Buqatuwar Bayi Mabuqata Zuwa Ga Allah Mawadaci

Buqatuwar Bayi Mabuqata Zuwa Ga Allah Mawadaci

Buqatuwar Bayi Mabuqata Zuwa Ga Allah Mawadaci

Ya ku Bayina

“Ya ku Mutane haqiqa ku mabuqata ne zuwa ga Allah, Allah shi ne kaxai mawadaci abin yabo”. (Faxir : 15).

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, cikin abin da ya rawaito daga Ubangijinsa Mai Girma Da Buwaya, Allah ya ce : Ya ku bayina haqiqa ni na haramtawa kaina zalunci, kuma na sanya shi haramun a tsakaninku, don haka kada ku yi zalunci. Ya ku bayina dukkanku vatattu ne, sai wanda na shiryar da shi, don haka ku nemi shiryarwata in shiryar daku. Ya ku bayina dukkanku mayunwata ne, sai wanda na ciyar da shi, ku nemi ciyawarta, in ciyar daku. Ya ku bayina dukkanku matsiraita ne, sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku. Ya ku bayina haqiqa kuna laifuka dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya, ku nemi gafara ta in gafarta muku. Ya ku bayina haqiqa ba ku isa ku cutar da niba, ballantana ku cuce ni, kuma ba ku isa ku amfanar da niba, balle ku amfane ni. Ya ku bayina da ace na farkonku da qarshenku, da mutanenku, da aljanunku, za su kasance akan zuciyar wanda ya fi kowa tsoron Allah a cikinku, hakan ba zai qara komai a cikin mulkina ba. Hakanan da za a ce na farkonku da na qarshenku da aljanunku da mutanenku za su kasance a kan zuciyar wanda ya fi kowa fajirci a cikinku, hakan ba zai tauye komai daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na qarshenku da aljanunku da mutanenku za su taru a wuri xaya, su roqe ni, in kuma baiwa kowa abin da ya roqe ni, to da hakan ba zai rage komai daga abin da yake wurina ba, sai kamar yadda allura za ta rage in sanyata cikin kogi. Ya ku bayina ayyukanku ne nake lissafawa, sannan in cika muku sakamakonsu, wanda ya samu alheri ya godewa Allah, wanda kuwa ya samu wanin haka, to kada ya zargi kowa sai kansa” (Muslim ne ya rawaito shi)

Ka Kiyaye Allah Sai Ya Kiyaye Ka

An karvo daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) wata rana ya goya ni akan abin hawa, sai yace, “Ya kai xan yaro zan sanar da kai wasu kalmomi. Ka kiyaye (addinin) Allah, Allah kiyayeka, kiyaye (addinin) Allah za ka sami Allah kusa da kai, idan za ka yi roqo, to roqi Allah, idan zaka nemi taimako, ka nema a wajen Allah, ka sani cewa da al’umma za ta haxu akan ta amfaneka da wani abu, to da baza ta amfaneka da komai ba sai da abin da Allah ya rubuta maka, hakama da al’umma zata haxu akan ta cuce ka da wani abu, to da baza ta cuce ka ba, sai da abin da Allah ya rubuta zai same ka, an xaga alqaluma, takardun sun bushe” Tirmizi ne ya rawaito shi



Tags: