Qa'idoji Da Faxakarwa Game Da Fahimtar Sunayen Allah Da Siffofinsa

Qa'idoji Da Faxakarwa Game Da Fahimtar Sunayen Allah Da Siffofinsa

Qa’idoji Da Faxakarwa Game Da Fahimtar Sunayen Allah Da Siffofinsa

“Babu abin da ya yi kama da shi, shi mai ji ne mai gani”

1-Sunayen Allah gabaxayansu masu matuqar kyau ne, Allah ya ce, “Allah yana da sunaye mafiya kyau” (Al-aaraf : 180)

Allah ya sanar da mu zatinsa mai girma don mu bauta masa, mu girmama shi, mu so shi, mu ji tsoronsa, mu yi qaunar abin da yake wajensa.

2-Tabbatar da sunayen Allah da siffofinsa ta hanyoyi biyu ne, babu ta uku, su ne, littafin Allah mai girma da buwaya, da sunnar Manzonsa (S.A.W). Sunayen Allah da siffofinsa ba sa tabbata da waninsu. Sai mu tabbatar da abin da Allah da manzonsa suka tabbatar. Kuma mu kore abin da Allah da Manzonsa suka kore, mu tabbatar da kamala kishiyarta. Abin da Allah da Manzonsa ba su tabbatar da shi ba, na sunan Allah da siffofinsa, kuma ba su kore shi ba. To mu ma ba za mu tabbatar da shi ba, kuma ba za mu kore shi ba. Amma ma’anar lafazin sai mu yi filla-filla da shi, idan ana nufin gaskiya da shi wadda ta dace da Allah sai a karva, idan kuwa ana nufin wata ma’ana ce da ba ta dace da Allah ba to wajibi ne ya kore wannan ma’nar.

3-Magana akan siffofin Allah, kamar magana ce akan zatin Allah, kamar yadda ba mu san yaya zatin Allah yake ba, hakanan ma bamu san yaya siffofin Allah kyawawa suke ba, sai dai za mu yi imani mu sallama ba tare da shakka ba, ko canzawa ba, ko kamantawa, ko misaltawa ba.

4-Sunayen Allah da siffofinsa suna da ma’anoni na haqiqa ba na aro ko na kintace ba. Dukkaninsu suna nuna zatin Allah ne, da kuma siffofi cikakku waxanda suke tare da shi Allah. Kamar sunansa (Mai iko) (Masani) (Mai Hikima) (Mai ji) (Mai gani), duk waxannan sunaye ne da suke nuna zatin Allah, da kuma abin da yake tare da shi na iko da ilimi da hikima da ji da gani.

5-Tsarkake Allah daga tawaya, tsarkakewa ce ba tare da vata ma’ana ba, da kore dukkan naqasa daga Allah a dunqule, kowace irin naqasa ce, da tabbatar masa da kamala a cikin kowanne abu da ya kevanta da shi. Allah ya ce, “Babu abin da ya yi kama da shi. Shi mai ji ne mai gani” (Ashshura : 11)

6-kamar yadda imani da sunayen Allah suke hukunta yin imani da siffar da sunan ya qunsa, to haka ma imani da sunan Allah yana hukunta imani da abin da yake biyo bayan sunan na tasiri. Misali sunan Allah (Arrahman) wato mai rahama, ya qunshi cewa Allah yana da siffar rahama, kuma yana yi wa bayinsa rahama.

Ga wasu bayanai masu mahimmanci da zasu taimaka wajen fahimtar sunayen Allah da siffofinsa, ga su kamar haka :

1-Sunayen Allah ba su da wani adadi kyadadde. Ya zo a cikin hadisi: “Ina roqonka da duk wani suna da yake naka ne, ka kira kanka da shi, ko ka sanar da wani cikin halittarka shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka kevance kanka da sanin shi a cikin ilimin gaibu a wajenka” (Ahmad ne ya rawaito shi)

2-Daga cikin sunayen Allah akwai waxanda ya kevanta da su shi kaxai, babu wanda ya yi tarayya da shi a cikinsu, kuma ba ya halatta a kira wani da su, kamar : Sunan Allahu, Arrahman. Daga cikinsu kuma akwai waxanda za a iya faxawa waninsa, duk da cewa sun fi cikar ma’ana da cikar siffa a wurin Allah.

3-Ana ciro siffofin Allah daga sunayensa, duk wani suna na Allah to ya qunshi siffa. Amma ba a tsago siffar Allah daga sunansa, kamar mu ce Allah yana fushi, amma baza mu kira shi da suna mai fushi ba. Allah Maxaukakin Sarki ya xaukaka daga barin haka.Tags: