Allah Mai Girma Da Xaukaka

Allah Mai Girma Da Xaukaka

Allah Mai Girma Da Xaukaka

Allah mai girma da xaukaka, abin bautawa, abin yabo da godiya.

Sammai da qassai da abin da yake cikinsu suna yi masa tasbihi.

Duk wanda yafi sanin Allah, to yafi jin tsoronsa.

Da dare da abin da ya qunsa, da rana da abin da ya bayyana a cikinta, da tuda da cikin ruwa, dukkan waxannan suna tsarkake Allah suna yi masa tasbihi. Allah ya ce, “Babu wani abu face yana tasbihi da godiya ga (Allah) sai dai baku gane tasbihinsu”. (Al-isra’i 44)

Lafazin “Allah” Sanannen suna ne ba buqatar a yi bayaninsa, dukkan zukata sun san shi, kuma rayukansu suna sunkuyawa don saninsa.

Allah shi ne wanda zukata suke bauta masa, kuma rayuka suke kwaxayin samun afuwarsa, suke samun xebewar kewa in an ambace shi.

Allah wanda ya sanya tsoro da buqata a zukatan bayinsa, kuma babu abin da zai wadatar da zuciyar bawa har sai ya koma zuwa gareshi.

Lafazin Allah suna ne na zatin Allah, wanda ya siffatu da dukkan wata kyakkyawar siffa.

Buqatuwar Bayi Zuwa Ga Allah Ta’ala

Bawa yana buqatar mafaka da makoma a yayin da yake cikin musifa da baqin ciki, haka Allah ya halicce shi, don haka a kowanne lokaci yake da buqata wajen Ubangijinsa, yake kuma gaggawa wajen neman yardarsa, saboda zai haxu da shi.

Duk wani guzuri wanda ba imani da Allah ba, yana qarewa, haka ma duk wata madogara ko wani taimako wanda ba na Allah ba, to mai rugujewa ne.

Idan bawa ya maida buqatunsa zuwa ga Allah, ya yi abin da aka xora masa na wajibi, ya wadatu da abin da yake wajen Allah, kuma ya yi haquri to Allah zai sanya shi ya zama jagora abin koyi a cikin halittunsa, ya zama ana koyi da shi.. “Muka sanya su jagorori suna shiruwa da lamarinmu yayin da suka yi haquri, kuma sun kasance masu sakankancewa da ayoyinmu”. (Assajada : 24)

Don haka Allah ya sanya haquri da sakankancewa sababaine na samun jagoranci a addini.

An halicci halitta akan rataya zuciya ga mahalicci. Hakanan an halicce su akan son wanda ya kyautata musu, ya fifita su, wanda shi ne Allah Maxaukakin Sarki.

Girman Ilimin Sani Allah

Yana daga cikin karamcin Allah ga bawa ya sauwaqe masa saninsa.

Girman ilimi da darajarsa tana xamfare da abin da ake koya a cikinsa, babu kuwa abin da ya kai Ubangiji Allah girma da daraja, hakama sanin siffofinsa da sunayensa da hikimarsa da haqqinsa akan bayi, don haka tauhidi ya zama shi ne qunshin addini, kusan kashi xaya bisa uku na Alqur’ani duk tabbatar da tauhidi ne qarara

A Cikin Komai Yanada Aya

Allah ya sanya ayar dake nuna samuwarsa da kaxaitakarsa da cikarsa da girmansa da xaukakarsa a cikin dukkan abin da ya halitta. Kai ya yi ma umarni da a yi tunani a cikin waxannan dalilai (waxanda suke nuna samuwar Allah) ya ba mu labarin cewa waxannan abubuwa ayoyi ga masu hankali masana masu tunani.

A gurguje mu duba wasu ayoyin Alqur’ani, waxanda suke kiran masu hankali da tunani zuwa ga imani da Allah shi kaxai wanda ake nufata da buqatu. Allah ya ce, “A bayan qasa akwai ayoyi ga matafiya, haka ma a cikin halittar kawunanku, yanzu baku gani”. (Azzariyat : 20 – 21)

Kuma Allah ya ce, “Ka ce, ku yi tunani, meye a cikin sammai da qasa”. (Yunus : 101).

Allah ya ce, “Haqiqa Ubangijinku Allah, wanda ya halicci sammai da qassai a cikin kwana shida, sannan ya daidaita a kan Al’arshi, yana jujjuya lamura, babu wani mai ceto sai da izininsa, wannan shi ne Allah Ubangijinku ku bauta masa, yanzu ba za ku yi tunani ba. Dukkan makoma tana gare shi, alqawarin Allah ne na gaskiya, kuma haqiqa Allah yana farar da halitta sannan ya dawo da ita, don ya sakawa waxanda suka yi imani da aiki na qwarai da adalci, waxanda suka kafirta kuwa suna da abin sha mai zafi da azaba mai raxaxi saboda kafircin da suka kasance suna yi. Allah ne ya sanya rana ta zama haske, ya sanya wata ya zama haske, ya sanya shi mai tafiya akan matakai daban daban don ku san adadin shekaru da lissafi, duk Allah bai halicci waxannan (abubuwa) ba sai da gaskiya, kuma yana rarrabe ayoyi ga mutane masu ilimi. A cikin savawar dare da yini, da abin da Allah ya halinta a cikin sammai da qasa akwai ayoyi ga mutane masu taqawa”. (Yunus : 3 – 6).

Kuma Allah ya ce, “A cikin halittar sammai da qasa da savawar dare da yini akwai ayoyi ga masu hankali. Waxanda suke ambaton Allah a tsaye da zaune da kwance, kuma suke tunani a cikin halittar sammai da qasa, (suna cewa) ya Ubangijinmu baka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata a gareka, ka tseratar da mu daga azabar wuta”.(Ali-Imran : 190 – 191)

Ya kuma cewa : “A cikin halittarku da abin da (Allah) ya watsa na dabbobi masu tafiya a bayan qasa akwai ayoyi ga mutane masu yaqini”. (Al-Jasiya : 4)

Kuma ya ce, “Ashe ba za su yi tafiya a bayan qasa ba, ya zama suna da zukata da suke hankalta da su ba, da kunnuwa da suke ji da su ba” (Al-hajji 46)

Ya ce, “Yanzu ba za su kalli sama dake samansu ba, (su ga) yaya muka ginata, ,muka qawata ta, ba ta da wasu hudoji”. (Qaf : 6)

Kuma ya ce, “Aikin Allah ne wanda ya kyautata dukkan komai” (Annamli : 88)

Kuma Ya ce, “lallai a cikin haka akwai ayoyi ga masu hankali” (Xaha : 54)Tags: