Allah Mai iko, mai iyawa

Allah Mai iko, mai iyawa

Allah Mai iko, mai iyawa

Haqiqa Allah mai iko ne mai iyawa.

“Allah mai iko ne akan dukkan komai” (Abaqra : 284) , “A wurin zama na gaskiya, wajen gawurtaccen Sarki mai iko” (Alqamar : 55) , “Ka ce shi mai iko ne” (Al-an’am : 65)

“Mai iko”.. Cikakken iko, da ikonsa ya samar da dukkan komai, da ikonsa ne yake jujjuya su, da ikonsa ne ya daidiata su, ya kyautata su, da ikonsa ne yake rayawa, yake kashewa, yake tayar da bayi, don yi musu sakamako, yake sakawa mai kyautatawa da kyautatawarsa, mai munanawa da munanawarsa. Idan ya yi nufin abu sai ya ce masa “Kasance, sai ya kasance. Da ikonsa ne yake jujjuya zukata, yaka sarrafa su a kan abin da ya so kuma yake nufi.

“Mai Iko”

Ma’abocin tsananin qarfi, mai iko a kan abin ya ga dama da abin da ya so.

“Mai iko”

Mai cikakken iko, ya raya ya kashe, ya samar da halittu, ya tsara su, ya kyautata su.

“Mai Iko”

Yana tayarwa ya yi sakamako, ya juya zuciya yadda ya so.

“Mai iko”

Mai cikakken iko, babu gajiyawa ko tawaya a tare da shi, a kowane hali da yanayi

‘Mai iko”

Wanda yake tsara wa halintarsa abin da yake so, da abin da yake so, Yin haka yana daga cikin kamalar ikonsa da cikar iliminsa.

Shi ne Allah mai iko



Tags: