Allah Mai Mulki, Mamallaki

Allah Mai Mulki, Mamallaki

Allah Mai Mulki, Mamallaki

Lallai shi ne Allah mai mulki.. “Mai mulki tsarkakakke” (Al-hashru : 23)

“Mai Mulki”

“Mamallaki mai mulki” .. wanda mulki nasa ne, ya siffata da siffar mulki, sifa ce ta girma da xaukaka, da rinjaye da jujjuya al’amura, shi ne wanda yake da cikakken tasrifi a cikin halitta da umarni da sakamako, duniyar sama da qasa ta shi ce, dukkansu bayinsa ne, ababan mallakarsa ne, masu buqata ne a gurinsu.

Ma’abocin girma da xaukaka, yana jujjuya al’amuran bayinsa yana tasarrufi a cikinsu, su bayinsa ne, mabuqata a gurinsa, shi kuma mamallakinsu ne mai mulkinsu.

Yana da mulki cikakken mulki, babu wani sarki ko mai mulki ko shugaba face mallakarsa ne, babu wani alheri a sama ko a qasa face kyautarsa ce da falalarsa.. “Dukkan abin da yake sammai da qasa nasa ne” (Albaqra : 255)

Mai Mulki

“Yana bayarwa babu hisabi, yana kyauta mai yawa ga bayinsa, hakan ba ya rage komai daga mulkinsa, kuma babu wani abu da yake shagaltar da shi. Ya zo a cikin hadisi qudusi : “Da a ce na farkonku, da qarshenku, da mutanenku, da aljanunku, za su tsaya a wuri xaya, su roqi wani abu, kuma in baiwa kowa abin da ya roqa, da hakan ba zai tauye komai daga cikin mulkina ba, sai kamar yadda allura za ta rage daga teku idan an shigar da ita cikinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

“Mai Mulki”

Yana ba wanda ya ga dama mulkinsa. Allah ya ce, “Ka ce Allah mamallakin Mulki kana ba da mulki ga wanda ka ga dama, kana cire wanda ka ga dama, kana xaukaka wanda ka ga dama, kana qasqanta wanda ka ga dama, alheri yana hannunka, haqiqa kai mai iko ne akan dukkan komai” (Al-Imran : 26)

“Mamallaki”

Wanda ya mallaki halittarsa, mai tasarrufi a cikinsu duniya da lahira, don haka bayi su yi kwaxayin abin da yake wajensa, su koma wajensa, su qara kwaxayin abin da yake wajensa, da naci da roqo.

Haqiqa Allah mamallaki ne mai mulki”



Tags: