Allah Mai hikima ne

Allah Mai hikima ne

Allah Mai hikima ne

Lallai shi ne Allah mai hikima.. “Ashe ba Allah ba ne mafi iya hukuncin masu hukunci” (Attiin : 8)

“Mai Hikima”

Wanda ya kyautata komai, yake sanya komai a wurin da ya dace da shi, da qaddarawarsa mai girma da xaukaka.

“Mai hikima”.. shi ne wanda yake da hikima maxaukakiya a cikin halittarsa da al’amuransa, ba ya halittar abu don wasa, baya shar’anta komai haka kawai ba hikima, shi ne wanda yake da hukunci a duniya da lahira.

“Mai hikima”

Ya shar’anta shari’o’i saboda hikimarsa, ya sunnanta sunnoni saboda hikimarsa, Shari’arsa ta kai matuqa wajen hikima, a cikin manufofinta da sirrikanta da sakamakonta duniya da lahira

“Mai hikima”

Mai hikima ne cikin abin da ya qaddara ya hukunta, mai hikima cikin abin da ya zartar ya hukunta, mai hikima ne akan talaka da talaucinsa, ko maras lafiya da rauninsa, ko wanda ake bi bashi da damuwarsa da rashinsa, babu matsala a cikin abin ya shirya, babu tawaya a cikin maganganunsa, ko ayyukansa. Tsarki ya tabbata gare shi ma’abocin hikima ta qarshe.

“Mai hikima”

Wanda ya kimsawa bayinsa hikima da sani da nutsuwa da bi a hankali, ya sanya al’amura a wurin da ya dace da su.

Allah ne mafi hikimar masu hikima, babu wani abu da zai faru a duniyarsa sai da izininsa, shi ne yake halattawa yake haramtawa, abin da ya shar’anta shi ne hukunci, addini shi ne abin da ya yi umarni da shi da abin da ya hana, babu mai cin gyarar hukuncinsa, babu mai mayar da hukuncinsa da qaddararsa.

“Mai hikima”

Ba ya zaluntar kowa, mai adalci ne cikin umarninsa da haninsa, da labarinsa.

Lallai Allah mai hukunci ne mai hikimaTags: