Allah Mai Amsawa

Allah Mai Amsawa

Allah Mai Amsawa

Lallai Allah mai amsawa ne mai girma da buwaya.. “Haqiqa Ubangijina makusanci ne mai amsawa” (Hud : 61)

“Mai amsawa”

Yana amsawa bayinsa idan suka kama qafa gare shi, suka kirawo shi, suka roqe shi. Shi ne wanda ya umarce su da addu’a, kuma ya yi musu alqawarin amsawa.

“Mai amsawa”.. yana amsawa masu roqo duk irin yadda suka kasance, a duk inda suke, a kowanne hali suke ciki.

“Mai amsawa”

Da shi ne fursina ya dogara a cikin kurkunsa, hakanan da shi talaka ya dogara a halin talaucinsa, hakanan maraya a halin maraicinsa, da marar lafiya a lokacin rashin lafiyarsa, da bakararre yayin da ya rasa haihuwa. Kuma duk ya biya musu buqatunsu duka.

“Mai amsawa”

Yana amsawa mai tsananin buqata “Waye yake amsawa wanda yake cikin tsananin buqata idan ya kira shi, kuma ya yaye cuta”. (Annamli : 62)

A lokacin da ya fi kusancin amsa addu’a shi ne lokacin da bawa ya kira shi, ya yi kamun qafa da sunayensa da siffofinsa. Sau tari fursuna ya roqe shi ya fito da shi, wanda ruwan teku ya ci, ya roqe shi ya kuvutar da shi, ya nemi arziqinsa daga talaucin da yake ciki ya azurta shi. Maraya nawa ne ya roqe shi, ya amsa masa ya kula da shi, har ya girma. Mara lafiya nawa ne ya roqe shi lafiya, kuma ya rubuta masa waraka. Nawa wanda ba ya haihuwa ya qasqantar da kai gare shi, ya azurta shi da xa, ya karrama shi.

Lalla Allah mai amsawa ne



Tags: