Ma'anar Ubangiji

Ma'anar Ubangiji

Ma’anar Ubangiji

Lafazin Allahu, suna ne mai daxi a wajen ma’ana da faxa, kuma ya samo asali daga Allantaka da so da qauna, da kaxaitawa da tsakake zuciya, me ya fi wannan sunan girma!! “Shi ne Allah Mahalicci mai qirqirar halitta” (Alhashar : 24)

Ubangiji shi ne shugaban da babu kamarsa, wanda yake gyara al’amuran halittarsa da abin da ya zubo musu na ni’imomi. Mai mulkin da yake da halitta da al’amura gabaxaya, ba a amfani da lafazin (Arrabbu) a kan halitta sai dai idan an goya shi da wani suna,kamar a ce, Rabbud Dari, ko Rabbul Mali, wanda ya mallaki gidan ko dukiyar, amma a faxe shi haka kurum ba tare da an goya shi da wani suna ba, to wannan sai ga Allah shi kaxai.

Shi ne Allah Mahalicci wanda ya yi qirqira, mai kamanta halitta yadda ya so, wanda ya halicci dukkan komai, ya samar da su ya daidaita su, ya suranta su da hikimarsa, kuma Allah bai gushe ba da wannan siffofi har abada.

Da yake mutane sun riga sanin buqatarsu ga wanda zai rene su ya kula da su, kafin su san buqatarsu ga abin bauta, haka ma sun fi sanin a biya musu buqatunsu na gaggawa kafin waxanda za a biya musu a nan gaba, don haka sai suka yadda da kaxaituwar Allah da ayyuka, kafin su yarda da cancantarsa da bauta kiransa shi kaxai, da neman taimakonsa da dogara da shi fiye da bauta masa da komawa zuwa ga gare shi.

Allah Ubangiji shi ne mai renon dukkan bayinsa, ta hanyar jujjuya al’amura da ni’imomi kala-kala, musamman ma renon da yake wa bayinsa kevantattu na gyara musu zukata da halaye, don haka suke yawan kiran shi da sunan (Rabbu) don suna neman irin wannan renon kevantacce.

Lafazin (Arrabbu) ya qunshi abubuwa da dama, kamar jujjuwa abubuwa, da azurtawa, da ba da lafiya, da datarwa, Allah yana cewa, “Shi ne wanda yake ciyar da ni yake shayar da ni. Idan na yi rashin lafiya shi ne yake warkar da ni. Wanda kuma yake kashe ni kuma yake rayani” (Ashua’ara : 79 – 81)



Tags: