Allah Rayayye Tsayayye

Allah Rayayye Tsayayye

Allah Rayayye Tsayayye

Haqiqa shi ne Allah Rayayye Tsayayye “Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, rayayye tsayayye” (Al-imran : 2)

“Rayayye”

Cikakkiyar rayuwa, ba ya buqatar waninsa, amma kowa yana buqatarsa, kuma komai zai halaka Fuskarsa.

“Tsayayye”

Wanda yake tsaye da kansa, mawadaci gabarin waninsa

“Rayayye Tsayayye”.. Mai cikakkiyar rayuwa, wanda yake tsaye da kansa, kuma wanda yake tsaye a kan ma’abota sammai da qassai, wajen jujjuya al’amuransu da halayensu. “Rayayye”.. Wanda ya zatinsa ya tattara dukkan siffofin kamala

“Tsayayye”

Wanda yake tsaye akan kowace rai da abin da ta aikata, mai kiyaye ayyukan ba yi da halayensu da maganganunsu, da kyawawan ayyukansu da munannansu, mai ba su sakamako a kansu.

“Tsayayye”

Wanda yake lissafa abin da bayi suka aikata.

“Tsayayye”

Wanda ya xau nauyin rayuwar dukkan halittarsa, yana azurta su, yana jujjuya al’amuransu, da sha’aninsu.

“Rayayye Tsayayye”

Mawadaci wanda ba zai gushe ba. Ya xaukaka ya tsarkaka.

Haqiqa Shi ne Allah rayayye tsayayye.



Tags: