Allah ne mawadaci Mai wadatarwa

Allah ne mawadaci Mai wadatarwa

Allah ne mawadaci Mai wadatarwa

Shi ne Allah mawadaci mai wadatarwa

“Mawadaci”

Wadatar zati, wanda yake da wadata cikakkiya, babu wata tawaya ko aibi a cikin siffofinsa ta kowace irin fuska, kuma koyaushe a wadace yake, saboda wadatarsa tana daga siffofin zatinsa, kamar yadda ya zama mai halitta ba, mai iko, mai kyautatawa. Baya buqatar kowa ta kowace fuska, shi ne mawadacin da taskokin sammai da qasa suke hannunsa, da taskokin duniya da lahira. Kuma mai wadatar da dukkan halittarsa wadata gamammiya.

Mawadaci

Mawadaci ga barin bayinsa, baya buqatar abinci ko abin sha a wurinsu, bai kuma halicce su ba don ya qara yawa da su saboda qaranci, ko kuma ya yi qarfafa da su, ko ya xebe kewa da su, a’a su ne suke da buqatarsa a wajen abincinsu da abin shansu da sauran al’amuransu. Allah Maxaukakin Sarki ya ce,.. “Ban halicci aljanu da mutune ba sai don su bauta min. Ba na buqatar wani arziki daga wajensu, kuma ba na buqatar su ciyar da ni” (Azzariyat : 56 – 57)

Mai wadatarwa

Ya wadatar da mutane daga talaucinsu da buqatunsu, kyautarsa ba ta rage masa komai ba, kuma bayinsa ba sa buqatar wani wanda ba shi ba. Kamar yadda ya zo a cikin hadisi qudusi : “Da a ce na farkonku da na qarshenku da mutananku da aljanunku za su tsaya a wuri xaya, su roqe ni , in baiwa kowa abin da ya roqe ni, da hakan ba zai tauye abin da yake wurina ba, sai dai kamar abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita teku” (Muslim ne ya rawaito shi)

“Mai Wadatarwa”

Ya wadatar da wasu daga cikin bayinsa ta hanyar shiryar da su zuwa ga gyaruwar zuciyarsu, da saninsa da xaukaka shi da girmama shi, da son shi, sai ya wadatar da su da abin da ya fi cika da kaiwa matuqa daga gyaruwar duniyarsu.

Ya wanda kyauta ba ta rage abin da yake wajensa, ka wadatar da mu da halal xinka daga barin abin da ka haramta, haqiqa kai mawadaci ne mai wadatarwa.

Haqiqa shi Allah mawadaci ne mai wadatarwa.



Tags: