubai, waxanda mutane suke raina su, Manzon Allah (S.A.W) ya yi mana misalinsu da wasu mutane da suka sauka a wani kwari, sai wannan ya zo da itace xaya, wannan ya zo da ice xaya, har suka tara abin da suka gasa gurasarsu da shi. Anan akwai alaqa tsakanin itacen da aka tara aka hura wuta da zunubai waxanda suke jawo wa masu su qonewa a wuta rana qiyama. “Duk lokacin da fatunsu suka qone” (Annisa’i : 56)

10-Bawa ya sani cewa mutuwa na iya shiga tsakaninsa da tuba, ta hanyar yi masa bazata. A lokacin da ko ya yi nadama, nadamar ba za ta amfane shi komai ba. Allah Ta’ala ya ce : “Har sai mutuwa ta zo wa xayansu sai ya ce, ya ubangiji mayar da ni” (Almuminuna : 99)

Kuma Ya ce, “Ka yi musu gargaxi game da ranar nadama” (Maryam : 39)

11-Tunanin mummunar makoma. Allah ya ce, “Mala’iku suna dukan fuskokinsu da bayansu” (Al’anfal : 50)

12-Ka zauna da mutanen da za su samar maka da tsoron Allah, Allah ya ce, “Ka haqurar da ranka tare da waxanda suke bautawa Ubangijinsu safe da yamma, suna nufin fuskarsa” (Alkahfi : 28)

Tsoron Allah ya ratayu da abubuwa biyu

1-Tsoron azabarsa: Wadda ya yi alqawarinta ga wanda ya yi shirka da shi, da wanda ya sava masa, ya nisanci tsoronsa da xa’arsa.

2-Tsoron Allah tsantsa : Wannan shi ne tsoron da malamai da masana Allah suke da shi. “Allah yana tsoratar da ku kansa” (Al-imran : 28)

Duk lokacin da sanin Allah ya qaru sai tsoronsa ya qaru. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kaxai malamai ne suke tsoron Allah” (Faxir : 28)

Domin a duk lokacin da saninsu da Allah da sunayensa da siffofinsa ya qaru ya cika, sai su qara tsoronsa, sai tasirin hakan ya kwarara akan zuciyarsu, sai ya kwarara akan gavvansu.

Daga cikin Amfanin Tsoron Allah

A-A duniya..

1-Dalili ne da yake kawo kafuwa a bayan qasa da qarin imani da nutsuwa, domin in abin da akai ma alqawari ya samu sai ka qara yarda da aminta. Allah ya ce, “Waxanda suka kafirta suka cewa Manzanninsu za mu fitar da ku daga qasarmu, ko kuma ku dawo addininmu, sai Ubangijinsu ya yi musu wahayi cewa tabbas za mu halakar da Azzalumai. Za mu zaunar daku a bayan qasa bayansu, wannan kuwa ga wanda ya ji tsoron tsayawa gabana ya ji tsoron narkona” (Ibrahim : 13 – 14)

Idan tsoron Allah ya zauna a cikin zuciya, sai ya qona wuraren sha’awa a cikinta, ya kori duniya daga cikinta.

2-Yana kwaxaitarwa akan aiki na qwarai da tsarkake zuciya, da rashin neman wani sakamako a duniya, balle ladan lahira ya ragu. Allah ya ce, “Kaxai muna ciyar daku don Allah ne, ba ma buqatar wani sakamako ko godiya a wurinku. Mu muna tsoron wani yini daga Ubangijinmu mai tsananin murtuke fuska” (Al-insan : 9 – 10)

Ya ce, “A cikin xakunan da Allah ya yi izini a xaukaka su a ambaci sunan shi a cikinsu, ana masa tasbihi a ciki safe da yamma. Wasu mazaje da kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsaida sallah da bayar da zakkah, suna tsoron wata rana da zukata da gannai suke juyawa a cikinta” (Annur : 36)

Ma’’ana : zukata suna raurawa da jujjuyawa, wannan shi ne abin da ya ja su zuwa ga aiki, suna neman tsira, suna gudun halaka, suna jin tsoron a ba su littattafansu a hannayensu na hagu.

B-A Lahira :

1-Bawa zai kasance a qarqashin inuwar Al’arshi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi da lalata, sai ya ce, ni ina tsoron Allah” (Bukhari ne ya rawaito shi).

Duk wanda ya ji tsoron Allah, yin hakan zai jawo masa dukkan alheri

Zahirin hadisi yana nuna ya faxa ne da bakinsa, don matar ta tsawatu daga barin abin da za ta yi, kuma don ya tunatar da kansa, ya kuma doge akan matsayinsa ba tare da ya dawo ba, bayan ya faxi abin da yake kai. “Da mutumin da ya ambaci Allah shi kaxai, idanuwansu suka zubar da hawaye” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Tsoron Allah zai sa a zubar da hawaye, yana hana wuta ta shafi wannan idon ranar alqiyama.

2-Dalili ne na samun gafara, saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce, “Wani mutum a cikin waxanda suke gabaninku Allah ya azurta shi da dukiya, lokacin da ya zo mutuwa, sai ya cewa ‘ya’yansa, “Wanne uba ne ni a gareku? Sai suka ce, “Uba ne na qwarai “ Sai ya ce, To ni ban tava aikata alheri ba, don haka idan na mutu ku qona ni, sannan ku sheqe ni a wata rana mai iska. Sai suka yi masa haka. Sai Allah ya tattara shi, ya ce masa, “Me ya sa ka yi haka? Sai ya ce, “Tsoronka (Ya Allah), Sai ya yi masa rahama” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Allah ya yi masa uzuri saboda jahilci, kuma tsoron Allah ya cece shi. Don ba don haka ba duk wanda ya yi musun tashi bayan mutuwa kafiri ne

3-Yana kai ma’abocinsa zuwa ga Aljannah, saboda Annabi (S.A.W) ya ce, “Wanda yake jin tsoro zai fara tafiyarsa tun farkon dare, wanda ya fara tafiyarsa tun farkon dare to zai isa masauki. Ku saurara, hajar Allah mai tsada ce. Ku saurara, hajar Allah ita ce Aljanna” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

4-Samun aminci ranar alqiyama. Allah Maxaukakin Sarki ya ce a cikin hadisi qudisi : “Na rantse da buwayata, ba zan haxawa bawana tsoro biyu ba, idan ya ji tsorona a duniya, zan amintar da shi ranar alqiyama, idan kuma ya amince da ni a duniya sai in tsoratar da shi a ranar alqiyama” (Baihaqi ne ya rawaito shi)

5-Shiga cikin waxanda Allah ya siffata su daga bayinsa muminai, kamar faxin Allah Maxaukakin Sarki, “Haqiqa musulmai maza da musulmai mata, da muminai maza da muminai mata, da masu qanqan da kai maza, da masu qanqan da kai mata, da masu gaskiya maza, da masu gaskiya mata, da masu haquri maza, da masu haquri mata, da masu tsoron Allah maza, da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza, da masu sadaka mata, da amsu azumi maza, da masu azumi mata, da masu kiyaye farjinsu maza, da masu kiyaye farjinsu mata” (Al’ahzab : 35)

Dukkan waxannan lafazai ne masu girma da ake gaggawar samunsu

Allah ya ce, “Gefunansu suna nisantar makwantansu, suna kiran Ubangijinsu cikin tsoro da kwaxayi, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su. Wata rai ba ta san abin da aka voye musu ba na sanyin ido, sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa”. (Assajdah : 16)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wanda yake tsaye a cikin dare yana sujjada yana miqewa, yana tsoron lahira yana fatan rahamar Ubangijinsa, shin yanzu wanda ya sani da wanda bai sani ba, za su daidaita, kaxai waxanda suke da hankali ne suke wa’azantuwa” (Azzumar : 9)

Ya ce, “Waxanda suke jin tsoron azabar Ubangijinsu. Lallai azabar Ubangijinsu ba a bar amincewa ba ce” (Al-ma’arij : 27 – 28)

Allah ya yabi mafi kusancin bayinsa da shi, su ne Annabawa saboda tsoronsa da suke ji, ya ce, “Haqiqa su, suna gaggawa cikin alheri, suna bauta mana a cikin kwaxayi da tsoro” (Al’anbiya : 90)

Mala’iku ma kansu suna jin tsoron Ubangijinsu, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Suna jin tsoron Ubangijinsu a samansu, suna aikata abin da aka umarce su” (Annahli : 50)

6-Samun yardar Allah Maxaukakin Sarki : “Allah ya yarda da su, suma sun yarda da Allah, wannan ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa ne” (Albayyinah : 8)

Tsoron masana Allah

Haqiqa masana Allah suna kan kyawawan ayyukansu da fatan su ga Allah, sai dai fa suna jin tsoron Allah iyakar jin tsoronsa, misalin haka.

- Kukan Manzon Allah (S.A.W) idan yana sallah, har a riqa jin qara a qirjin shi, kamar sautin tukunya mai tafarfasa. Ahmad da Abu Dawud da Nasa’i ne suka rawaitoshi.

- Abubakar – Allah ya yarda da shi – yana kama harshensa ya ce, “Wannan shi ne wanda ya kaini halaka”.

Kuma Yana cewa, “Kaicona, ina ma na zama bishiyar da ake ci”.

- Umar xan Khaxxab – Allah ya yarda da shi – yana cewa, “Kaicona inama ni ba komai ba ne, kaicona ina ma uwata ba ta haife ni ba”.

Yana cewa : “Da Raqumi zai mutu a gefen tekun Furata saboda yunwa da na ji tsoron Allah ya tambaye ni a kanshi ranar Alqiyama”

Kuma Yana cewa, “Da mai kira zai yi kira a cikin sama, ya ce, Ya ku mutane dukkaninku za ku shiga Aljannah sai mutum xaya, da na ji tsoron kada in kasance ko ni ne shi”.

- Usman xan Affan – Allah ya yarda da shi – yana cewa, “Na yi burin a ce ma na mutu ba a tashe ni ba”.

Alhali shi ne wanda yake yanke dare yana tasbihi da sallah da karatun Alqur’ani

- Uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – tana karanta faxin Allah,.. “Sai Allah ya yi mana baiwa ya tseratar da mu wata azaba mai zafi” (Axxur : 27)

A cikin sallarta, sai ta fashe da kuka, ta yi ta yi ba qauqautawa. “In ka azabtar da su, su bayinka ne, in kuwa ka yi musu gafara, to haqiqa Kai Allah Mabuwayi ne Mai Hikima” (Alma’idah : 118)

Hukunce-Hukuncen Tsoro Da Faxakarwa

1-Tsoro na (Khashyah) ya fi tsoro na (khauf), saboda (khashyah) tsoro ne na wanda ya fi sanin Allah. Allah ya ce, “Kaxai waxanda suke jin tsoron Allah su ne malamai (Waxanda suka san Allah) Haqiqa Allah Mabuwayi ne mai yawan gafara “ (Faxir : 28)

“Kaxai waxanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne malamai. Lallai Allah mabuwayi ne mai yawan gafara” (Alfaxir : 28)

Tsoro ne na wanda suka san shi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wallahi ni na fiku kiyaye dokokin Allah da tsoronsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

Gwargwadon yadda aka san Allah da sunayensa da siffofinsa da kamalarsa da girmansa, gwargwadon yadda za a samu tsoronsa.

2-Tsoro yana da amfani idan ya qarawa mai shi qoqarin aiki da tuba, da nadama da barin savo, tsoro yana samuwa daga sanin munin laifi, da gaskata da alqawarin da aka yi na azaba, saboda sanin Allah mai girma da xaukaka, kuma ba zai yiwu ba, a samu tsoron Allah da ba ya sa qoqari da tuba.

Duk wanda ya ji tsoron Allah ba wanda zai cutar da shi, wanda kuwa ya ji tsoron wani ba wanda zai amfanar da shi.

Fudail xan Iyadh

3-Tsoron Allah wajibi ne daga cikin wajibai, kuma yana daga cikin abin da imani yake kawowa, kuma shi ne mafi xaukakar matsayi da amfani ga zuciya, sannan wajibi ne a kan dukkan kowane mutum, kuma yana hana savo da son duniya da abokan banza, da gafala da rashin tunani.