Yayin Da Aka Rasa Imani Da Allah

Yayin Da Aka Rasa Imani Da Allah

Yayin Da Aka Rasa Imani Da Allah

Imani da Allah shi ne matakin farko na canzawar rayuwar mutane daga qangin bauta zuwa ga bautawa Allah mai girma da buwaya wanda ya cancanta a bauta masa

Yayin da za a rasa mabuxin imani a rayuwar da yawa daga cikin mutane, to babu shakka sakamakon zai kasance qunci ne da wahala, abin da yakan sa wasu al’ummomi su qirqiri sababbin hanyoyin kashe kansu da kansu, don rabuwa da rayuwar qunci da takuruwa. Godiya ta tabbata ga Allah a bisa ni’imar musulunci, kuma lallai ta isa ni’ima. Mu karanta wannan labari mai zuwa :

Sabuwar Hanyar Fita Daga Duniya

Philip Nistsehke xan ranjin kiran kisan tausayi a qasar Ustaraliya y ace, : Na’urar kashe kai wanda ake kira da (jakar mutuwa) wadda kuma ake nemanta ta hanyar akwatin gidan waya, daga Kanada ana cin riba sosai a qasar.

Kuxin Na’ura xaya ta kai dala talatin ta America, a cikin wannan jakar a kan haxo ta da wata jaka ta leda wacce take taimakawa wajen fitar da rai ta hanyar maqara.

Nistsechke ya faxawa gidan radion E.B.C na Autsralia cewa duk da wannan na’urar mai sanya damuwa ce kwarai sai dai fa nan da nan take kawar da rai.

Ya ci gaba da cewa : Ana amfani da wannan na’ura sosai, kuma da mutane da yawa sukan yi masa maganarta da bayanin yadda take da sauran abubuwan da suka shafe ta.

Ta wani vanagaren kuma wata mace yar birtaniya, wadda take fama da rashin lafiyar da take hana mutum motsawa, ta kai qarar mijinta a babban kotun dake London, don kotun ta bashi damar ya taimaka mata ta kashe kanta.

Hakanan radion London ya ba da labarin wata mace yar shekara 42, da ake kira da Dayana Pirate, wadda ta kamu da irin wannan cuta a shekaru biyu da suka wuce, kuma ta je kotu ta kai qara, saboda hukumomi sun qi yarda su qyale mijinta kada su kama shi idan ya taimaka mata ta kashe kanta.. Allah Mai Girma Da Buwaya yana cewa, “Wanda duk ya kawar da kai daga ambatona to yana da rayuwar qunci”. (Xaha : 124)Tags: