Soyayya

Soyayya

Soyayya

Abin da ake nufi da son Allah

Duk wanda ya san Allah sai ya so shi

Son Allah: Shi ne zuciya ta nutsu da Allah, da karkata gare shi, ta amsa masa cikin dukkan abin da yake so, ambaton Allah ya mamaye dukkan zuciyar

Haqiqanin Son Allah

Son Allah shi ne son ibada da qanqan da kai da girmamawa, ya zama a cikin zuciyar masoyi akwai gimama wanda yake so, wato Allah, abin da zai kai zuwa ga kamanta umarninsa, da nisantar abin da ya hana. Wannan son shi ne tushen imani da tauhidi, akwai falala mai yawa a kansa wadda ba za su lissafu ba. Yana daga cikin son Allah son abin da Allah yake so, na wurare da lokuta da mutane, da ayyuka da maganganu, da wasunsu daga abubuwan da Allah yake so

Kamar yadda son Allah ya wajaba ya kasance don shi kaxai aka yi, amma wannan ba ya karo da so na xabi’a, kamar son xa ga mahaifinsa, da mahaifi ga xansa, da xalibi ga malaminsa, ko kamar son abinci da abin sha, da aure, da tufafi da abokai da sauransu.

Babu wani abin da aka bautawa Allah da shi kamar so da tsoro da fata.

Amma haramtaccen so shi kamar haxa Allah da wani cikin soyayya, kamar irin son da mushirikai suke yi wa gumakansu da waliyyansu, ko kuma gabatar da son zuciya akan abin da Allah yake so, ko son abin da Allah ba ya son shi, na lokuta da wurare da mutane da ayyuka da maganganu, kuma shi ma wannan son hawa-hawa ne. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Daga cikin mutane akwai wanda yake riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah, suna son su kamar yadda suke son Allah, waxanda suka yi imani sun tsananan son Allah. (Albaqra : 165)

Daga cikin Falalar Son Allah

1-Ita ce tushen tauhidi. Tsarkake soyayya ga Allah shi kaxai shi ne ruhin tauhidi, kai ita ce ma haqiqanin bauta, tauhidi baya cika har sai son bawa ga Ubangijinsa ya cika, kuma son Allah ya riga yi duk wata soyayya, ta yarda zai kasance dukkan abin da bawa yake so yana bin bayan abin da Allah yake so, da irin wannan soyayya ne bawa yake samun arziki da rabo.

Shauqin zuwa ga Allah da son gamuwa da shi wani abu ne da yake tasowa daga zuciya don ya tafiyar da zafin duniya.

2-Jin rarrashi yayin afkuwar masifa : Masoyi yana samun daxin soyayya da zai sa shi ya manta da masifa, kuma ta zama mai sauqi a kanshi.

Babu wanda ya fi tavewa a bayan qasa fiye da wanda aka hana masa samun nutsuwa da Allah mai girma da buwaya.

3-Samun cikakkiyar ni’ima da farin ciki mai yawa : hakan baya samuwa sai da son Allah mai girma da buwaya, babu abin da yake wadatar da zuciya, ya kare mata buqatarta, ya qosar da yunwarta sai son Allah da fuskantarsa mai girma da buwaya. Da mutum zai samu dukkan abin da ake jin daxi da shi, ba zai samu nutsuwa ba da kwanciyar hankali sai da son Allah, don haka son Allah shi ne ni’imar zuciya, lafiyayyun zukata da lafiyayyun hankula ba su da abin da ya son Allah da shauqin gamuwa da shi daxi da farin ciki a garesu, daxin da mumini yake ji a zuciyarsa yana sama da kowane daxi, ni’imar da yake ji tafi kowace ni’ima cika, daxin da take ji ya fi kowane daxi. “Abubuwa guda uku, wanda yake da su, to ya samu zaqin imani, Allah da Manzonsa su zama mafi soyuwa a wurinsa fiye da waxanda ba su ba. Ya so mutum ba ya son shi sai don Allah. Ya qi ya koma kafirci kamar yadda yake qin a jefa shi a wuta” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi)

Abubuwan Da Suke Jawo Son Allah

Ubangijinmu Allah mai girma da buwaya yana son wanda yake son shi, da wanda ya kusance shi, saboda haka farkon abin da yake jawo son Allah Maxaukakin Sarki shi ne bawa ya so Ubangijinsa son da ba ya yima wani daga cikin halitta. Ga bayanin abubuwan da suke jawo son Allah Maxaukakin Sarki gasu kamar haka :

1-Karanta Alqur’ani da fahimtar ma’noninsa da abin da ake nufi da su : Duk wanda ya shagala da littafin Allah ya yi aiki da shi, to za a raya masa zuciya da son Allah.

2-Kusantar Allah da nafilfili bayan an yi farillai “Bawana bai zai gushe ba, yana kusantata da nafilfili har sai na so shi, idan na so shi, sai in zama jinsa da yake ji da shi, in zama ganinsa da yake gani da shi, in zama hannunsa da yake damqa da shi, in zama qafarsa da yake tafiya da ita, idan ya roqe ni zan ba shi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina tabbas wallahi zan tsare shi (Hadisi Qudusi Bukhari ne ya rawaito shi)

3-Dauwama a cikin ambaton Allah a kowane lokaci da harshe da zuciya da aiki da hali

4-Gabatar da abin da Allah yake so akan abin da zuciya take so, na kwaxayi da sha’awar duniya

“Yana son su, kuma su ma suna son shi” (Alma’idah : 54)

5-Tsinkayo sunayen Allah da sifofinsa da saninsu a cikin zuciya.

6-Kallon kyautatawar Allah da ni’imominsa na fili da na voye.

7-Karyewar zuciya a gaban Allah mai girma da buwaya.

8-Kaxaita da Allah a qarshen kashi uku na dare, a lokacin da Ubangijinmu yake sauka zuwa ga sama ta kusa, sai bawa ya kevanta da Allah ya gana da shi, ya karanta littafinsa, ya yi ladabi a gabansa, yana tsaye yana sallah, ya cika da tuba da neman gafara.

9-Zama da masoya Allah na gaskiya, da zavar maganganunsu masu daxi, kamar yadda yake zavar ‘ya’yan itace mai daxi, da rashin magana sai yayin da maslahar maganar ta bayyana, ya bayyana akwai amfanuwar wani a cikin maganar

10-Nisantar dukkan wani abin da yake shiga tsakanin zuciya da Allah, mai girma da buwaya

Daga Cikin Amfanin Allah Ya So Bawa

Duk wanda Allah ya so shi, zai shiryar da shi ya kusantar da shi gare shi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ni ina akan yadda bawana ya zace ni, ina tare da shi idan ya ambace ni, idan ya ambace ni a cikin ran shi, sai in ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin taro, sai in ambace shi a cikin taron da ya fi nashi alheri, idan ya kusace ni xani xaya, sai in kusace shi zira’i xaya, idan ya kusace ni zira’i, sai an kusace shi kamu, idan ya zo min yana tafiya, zan zo masa ina sarsarfa. (Sahihul Bukhari)

Don haka duk lokacin da bawa ya ji tsoron Ubangijinsa sai ya samu wata shiriyar, a duk lokacin da ya so Allah, sai ya qara masa shiriya, duk lokacin da ya shiryu zai tsoron Allansa ya qaru.

Duk wanda Allah ya so shi, zai rubuta masa karvuwa a bayan qasa

Abin da ake nufi karvuwa ga wannan bawan da Allah yake so, da karkata zuwa gare shi, da yarda da shi, da yabonsa, komai zai so sai dai kafiri, saboda shi kafiri baya son Allah mai girma da buwaya, to ta yaya zai so masoya Allah? Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Idan Allah ya so bawa, sai ya kira Jibrilu, ya ce masa, ni ina son wane ka so shi, sai Jibrilu ya so shi, sannan sai ya yi kira a sama, ya ce, Allah yana son wane, ku so shi, sai waxanda suke sama su so shi, ya ce, sai a sanya masa karvuwa a bayan qasa” (Muslim ne ya rawaito shi)

To haka lamarin yake idan Allah ya so bawa sai ya kewaye shi da kulawarsa da kiyayewarsa, kuma ya sanya komai ya yi masa xa’a ya kusantar masa da nesa, ya sauqaqa masa al’amarin duniya, ba zai ji wata gajiya ba ko wahala ba. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Haqiqa waxanda suka yi imani suka yi aiki na qwarai Allah mai rahama zai sanya musu so da qauna” (Maryam : 96)

Duk wanda Allah ya so shi, sai ya sanya shi tare da shi. Idan Allah ya so bawa sai ya zama tare da shi, yana kiyaye shi yana kula da shi, ba zai ba wani dama a kanshi ba ya cuce shi. A cikin hadisi qudusi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah ya ce, wanda ya yi gaba da waliyyina to na yi masa shelar yaqi, bawana ba zai kusance ni ba da wani abu da nafi so, fiye da abin da na wajabta masa, bawana ba zai gushe ba yana kusantata da nafilfili har sai na so shi, idan na so shi, sai in zama jinsa da yake ji da shi, in zama ganinsa da yake gani da shi, in zama hannunsa da yake damqa da shi, in zama qafarsa da yake tafiya da ita, kuma lallai idan ya roqe ni tabbas zan ba shi, kuma wallahi idan ya nemi tsarina tabbas wallahi zan tsare shi. Babu wani abu da zan aikata, na yi kaikawo a kansa kamar karvar ran mumini, yana qin mutuwa ni kuma ina qin sava masa” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Imani na gaskiya rayuwa ce ga zukata, kuma fage ne na farin ciki, kamar yadda kaficewa Allah yake mutuwa ga zukata tun gabanin mutuwa, kuma fage na baqin ciki.

Wanda Allah ya so shi sai ya amsa masa addu’arsa : Daga cikin alamar son Allah ga bayinsa muminai shi ne ya amsa musu addu’o’insu, ya yi musu ni’ima da sun xaga hannayensu sama, sun ce “Ya Ubangijin”. Allah ya ce, “Idan bayina suka tambayeka dangane da ni, to ni ina kusa, ni amsa kiran mai kira idan ya kirani, su amsa mini su yi imani da ni, ko sa samu shiriya” (Albaqra : 186).

An karvo daga Salmanul Farisi ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Allah mai kunya ne da karamci, yana cin kunyar bawansa idan ya xaga hannunsa sama ya dawo da su ba komai” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Idan Allah ya so bawa, sai sanya Mala&"iku su riqa nema masa gafara. Mala&"iku suna newawa wanda Allah yake so gafara, suna nema masa rahama daga wajen Allah, Allah ya ce, “Waxanda suke xauke da Al’arshi da waxanda suke gefensa suna yin tasbihi ga Ubangijinsu, suna yin imani da shi, suna nema wa waxanda suka yi imani gafara, (suna cewa) Ya Ubangijinmu ka yalwaci komai da rahama da ilimi, ka gafarta wa waxanda suka tuba, suka bi hanyarka, ka tseratar da su daga azabar Jaheem” (Gafir : 7)

Allah yana cewa “Sama ta kusa ta tsage a samansu. Mala’iku suna godewa Ubangijinsu suna neman gafararsa ga waxanda suke bayan qasa. Ku saurara! Haqiqa Allah shi mai yawan gafara ne mai jinqai”. (Asshura : 5)

Idan Allah ya so bawa, sai ya xauki ransa yana kan aiki na qwarai. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Idan Allah ya nufi bawa da alheri, sai ya buxa masa. Aka ce, meye ma’anar ya buxa masa? Sai ya ce, “ya buxe masa aikin qwarai gabanin mutuwarsa, sannan sai ya xauke shi a kansa”. (Ahmad ne ya rawaito shi)

-Idan Allah ya so bawa sai ya amintar da shi yayin mutuwa.

Idan Allah ya so bawa sai ya amintar da shi a duniya, ya azurta shi mutuwa cikin aminci da sabati, ya aiko masa Mala’ikunsa su karvi ransa cikin sauqi, su tabbatar da shi akan gaskiya yayin mutuwa, su yi masa bushara da Aljannah. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Waxanda suka ce Ubangijinmu Allah sannan suka daidaita, Mala’iku suna sauka a gare su, (Suna ce musu) kada ku ji tsoro, ku yi bushara da Aljannah wadda aka kasance ana muku alqawari” (Fussilat : 30).

-Idan Allah ya so bawa sai ya dauwamar da shi a cikin Aljannah

Wanda duk Allah ya so shi, to yana cikin Aljannah a lahira, girmamawar Allah da karamcinsa ga bawa a lahiri wani abu ne wanda tunani bai iya tunaninsa, Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa masoyansa alqawarinsa da Aljannah, wadda a cikinta akwai abin da zuciya take so, kamar yadda ya zo a cikin hadisi qudusi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce,.. “Allah ya ce, na tanadarwa bayina salihai abin da idanu ba su tava gani ba, kunnuwa ba su tava ji ba, kuma bai taba xarsuwa ba a zuciyar wani mutum. Ku kuranta wannan ayar in kun ga dama, “Wata rai ba ta san abin da aka voye musu ba na farin ciki” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Duniya ba ta tava daxi ba, sai da son Allah da yi masa xa’a, haka nan Aljannah bata tava daxi ba sai da ganin Allah Maxaukakin Sarki

Daga cikin fa’idar son Allah ga bawa, ganin da bawa zai yi wa Allah Maxaukakin Sarki.

Ubangiji mai girma da buwaya yana bayyana da haskensa ga bayinsa waxanda yake son su, ba za su ga wani abin da suke so fiye da shi ba, har abada, saboda abin da aka rawaito cewa Manzon Allah (S.A.W) ya kalli wata a lokacin da ya cika, ya ce, ..“Haqiqa za ku ga Ubangijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba za ku yi turarreniya ba wajen ganinsa. , Idan kun sami dama kada a rinjaye ku akan barin sallah kafin vullowar rana da gabanin faxuwarta to ku yi, ku karanta faxin Allah : “Ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kafin vullowar rana da gabanin faxuwarta”(Sahihul Bukhari)

Wasu Hukunce-Hukunce Da Faxakarwa Akan So

1-Son Allah ga bawa ba ya hana faruwar bala’i gare shi, Manzon AllAh (S.A.W) ya ce, “Girman lada yana tare da girman bala’i, kuma idan Allah ya so mutane sai ya jarrabe su, duk wanda ya yarda yana da yarda, wanda ya yi fushi, shi ma fushi ya hau kansa”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Sai Allah ya jarrabi bayi da nau’ikan bala’i, har sai ya tsarkake su daga zunubi, ya raba zukatansu daga shagala da duniya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Za mu jarrabeku har sai mun san mujahidai a cikinku da masu haquri, kuma mu jarrabi labarurrukanku” (Muhammad : 31)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Tabbas za mu jarrabeku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar rayuka da dukiya da ‘ya’yan itace. Ka yi wa masu haquri bushara. Waxanda idan musifa ta same su, sai su ce, mu daga Allah muke, kuma gare shi za mu koma. Waxannan suna da tsira da rahama daga Ubangijinsu. Waxannan sune shiryaryu” (Albaqra : 155 – 157)

2-Savawa bawa ga Allah yana rage son Allah, ya kawar da kamalarta, saboda soyayya ma kamar imani ce, tana da tushe da kamala, gwargwadon savo gwargwadon yadda zata ragu. Idan mutum ya shiga cikin shakka da babban munafunci, sai asalinta ya tafi, ya zama babu, wanda kuma a zuciyarsa babu son Allah to kafiri ne ya yi ridda, ya zama babban munafiki, bai da rabo a cikin addini. Amma masu savo ba zai yi wu a ce ba sa son Allah ba, sai dai a ce son su ga Allah ragagge ne, don haka akan haka za a yi musu mu’amala. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Da ba ku yin zunubi da Allah ya halicci wasu mutane suna yin zunubi yana gafarta musu” (Ahmad ne ya rawaito shi)

“Yanci shi ne ‘yantuwar zuciya daga shirka da sha’awa da shubuhohi. Bauta kuma ita ce bautar zuciya, ta zama ba ga wanin Allah ba.

3-Son Allah ba ya kore so na xabi’a, wanda zuciya take karkata zuwa gare shi, kamar son abinci da abin sha da ruwa, da sauransu. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An sanya min son mata da turare a duniya” (Ahmad ne ya rawaito shi)

Don haka akwai wasu abubuwa a duniya da son su ba ya cikin shirka, saboda Manzon Allah ya so su, don haka ya halatta mutum ya so wani abu na duniya matuqar dai ba abin da aka haramta ba ne.

4-Wanda duk ya so wani kamar yadda yake son Allah, to shi mushiriki ne. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa, “Daga cikin mutane akwai waxanda suke riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah suna son su kamar yadda suke son Allah, waxanda suka yi imani sun fi tsananin son Allah. Da waxanda suka yi zalunci za su ga, - yayin da za su ga azaba - cewa dukkan qarfi na Allah ne gabaxaya, kuma Allah mai tsananin azaba ne”. (Albaqra : 165)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi soyuwar aiki a wurin Allah mai girma da buwaya shi ne so don Allah da qi don Allah”.

A cikin wannan ayar akwai narkon azaba mai tsanani ga wanda ya daidaita soyaryar wani da ta Allah a wajen ibada da girmamawa.

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “ka ce in iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara, da kasuwancin da kuke jin tsoron lalacewarsa, da wuraren zama da kuke so, sun fi soyuwa a wajenku fiye da Allah da Manzonsa da Jihadi akan tafarkinsa to ku jira, har Allah ya zo da lamarinsa” (Attaubah : 24)

A cikin wannan ayar akwai narko mai tsanani ga mutumin waxannan abubuwa guda takwas suka fi soyuwa a wajensa fiye da Allah. An karvo daga Anas, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Xayanku ba zai yi imani ba, har sai na kasance mafi soyuwa a wajensa fiye da ‘ya’yansa da iyayensa da dukkan mutane gabaxaya” (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)

5-Jivinta da son mushirikai koma bayan muminai ya ci karo da son Allah, saboda shirkar mushiriki a addininsa. Son don Allah da qi don Allah tushe babba a musu lunci. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kada muminai su riqi kafirai ababen jivinta ba muminai ba, duk wanda ya yi haka, sai dai in don ku kare kanku daga gare su ne” (Al-Imran : 28)

Allah ya hana muminai su jivinci kafirai, ya qarfafa hanin da cewa, duk wanda ya yi haka, to ba shi ba soyayyar Allah a cikin komai, son masoyi da son maqiyinsa sun savawa juna ba sa haxuwa. “Sai dai ku kare kanku daga garesu” (Al-Imran : 28)

Allah ya yi rangwame wajen son su idan musulmi sun ji tsoronsu,kuma ba za su iya zama da su ba, sai da hakan, a wannan lokaci ya hallata su cakuxu da su a zahiri, amma zuciyarsu ta zama cike da Imani da qyamar kafirai. Kamar yadda Allah mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa tana cike da Imani” (Annahli : 106)

Walqiyar So

Alamar son Allah yawan ambatonsa, da shauqin gamuwa da shi, duk wanda yake son abu zai ya yawaita ambatonsa, ya so gamuwa da shi.

Arrabi›u xan Anas

Yayin da aka ba Annabinmu (S.A.W) zavi tsakanin rayuwar duniya ko gamuwa da Allah mai girma da buwaya, sai ya ce, “A’a zuwa ga abokantaka mafi xaukaka” (Ahmad ne ya rawaito shi)

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya zavi son Allah mai girma da buwaya, da son haxuwa da shi, ya fifita hakan, ya gabatar da shi akan son duniya da sha’awarta da kayan jin daxinta.Tags: