Tasirin Imani Da Sunayen Allah Da Sifffofinsa A Kan Bawa

Tasirin Imani Da Sunayen Allah Da Sifffofinsa A Kan Bawa

Tasirin Imani Da Sunayen Allah Da Sifffofinsa A Kan Bawa

1-Bautawa Allah da sunayensa da siffofinsa. Bawa idan ya san sunayen Allah da siffonfinsa, ya yi imani da su kamar yadda Allah yake so, ya san ma’anarsu akan yadda imaninsa zai qaru, sai ya girmama Allah, a cikin zuciyarsa, don haka aka ce, “wanda duk yafi sanin Allah to ya fi tsoronsa”.

2-Qaruwar Imani : Sanin Sunayen Allah mafiya kyau, da siffofinsa maxaukaka suna sa bawa ya ji girman Allah, sai imaninsa da qasqantar da kansa ga Allah mai girma da buwaya su qaru. “Waxanda suka shiriya, ya qara musu shiriya” (Muhammad : 17)

3-Ambaton Allah : Duk wanda ya san Allah sai ya so shi, wanda kuma ya so Ubangijinsa sai ya yawaita ambatonsa, saboda zai mamaye masa zuciya da so, har a wayi gari ba ya soyayya sai don saboda shi, ba ya qiyayya sai saboda shi.

4-Son Allah mai girma da buwaya Allah yana cewa : “Daga cikin mutane akwai waxanda suke riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah, suna son su kamar yadda suke son Allah, waxanda suka yi imani sun fi tsananin son Allah”. (Albaqra : 165)

Idan bawa ya san girman siffar Ubangiji sai ranshi ya karkata zuwa gare shi, ya ratayu da shi, zuciya ta farin ciki da sanin Ubangijinta, saboda kamalarsa da kyansa, sai bawa ya ji daxin zancen Allah, ya samu hutu ta hanyar kiran shi, da fata gare shi da tsoronsa, saboda son Allah duk yana kawo haka, sai ka samu bawa yana son Allah, yana son abin da Allah yake so, yana son wanda Allah yake so.

Bai halatta ga wani ba ya faxi komai akan zatin Allah, ko ya siffata shi sai da abin da ya siffata kanshi da shi, kada ya faxi komai a kan Allah da ra’ayinsa, Allah Maxaukakin Sarki Ubangijin Talikai.

Imam Abu Hanifa

5-Jin kunyar Allah : Duk lokacin da ka ga kwarjinin Ubangiji sai jin kunyarsa ta qaru a wajenka, sai ka tuna mutuwa ka yi kuka, ka kiyaye gavvanka don ka samu yardar Allah.

6-Qasqantar da kai ga Allah : Idan kasan buwayar Allah, sai kasan qasqancinka. Idan kasan qarfin Allah, sai ka gane rauninka. Idan ka san abubuwan da Allah ya mallaka sai ka san talaucinka. Idan kasan kamalar Allah sai kasan tawayarka. Idan ka san cikar siffofinsa da kyan sunayensa sai kasan cikar talaucinka da buqatarka da qasqancinka, don haka kai ba kowa ba ne face bawa.



Tags: