Allah mai azurtawa

Allah mai azurtawa

Allah mai azurtawa

Shi ne Allah mai azurtawa.. “Haqiqa Allah shi ne mai tsananin karfi” (Azzariyat : 58)

“Mai azurtawa”

Wanda arziqin bayi yake hannunsa, shi ne wanda yake shimfixa arziqi ga wanda ya so daga cikin bayinsa ya qaddara masa abin da ya so, a hannunsa. Makullan sammai da qasa suke a gunsa. Allah maxaukakin Sarki ya ce, “babu wata dabba a bayan qasa face arziqinta yana ga Allah, ya san matabbatarta da ma’ajiyarta” (Hud : 6)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Dabba nawa ce da bata xauke da arziqinta Allah ne yake azurtata da ku gabaxaya. Shi ne mai ji masani” (al’ankabut : 60)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Haqiqa Ubangijinka yana shimfixa arziki ga wanda ya ga dama ya Quntata shi ga wanda ya ga dama. Haqiqa shi dangane da bayinsa masani ne mai gani” (Al-isra’i : 30)

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Allah yana azurta wanda ya ga dama ba tare da lissafi ba” (Albaqra : 212)

“Mai azurtawa”

Dukkan mutane mabuqata ne, gare shi da arzikinsa, yana azurta dukkan mutane, nagarinsu da fajiransu, na farkonsu da na qarshensu.

“Mai azurtawa”

Yana azurta wanda ya fuskance shi da zuciya mai kyau, gyaruwar zukata shi ne mafi girma arziki. Yana kwarara ilimi da imani ga wanda ya roqe shi, yana ba da arziqi na halal ga wanda ya neme shi, wanda yake taimakawa wajen gyara zuciya, da gyaruwar addini, ga wanda ya bukaci hakan daga wajensa.

Lallai Shi ne Allah Mai azurtawaTags: