Imani da Manzannin Allah Waxanda suke sanar da mutane Allah.

Imani da Manzannin Allah Waxanda suke sanar da mutane Allah.

Imani da Manzannin Allah Waxanda suke sanar da mutane Allah.

Allah bai halicci bayinsa haka sakakai ba, bai kuma barsu aka kara-zube ba, don haka ya aiko musu da Manzanni waxanda suke sanar da su Shi Allah, da girmansa da kamalarsa, suke sanar da su shari’arsa. Allah ya aiko mafifitan mutane, ya aiko manzanni masu yawa daga cikin mutane, Nuhu, Ibrahim, Musa, Isa, (A.S) ya cike aikensa da mafificin manzanni, Muhammad (S.A.W). Ya sanya musu ayoyin da suke nuna gaskiyarsu, suka sauke amana, suka isar da saqo, suka sanar da bayin Ubangijinsu, mahaliccinsu, don haka duk wanda bai yi imani da saqonsu ba, bai gaskata su ba, to bai yi imani da Allah ba. Allah ya ce, “Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, haka ma muminai, dukkaninsu sun yi imani da Allah da Mala’ikunsa da littattafansa da Manzanninsa” (Baqara : 285)

Domin su ne masu isar da saqon Allah, waxanda ya aiko, mu yi imani da su gabaxaya, Allah ya ce, “Ba za mu bambanta wani daga cikinsu ba” (Baqara : 285)

Allah ya aiko manzanni tare da littattafai saboda su zama haske ga mutane, ya aiko Ibrahim da takardu (Suhuf) Dawud da Zabura, Musa da Attaura, Isa da Injila, Muhammad (S.A.W) da littafi, gagara koyo Alqur’ani mai daraja. Allah ya ce, “Wani littaffi ne da an kyautata ayoyinsa sannan aka rarrabe su daga wajen mai Hikima Masani” (Hud : 1)

Allah ya sanya shi (Alqur’ani) shiriya da haske da albarka da hujja, Allah ya ce, “Wannan littafi ne mun saukar da shi mai albarka ku bi shi, ku ji tsoron Allah, ko kwa samu rahama” (Al-an’am : 155)

Ya kuma cewa, “Ya ku mutane haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku, ya kuma saukar muku da haske mabayyani” (Annisa’i :174)

Allah ya sanya imani da cikamakin Annabawa da Manzanni, fiyayyen halitta, Muhammad (S.A.W) da saqonsa wani yanki ne na imani da kaxaituwar Allah Ta’ala, a cikin kalmar shahada, wadda ita ce, “Na shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma na shaida Muhammad Manzon Allah”. Allah ya aiko shi don rahama ga talikai, ya fitar da su daga duhu zuwa haske, daga jahilci zuwa ilimi, daga vata zuwa shiriya da imani, ya sauke amana, ya yi al’umma nasiha, ya kasance mai kwaxayin alheri ga al’ummarsa.

Allah ya ce, “Haqiqa wani Manzo ya zo muku daga cikinku, duk abin da zai wahalar da ku yana yi masa nauyi, mai kwaxayin (alheri) gareku, dangane da muminai mai tausayi ne mai jinqai” (Attaubah : 128)

Allah Maxaukakin Sarki ya baiwa Annabinsa Manzonsa haqqoqin da suka cancanta da shi, shi ne mafi alherin mutane, kuma shugabansu, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ni ne shugaban yayan Adam, amma (na faxi haka ne) ba don alfahari ba” (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

Daga cikin haqqoqinsa (S.A.W)

1-Imani da cewa shi bawan Allah ne Manzonsa, kuma Allah Maxaukakin Sarki ya aiko shi don jin qai ga talikai, ya sauke amana, ya isar da saqo, Allah ya ce, “Ku yi imani da Allah da Manzonsa da hasken da muka saukar” (Attagabun : 8)

Manzon Allah (S.A.W) “Na rantse da wanda ran Muhammad yake hannunsa, babu wani wanda zai ji labarina daga cikin wannan al’umma, bayahude ne ko banasare, sannan ya mutu bai yi imani da abin da aka aiko ni da shi ba, face sai ya kasance daga ma’abota wuta” “Muslim ne ya rawaito shi”

2-Gaskata da karvar abin da ya zo da shi daga Ubangijinsa Maxaukakin Sarki, da kuma sakankancewa saqon na shi gaskiya ne daga wajen Allah, babu shakka ko kokwanto. Allah ya ce, “Muminai su ne kaxai waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi shakka ba” (Alhujurat : 15).

Kuma Allah ya ce, “ Na rantse da Ubangijinka ba za su yi imani ba, har sun kai maka hukunci akan abin da ya faru tsakaninsu, sannan kuma ba za su ji qunci ko damuwa ba dangane da abin da ka hunkunta, su kuma sallama, sallamawa ta gabaxaya” (Annisa’i : 65)

3-Son shi (S.A.W) Allah ya ce, “Ka ce idan iyayenku da yayanku da yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyinku waxanda kuka tara, da kasuwancinku wanda bakwa so ya lalace, da wuraren zaman da kuka yarda da su, sun fi soyuwa a wurinku fiye da Allah da Manzonsa da jihadi akan tafarkinsa, to ku jira har Allah ya zo da lamarinsa, Allah ba ya shiryar da mutane fasiqai” (Attaubah : 24)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Xayanku ba zai yi imani ba har sai na zama mafi soyuwa a wajensa, fiye da babansa da xansa da dukkan mutane gaba xaya” (Bukhari ne ya rawaito shi)

4-Girmamashi da darajta shi. Allah ya ce, “Don ku yi imani da Allah da Manzonsa, ku qarfafe shi, ku girmamshi” (Alfathu : 9)

Ya kuma cewa, “Waxanda suke yi imani da shi, suka qarfafe shi, suka taimake shi, suka bi hasken da aka saukar gare shi, waxannan su ne masu rabauta” (Al-araf : 157)

5-So da qauna da girmama iyalan gidansa, waxanda suke musulunta, suka tafi akan sunnarsa, waxannan su ne wasiyyar da Annabinmu Muhammad (S.A.W) ya yi mana, inda yake cewa, “Ina tunatar daku Allah akan iyalan gidana, ina tunatar daku Allah a kan iyalan gidana, ina tunatar daku Allah a kan iyalan gidana”. (Muslim ne ya rawaito shi).

Iyalan gidansa su ne mafifitan mutane, kamar matansa, da zuriyarsa, da yan uwansa, waxanda sadaka ta haramta a kansu, ba ya halatta a tauye su, ko a zage su, kamar yadda ba ya halatta a yi da’awar cewa ba sa savo (Ma’asumai) ko kuma a kira su ba Allah ba.

6-Son sahabbansa, waxanda suke yi imani da shi, suka gaskata shi, da kuma barin kutsawa cikinsu da munanan maganganu, Haqiqa Allah ya yabe su,

7-Kada a kutsa cikin tarihin sahabbansa waxanda suka yi imani da shi da munanan mganganu, saboda su ne waxanda Allah Maxaukakin Sarki ya yabe su, ya ce, “Muhammad Manzon Allah ne, waxanda suke tare da shi masu tsanantawa ne ga kafirai, masu jinqai a tsakaninsu, za ka gan su suna yawan ruku’u da sujjada, suna neman falala daga wajen Allah da yarda, alamominsu suna fuskokinsu daga alamar sujjada” (Alfathu : 29)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “kada ku zagi sahabbaina, kada ku zagi sahabbaina, na rantse da wanda raina yake hannunsa, da xayanku zai ciyar da misalin dutsen Uhud na zinariya, da ba zai kai mudun xayansu ko rabin sa ba” (Muslim ne ya rawaito shi)

Mafifitan Sahabbai su ne khalifofi shiryayyu, Abubakar, sai Umar, sai Usman, sai Aliyyu, Allah ya yarda da su, da sauran sahabbai gabaxaya, Allah ya ce, “Waxanda suka riga (Shiga musulunci) daga Sahabban da suka yi hijira (Almuhajirai) da na Madinah (Al’ansar) da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi, ya tanadar musu da Aljanatai waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dauwama a cikinsu har abada, wannan shi ne rabo mai girma” (Attaubah : 100)

Dukkan waxannan sahabbai sun isar mana da saqon Manzon Allah (S.A.W) har ilimi da imani ya zo mana.Tags: