Ma'arnar kalmar Ilahu

Ma'arnar kalmar Ilahu

Ma’arnar kalmar “Ilahu”

Dialah Allah yang tiada sesembahan haq kecuali Dia (QS. Al Hasyr: 22)

Kalmar “Ilahu”

Tana nufin abin bautawa, abin yiwa xa’a, wanda ya cancanta a bauta masa.. “Ku bautawa Allah kada ku haxa shi da komai a wajen bauta” (Annisa’i : 36)

Ma’anar kalmar Shahada “La’ilaha Illal Lahu”

Ita ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

Ta haxa rukunai guda biyu manya-manya.

Na Farko : Kore bauta ta gaskiya daga wani Allah mai girma da buwaya.

Na Biyu : Tabbatar da bautar gaskiya ga Allah maxaukakin Sarki koma bayan waninsa.. “Shi ne Allah Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi” (Al-hashar : 22)

Kalmar Shahada (La Ilaha Illal Lahu)

Ita ce tsantsar kalmar tauhidi, kuma ita ce mafi girmar farillar da Allah da ya wajabta ta akan bayinsa, matsayinta a addini kamar matsayin kai ne a jiki.Tags: