Tsoro

Tsoro

Tsoro

Ma’anarsa :

“Allah yana tsoratar da ku kansa” (Al-imran : 30)

Tsoron Allah yana daga cikin ibadu masu girma da ake yi da zuciya. Allah ya ce, “Wancan Shaixan ne yake tsoratar da ku masoyansa, kada ku ji tsoronsu, ku ji tsorona in kun kasance muminai” (Al-imran : 175)

A cikin wannan aya akwai abin da yake nuna wajabcin tsoron Allah shi kaxai, da qarfafa cewa hakan yana cikin lawazim na imani, gwargwadon imanin bawa gwargwadon tsoronsa ga Allah.

An karvo daga uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce, Na tambayi Annabi (S.A.W) akan wannan aya : “Waxanda suke bayar da abin da aka ba su zukatansu suna jin tsoro”Su ne waxanda suke shan giya, suke sata? Sai Manzon Allah ya ce, “A’a yake ‘yar Siddiq, su ne waxanda suke azumi suke sallah, suke sadaka, amma suna tsoron kada ko ba a karva daga gare su ba”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Abubuwan Da Suke Kawo Tsoron Allah

1-Girmama Allah, saboda da saninsu ga sunayen Allah da siffofinsa.. “Suna tsoron Ubangijinsu a samansu” (Annahli : 50)

2-Tsoron kada makoma ta kasance abin da ba a so, na azaba mai raxaxi a cikin wuta, tir da wannan makoma.

3-Jin gazawa wajen sauqe wajiban da suke kansa, tare da riskar cewa Allah ya san komai kuma yan gani kuma yana da iko, da rashin ganin qanqantar zunubi fiye da ganin girman wanda aka savawa.

4-Tuntuni game da zancen Allah wanda yake cike da alqawarin azaba da tsoratarwa ga wanda ya savawa Allah, ya bar shari’arsa, da barin hasken da aka aiko shi da shi.

5-Tuntuni game da zancen Allah da Manzonsa, da duba tarihin Annabi (S.A.W)

6-Tunani akan girman Allah mai girma da buwaya, duk wanda ya yi tunani a kan haka, zai ga sifofin Allah mai girma da buwaya da girmansa, kuma duk wanda zuciyarsa ta hararo girman Allah zai san girman tsoratarwarsa, to ba makawa zai ji tsoron Allah. Allah ya ce, (Allah yana tsoratar daku kansa) (Al-Imran : 28)

Allah mai girma da buwaa ya ce, (Ba su girmama Allah ba yadda ya cancanci a girmama shi, qasa gabaxayanta damqarsa ce ranar alqiyama, sammai kuma suna naxe a damansa) (Azzumar : 67)

Tsoron Allah yana lazimta saninsa, sanin Allah yana lazimta tsoronsa, tsoronsa kuma yana lazimta yi masa xa’a

7-Tunanin mutuwa da tsananinta, kuma babu mai guje mata “Ka ce mutuwar da kuke gujewa za ta riske ku”. (Al-jumu’a : 8)

Wannan yana haifar da tsoron Allah, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku yawaita tuna mai katse jin daxi, babu wani wanda zai tunata yana cikin matsatsin rayuwa face sai ta yalwata masa, ko wanda yake cikin yalwa face sai ta quntata masa” (Xabarani ne ya rawaito shi)

8-Tuna abin da yake bayan mutuwa, na qabari da abubuwan ban tsoronsa. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Na kasance da na hanaku ziyarar maqabarta to ku ziyarceta yanzu, haqiqa tana sa gudun duniya, kuma tana tinatarwa ga lahira”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

An karvo daga Bara’u ya ce, “Mun kasance tare da Manzon Allah (S.A.W) a wata jana’iza, sai ya zauna a gefen qabarin, ya yi kuka har sai dai ya jiqa qasa, sannan ya ce, “Ya ‘yan uwana saboda irin wannan ku yi tanadi”. (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, kuma ku ji tsoron wata rana da uba ba ya isarwa da xansa da komai ba, ko wanda aka haifa ba zai iya isarwa wanda ya haife shi da komai ba. Haqiqa alqawarin Allah gaskiya ne, kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kada mai ruxi ya ruxe ku game da Allah” (Luqman : 33)

9-Tunani akan qarshen masu raina qananan zunubai, waxanda mutane suke raina su, Manzon Allah (S.A.W) ya yi mana misalinsu da wasu mutane da suka sauka a wani kwari, sai wannan ya zo da itace xaya, wannan ya zo da ice xaya, har suka tara abin da suka gasa gurasarsu da shi. Anan akwai alaqa tsakanin itacen da aka tara aka hura wuta da zunubai waxanda suke jawo wa masu su qonewa a wuta rana qiyama. “Duk lokacin da fatunsu suka qone” (Annisa’i : 56)

10-Bawa ya sani cewa mutuwa na iya shiga tsakaninsa da tuba, ta hanyar yi masa bazata. A lokacin da ko ya yi nadama, nadamar ba za ta amfane shi komai ba. Allah Ta’ala ya ce : “Har sai mutuwa ta zo wa xayansu sai ya ce, ya ubangiji mayar da ni” (Almuminuna : 99)

Kuma Ya ce, “Ka yi musu gargaxi game da ranar nadama” (Maryam : 39)

11-Tunanin mummunar makoma. Allah ya ce, “Mala’iku suna dukan fuskokinsu da bayansu” (Al’anfal : 50)

12-Ka zauna da mutanen da za su samar maka da tsoron Allah, Allah ya ce, “Ka haqurar da ranka tare da waxanda suke bautawa Ubangijinsu safe da yamma, suna nufin fuskarsa” (Alkahfi : 28)

Tsoron Allah ya ratayu da abubuwa biyu

1-Tsoron azabarsa: Wadda ya yi alqawarinta ga wanda ya yi shirka da shi, da wanda ya sava masa, ya nisanci tsoronsa da xa’arsa.

2-Tsoron Allah tsantsa : Wannan shi ne tsoron da malamai da masana Allah suke da shi. “Allah yana tsoratar da ku kansa” (Al-imran : 28)

Duk lokacin da sanin Allah ya qaru sai tsoronsa ya qaru. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kaxai malamai ne suke tsoron Allah” (Faxir : 28)

Domin a duk lokacin da saninsu da Allah da sunayensa da siffofinsa ya qaru ya cika, sai su qara tsoronsa, sai tasirin hakan ya kwarara akan zuciyarsu, sai ya kwarara akan gavvansu.

Daga cikin Amfanin Tsoron Allah

A-A duniya..

1-Dalili ne da yake kawo kafuwa a bayan qasa da qarin imani da nutsuwa, domin in abin da akai ma alqawari ya samu sai ka qara yarda da aminta. Allah ya ce, “Waxanda suka kafirta suka cewa Manzanninsu za mu fitar da ku daga qasarmu, ko kuma ku dawo addininmu, sai Ubangijinsu ya yi musu wahayi cewa tabbas za mu halakar da Azzalumai. Za mu zaunar daku a bayan qasa bayansu, wannan kuwa ga wanda ya ji tsoron tsayawa gabana ya ji tsoron narkona” (Ibrahim : 13 – 14)

Idan tsoron Allah ya zauna a cikin zuciya, sai ya qona wuraren sha’awa a cikinta, ya kori duniya daga cikinta.

2-Yana kwaxaitarwa akan aiki na qwarai da tsarkake zuciya, da rashin neman wani sakamako a duniya, balle ladan lahira ya ragu. Allah ya ce, “Kaxai muna ciyar daku don Allah ne, ba ma buqatar wani sakamako ko godiya a wurinku. Mu muna tsoron wani yini daga Ubangijinmu mai tsananin murtuke fuska” (Al-insan : 9 – 10)

Ya ce, “A cikin xakunan da Allah ya yi izini a xaukaka su a ambaci sunan shi a cikinsu, ana masa tasbihi a ciki safe da yamma. Wasu mazaje da kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsaida sallah da bayar da zakkah, suna tsoron wata rana da zukata da gannai suke juyawa a cikinta” (Annur : 36)

Ma’’ana : zukata suna raurawa da jujjuyawa, wannan shi ne abin da ya ja su zuwa ga aiki, suna neman tsira, suna gudun halaka, suna jin tsoron a ba su littattafansu a hannayensu na hagu.

B-A Lahira :

1-Bawa zai kasance a qarqashin inuwar Al’arshi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi da lalata, sai ya ce, ni ina tsoron Allah” (Bukhari ne ya rawaito shi).

Duk wanda ya ji tsoron Allah, yin hakan zai jawo masa dukkan alheri

Zahirin hadisi yana nuna ya faxa ne da bakinsa, don matar ta tsawatu daga barin abin da za ta yi, kuma don ya tunatar da kansa, ya kuma doge akan matsayinsa ba tare da ya dawo ba, bayan ya faxi abin da yake kai. “Da mutumin da ya ambaci Allah shi kaxai, idanuwansu suka zubar da hawaye” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Tsoron Allah zai sa a zubar da hawaye, yana hana wuta ta shafi wannan idon ranar alqiyama.

2-Dalili ne na samun gafara, saboda hadisin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce, “Wani mutum a cikin waxanda suke gabaninku Allah ya azurta shi da dukiya, lokacin da ya zo mutuwa, sai ya cewa ‘ya’yansa, “Wanne uba ne ni a gareku? Sai suka ce, “Uba ne na qwarai “ Sai ya ce, To ni ban tava aikata alheri ba, don haka idan na mutu ku qona ni, sannan ku sheqe ni a wata rana mai iska. Sai suka yi masa haka. Sai Allah ya tattara shi, ya ce masa, “Me ya sa ka yi haka? Sai ya ce, “Tsoronka (Ya Allah), Sai ya yi masa rahama” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Allah ya yi masa uzuri saboda jahilci, kuma tsoron Allah ya cece shi. Don ba don haka ba duk wanda ya yi musun tashi bayan mutuwa kafiri ne

3-Yana kai ma’abocinsa zuwa ga Aljannah, saboda Annabi (S.A.W) ya ce, “Wanda yake jin tsoro zai fara tafiyarsa tun farkon dare, wanda ya fara tafiyarsa tun farkon dare to zai isa masauki. Ku saurara, hajar Allah mai tsada ce. Ku saurara, hajar Allah ita ce Aljanna” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

4-Samun aminci ranar alqiyama. Allah Maxaukakin Sarki ya ce a cikin hadisi qudisi : “Na rantse da buwayata, ba zan haxawa bawana tsoro biyu ba, idan ya ji tsorona a duniya, zan amintar da shi ranar alqiyama, idan kuma ya amince da ni a duniya sai in tsoratar da shi a ranar alqiyama” (Baihaqi ne ya rawaito shi)

5-Shiga cikin waxanda Allah ya siffata su daga bayinsa muminai, kamar faxin Allah Maxaukakin Sarki, “Haqiqa musulmai maza da musulmai mata, da muminai maza da muminai mata, da masu qanqan da kai maza, da masu qanqan da kai mata, da masu gaskiya maza, da masu gaskiya mata, da masu haquri maza, da masu haquri mata, da masu tsoron Allah maza, da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza, da masu sadaka mata, da amsu azumi maza, da masu azumi mata, da masu kiyaye farjinsu maza, da masu kiyaye farjinsu mata” (Al’ahzab : 35)

Dukkan waxannan lafazai ne masu girma da ake gaggawar samunsu

Allah ya ce, “Gefunansu suna nisantar makwantansu, suna kiran Ubangijinsu cikin tsoro da kwaxayi, kuma suna ciyarwa daga abin da muka azurta su. Wata rai ba ta san abin da aka voye musu ba na sanyin ido, sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa”. (Assajdah : 16)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wanda yake tsaye a cikin dare yana sujjada yana miqewa, yana tsoron lahira yana fatan rahamar Ubangijinsa, shin yanzu wanda ya sani da wanda bai sani ba, za su daidaita, kaxai waxanda suke da hankali ne suke wa’azantuwa” (Azzumar : 9)

Ya ce, “Waxanda suke jin tsoron azabar Ubangijinsu. Lallai azabar Ubangijinsu ba a bar amincewa ba ce” (Al-ma’arij : 27 – 28)

Allah ya yabi mafi kusancin bayinsa da shi, su ne Annabawa saboda tsoronsa da suke ji, ya ce, “Haqiqa su, suna gaggawa cikin alheri, suna bauta mana a cikin kwaxayi da tsoro” (Al’anbiya : 90)

Mala’iku ma kansu suna jin tsoron Ubangijinsu, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Suna jin tsoron Ubangijinsu a samansu, suna aikata abin da aka umarce su” (Annahli : 50)

6-Samun yardar Allah Maxaukakin Sarki : “Allah ya yarda da su, suma sun yarda da Allah, wannan ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa ne” (Albayyinah : 8)

Tsoron masana Allah

Haqiqa masana Allah suna kan kyawawan ayyukansu da fatan su ga Allah, sai dai fa suna jin tsoron Allah iyakar jin tsoronsa, misalin haka.

- Kukan Manzon Allah (S.A.W) idan yana sallah, har a riqa jin qara a qirjin shi, kamar sautin tukunya mai tafarfasa. Ahmad da Abu Dawud da Nasa’i ne suka rawaitoshi.

- Abubakar – Allah ya yarda da shi – yana kama harshensa ya ce, “Wannan shi ne wanda ya kaini halaka”.

Kuma Yana cewa, “Kaicona, ina ma na zama bishiyar da ake ci”.

- Umar xan Khaxxab – Allah ya yarda da shi – yana cewa, “Kaicona inama ni ba komai ba ne, kaicona ina ma uwata ba ta haife ni ba”.

Yana cewa : “Da Raqumi zai mutu a gefen tekun Furata saboda yunwa da na ji tsoron Allah ya tambaye ni a kanshi ranar Alqiyama”

Kuma Yana cewa, “Da mai kira zai yi kira a cikin sama, ya ce, Ya ku mutane dukkaninku za ku shiga Aljannah sai mutum xaya, da na ji tsoron kada in kasance ko ni ne shi”.

- Usman xan Affan – Allah ya yarda da shi – yana cewa, “Na yi burin a ce ma na mutu ba a tashe ni ba”.

Alhali shi ne wanda yake yanke dare yana tasbihi da sallah da karatun Alqur’ani

- Uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – tana karanta faxin Allah,.. “Sai Allah ya yi mana baiwa ya tseratar da mu wata azaba mai zafi” (Axxur : 27)

A cikin sallarta, sai ta fashe da kuka, ta yi ta yi ba qauqautawa. “In ka azabtar da su, su bayinka ne, in kuwa ka yi musu gafara, to haqiqa Kai Allah Mabuwayi ne Mai Hikima” (Alma’idah : 118)

Hukunce-Hukuncen Tsoro Da Faxakarwa

1-Tsoro na (Khashyah) ya fi tsoro na (khauf), saboda (khashyah) tsoro ne na wanda ya fi sanin Allah. Allah ya ce, “Kaxai waxanda suke jin tsoron Allah su ne malamai (Waxanda suka san Allah) Haqiqa Allah Mabuwayi ne mai yawan gafara “ (Faxir : 28)

“Kaxai waxanda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne malamai. Lallai Allah mabuwayi ne mai yawan gafara” (Alfaxir : 28)

Tsoro ne na wanda suka san shi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wallahi ni na fiku kiyaye dokokin Allah da tsoronsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

Gwargwadon yadda aka san Allah da sunayensa da siffofinsa da kamalarsa da girmansa, gwargwadon yadda za a samu tsoronsa.

2-Tsoro yana da amfani idan ya qarawa mai shi qoqarin aiki da tuba, da nadama da barin savo, tsoro yana samuwa daga sanin munin laifi, da gaskata da alqawarin da aka yi na azaba, saboda sanin Allah mai girma da xaukaka, kuma ba zai yiwu ba, a samu tsoron Allah da ba ya sa qoqari da tuba.

Duk wanda ya ji tsoron Allah ba wanda zai cutar da shi, wanda kuwa ya ji tsoron wani ba wanda zai amfanar da shi.

Fudail xan Iyadh

3-Tsoron Allah wajibi ne daga cikin wajibai, kuma yana daga cikin abin da imani yake kawowa, kuma shi ne mafi xaukakar matsayi da amfani ga zuciya, sannan wajibi ne a kan dukkan kowane mutum, kuma yana hana savo da son duniya da abokan banza, da gafala da rashin tunani.



Tags: